< Ezra 10 >
1 Yayinda Ezra yake addu’a, yake kuma furta laifi, yana kuka, yana a durƙushe da kansa ƙasa a gaban gidan Allah, sai babban taron jama’ar Isra’ilawa, maza, mata da yara, suka taru a wurinsa. Su ma suka yi kuka mai zafi.
As Ezra was praying and confessing sins, weeping and falling down on his face before God's Temple, a very large crowd of Israelites, men, women, and children, gathered around him. The people were weeping bitterly as well.
2 Sai Shekaniya ɗan Yehiyel, daga zuriyar Elam ya ce wa Ezra, “Mun yi wa Allah rashin aminci ta wurin yin auratayya da maƙwabtanmu, amma duk da haka bai yashe mutanen Isra’ila ba.
Shecaniah, son of Jehiel, an Elamite, said to Ezra: “Yes, we have been unfaithful to our God because we have married foreign women from the people of the land. But even so there is still hope for Israel over this.
3 Yanzu bari mu yi alkawari da Allahnmu, mu kori matan da yaransu bisa ga abin da ranka yă daɗe da sauran shugabannin da kuke girmama umarnin Allah kuka shawarce mu, bari mu yi haka bisa ga doka.
Let us make a solemn agreement right now before our God that we will send away all the foreign wives and their children. We will follow the directions given by you and those who respect the instructions of our God, carried out according to the Law.
4 Sai ka tashi, gama wannan hakkinka ne, za mu ba ka goyon baya. Saboda haka ka yi ƙarfin hali ka aikata shi.”
Take action! It's your responsibility. We are with you. Be brave and do it!”
5 Sai Ezra ya tashi ya sa firistoci da suke shugabanni, da Lawiyawa, da dukan mutanen Isra’ila su rantse, cewa za su yi abin da aka ce. Sai suka yi rantsuwar.
So Ezra stood up and made the leading priests, Levites, and all the Israelites present take an oath to act on what had just been said. They all took the oath.
6 Sa’an nan Ezra ya tashi daga gidan Allah ya tafi gidan Yehohanan ɗan Eliyashib, a can ma bai ci wani abu ba, bai sha ruwa ba domin ya ci gaba da yin baƙin cikin rashin aminci na waɗanda suka dawo daga bauta.
Then Ezra left them in front of God's Temple, and went to the room of Jehohanan, son of Eliashib. During the time he stayed there, he didn't eat or drink anything, because he was still mourning the unfaithfulness of the exiles.
7 Aka yi shela a duk fāɗin Yahuda da Urushalima cewa dukan waɗanda suka dawo daga bauta su tattaru a Urushalima.
Then a proclamation was issued throughout Judah and Jerusalem that all the exiles should assemble in Jerusalem.
8 Duk wanda bai zo a cikin kwana uku ba, za a washe shi, a kuma ware shi daga jama’ar da suka dawo daga bauta. Haka shugabanni da dattawa suka zartar.
Anyone who did not come within three days would have all their property confiscated, and would be banned from the assembly of the exiles. This was the decision of the leaders and elders.
9 A cikin kwana uku duk mutanen Yahuda da na Benyamin suka taru a Urushalima. A ranar ashirin ga watan tara, dukan mutanen suka zauna a dandali a gaban gidan Allah cike da ɓacin rai saboda abin da ya faru da kuma ruwan da aka yi.
Within three days, everyone from Judah and Benjamin assembled in Jerusalem. On the twentieth day of the ninth month, all the people sat in the square beside God's Temple, shivering because of this issue and also because of the heavy rain.
10 Sai Ezra firist ya miƙe tsaye ya yi musu magana ya ce, “Kun yi rashin aminci; kun aure mata baƙi, ta haka kuka ƙara kan zunubin Isra’ila.
Ezra the priest stood up and told them, “You have committed sin by marrying foreign women, making Israel's guilt even worse.
11 Yanzu sai ku furta zunubanku ga Ubangiji, Allahn kakanninku, ku kuma yi nufinsa. Ku raba kanku da mutanen da suke kewaye da ku, ku kuma rabu da baƙin mata.”
Now you must confess your sin to the Lord, the God of your forefathers, and do what he requires. Sever your connections with the people of the land and your foreign wives.”
12 Mutanen kuwa suka tā da murya da ƙarfi suka ce, “Gaskiya ka faɗa, dole mu yi yadda ka ce,
The whole assembly answered in a loud voice: “We agree, and we promise to do as you say!
13 Amma akwai mutane da yawa, kuma lokacin damina ne; saboda haka ba za mu iya tsayawa a waje ba. Ban da haka ma, aikin nan ba na kwana ɗaya ko biyu ba ne, domin ba ƙaramin laifi muka yi ba.
But there are a lot of people here, and it's pouring with rain. We can't stay outside. More to the point, this isn't something that can be fixed in one or two days, for we have sinned extremely seriously in this.
