< Ezra 4 >
1 Sa’ad da abokan gāban Yahuda da na Benyamin suka ji cewa waɗanda suka dawo daga bauta suna gina haikalin Ubangiji, Allah na Isra’ila
2 sai suka zo wurin Zerubbabel da kuma wurin shugabannin iyalai, suka ce, “Bari mu taimake ku ginin domin mu ma muna addu’a ga Allahnku yadda kuke yi, muna miƙa masa hadaya tun lokacin Esar-Haddon sarkin Assuriya wanda ya kawo mu nan.”
3 Amma Zerubbabel, Yeshuwa, da sauran shugabannin iyalai na Isra’ila suka amsa suka ce, “Ba za ku sa hannu cikin gina wa Allahnmu haikali ba, mu kaɗai za mu gina wa Ubangiji, Allah na Isra’ila gini kamar yadda Sarki Sairus, sarkin Farisa, ya umarce mu.”
4 Sai mutanen da suke zama a wurin suka fara yin ƙoƙari su sa mutanen Yahuda su karaya, suka sa su ji tsoron ci gaba da ginin.
5 Suka yi hayar mashawarta don su ga cewa sun ɓata ƙoƙarinsu dukan kwanakin mulkin Sairus sarkin Farisa har zuwa kwanakin mulkin Dariyus sarkin Farisa.
6 A farkon mulkin Zerzes, sai abokan gāba suka kawo ƙarar mutanen Yahuda da na Urushalima.
7 A zamanin Artazerzes sarkin Farisa kuma, sai Bishlam, da Mitredat, da Tabeyel, da sauran abokansu suka rubuta wasiƙa zuwa ga Artazerzes. Aka rubuta wasiƙar da harufan Arameyik, aka kuma fassara ta a yaren Arameyik.
8 Rehum shugaban rundunar soja, da Shimshai marubuci, suka rubuta wasiƙar a kan Urushalima zuwa ga sarki Artazerzes, suka ce.
9 Rehum shugaban sojoji, da Shimshai marubuci, da sauran abokansu, wato, alƙalai, da masu riƙe da muƙamai daga Farisa, Uruk da Babilon, mutanen Elam da na Shusha,
10 da sauran mutane waɗanda mai girma Osnaffar ya kwaso, ya zaunar da su cikin birnin Samariya da sauran wurare na Kewayen Kogin Yuferites.
11 (Ga abin da suka rubuta.) Zuwa ga sarki Artazerzes. Daga bayinka, mutanen Kewayen Kogin Yuferites.
12 Ya kamata sarki ya san cewa Yahudawan da suka hauro wurinmu daga wurinka, sun je Urushalima suna sāke gina wannan mugun birni mai tawaye. Suna sāke gyara katangar, suna kuma gyara harsashin katangar.
13 Ya kamata fa, sarki ya san cewa in aka sāke gina wannan birni duk da katangar birnin, mutanen birnin ba za su dinga biyan haraji, da kuɗin shiga, da na fitar da kaya ba, wannan zai sa aljihun masarauta yă bushe.
14 Tun da yake muna ƙarƙashin fada, bai kyautu mu bari a rena sarki ba, Saboda haka muke sanar da sarki,
15 domin a bincika a littattafan tarihin kakanninka. Za ka ga cewa wannan birni mai tawaye ne. Tun daga zamanin dā wannan birnin yana ba sarakuna da yankuna damuwa. Wannan ne ya sa aka ragargazar da birnin.
16 Muna sanar da sarki cewa in har aka sāke gina wannan birnin da katangarsa, zai zama ka rasa kome a gefen Kewayen Kogin Yuferites ke nan.
17 Sarki ya aika da wannan amsa. Zuwa ga Rehum shugaban sojoji, Shimshai marubuci da kuma sauran abokansu waɗanda suke zama a Samariya da kuma sauran wurare a Kewayen Kogin Yuferites. Gaisuwa.
18 An karanta, an kuma fassara mini wasiƙar da kuma aika.
19 Na ba da umarni aka kuma yi bincike, aka tarar cewa wannan birni ya daɗe yana yi wa sarakuna tawaye, an yi tashin hankali a birnin.
20 Urushalima ta yi sarakuna masu iko sosai waɗanda suka yi mulkin Kewayen Kogin Yuferites gaba ɗaya, an kuma biya masu haraji, da kuɗin shiga da na fita na kaya.
21 Saboda haka sai ku ba da umarni yanzu cewa mutanen su daina wannan aiki sai lokacin da na ba da umarni.
22 Ku tabbata ka ɗauki wannan da muhimmanci. Don me za a bari wannan abu yă zama abin damuwa ga sarauta?
23 Da gama karanta wasiƙar sarki Artazerzes wa Rehum da Shimshai marubuci, da abokansu, sai suka yi sauri suka je wurin Yahudawa a Urushalima, suka hana su aikin ƙarfi da yaji.
24 Saboda haka aikin a gidan Allah a Urushalima ya tsaya cik sai a shekara ta biyu ta mulkin Dariyus sarkin Farisa.