14 Bari shugabanninmu su yi wani abu a madadin mutane duka, sa’an nan sai duk wanda ya san ya auri baƙuwar mace a garuruwanmu, sai yă zo nan a lokacin da aka shirya tare da dattawa da alƙalan kowane gari, har sai Allah ya huce fushinsa mai zafi da yake kanmu.”
Let our leaders act on behalf of the whole assembly. Then let every man in each of our towns who has married a foreign woman be given an appointment to come and meet, together with the elders and judges of that town, until our God is no longer angry with us over this.”
15 Yonatan ɗan Asahel, da Yazehiya ɗan Tikba su ne kaɗai ba su yarda da wannan shirin ba, sai Meshullam da Shabbetai Balawe kuma suka goyi bayansu.
The only ones to oppose this were Jonathan, son of Asahel, and Jahzeiah, son of Tikvah, supported by Meshullam and Shabbethai the Levite.
16 Sai waɗanda suka dawo daga bauta suka yi yadda aka zartar. Ezra firist ya zaɓi mutane waɗanda su ne shugabannin iyalai, ɗaya daga kowane sashe, aka rubuta sunan kowannensu. A ranar ɗaya ga watan goma kuwa suka zauna don su yi binciken waɗannan abubuwa.
So this what the exiles did, selecting Ezra the priest and family leaders, according to their family divisions, all of them specifically named. On the first day of the tenth month they sat down to begin the inquiry,
17 A rana ta farko ga watan farko, suka gama da bincike duk waɗanda suka auri baƙin mata.
and by the first day of the first month they had finished handling all the cases of men who had married foreign women.
18 A cikin zuriyar firistoci, ga waɗanda suka auri mata baƙi. Daga zuriyar Yeshuwa ɗan Yozadak da’yan’uwansa, akwai Ma’asehiya, da Eliyezer, da Yarib, da Gedaliya.
Among the descendants of the priests, the following had married foreign women: from the sons of Jeshua son of Jozadak, and his brothers Maaseiah, Eliezer, Jarib, and Gedaliah.
19 (Su ne suka miƙa hannuwansu suka nuna sun yarda su kori matansu baƙi, kowannensu kuma ya ba da rago daga cikin garkensa don a miƙa hadaya don zunubi.)
They vowed to send their wives away, and they presented a ram from the flock as a guilt offering for their guilt.
20 Daga zuriyar Immer, akwai Hanani da Zebadiya.
From the sons of Immer: Hanani and Zebadiah.
21 Daga zuriyar Harim, akwai Ma’asehiya, Iliya, Shemahiya, Yehiyel da Uzziya.
From the sons of Harim: Maaseiah, Elijah, Shemaiah, Jehiel, and Uzziah.
22 Daga zuriyar Fashhur, akwai Eliyohenai, Ma’asehiya, Ishmayel, Netanel, Yozabad da Eleyasa.
From the sons of Pashhur: Elioenai, Maaseiah, Ishmael, Nethanel, Jozabad, and Elasah.
23 Cikin Lawiyawa, akwai Yozabad, Shimeyi, Kelaya (wato, Kelita), Fetahahiya, Yahuda, Eliyezer.
Among the Levites: Jozabad, Shimei, Kelaiah (or Kelita), Pethahiah, Judah, and Eliezer.
24 Daga mawaƙa, akwai Eliyashib. Daga masu tsaron ƙofofin haikali, akwai Shallum, Telem da Uri.
Among the singers: Eliashib. Among the gatekeepers: Shallum, Telem, and Uri.
25 Ga sunayen sauran mutanen Isra’ilan da suke da wannan laifi. Daga zuriyar Farosh, akwai Ramiya, da Izziya, Malkiya, Miyamin, Eleyazar, Malkiya da Benahiya.
Among the Israelites: From the sons of Parosh: Ramiah, Izziah, Malkijah, Mijamin, Eleazar, Hashabiah, and Benaiah.
26 Daga zuriyar Elam, akwai Mattaniya, Zakariya, Yehiyel, Abdi, Yeremot, da Iliya.
From the sons of Elam: Mattaniah, Zechariah, Jehiel, Abdi, Jeremoth, and Elijah.
27 Daga iyalin Zattu, akwai Eliyohenai, Eliyashib, Mattaniya Yeremot da Zabad da Aziza.
From the sons of Zattu: Elioenai, Eliashib, Mattaniah, Jeremoth, Zabad, and Aziza.
28 Daga zuriyar Bebai, akwai Yehohanan, Hananiya, Zabbai, da Atlai.
From the sons of Bebai: Jehohanan, Hananiah, Zabbai, and Athlai.
29 Daga zuriyar Bani, akwai Meshullam, Malluk, Adahiya, Yashub, Sheyal, da Ramot.
From the sons of Bani: Meshullam, Malluch, Adaiah, Jashub, Sheal, and Jeremoth.
30 Daga zuriyar Fahat-Mowab, akwai Adna, Kelal, Benahiya, Ma’asehiya, Mattaniya, Bezalel, Binnuyi, da Manasse.
From the sons of Pahath-moab: Adna, Kelal, Benaiah, Maaseiah, Mattaniah, Bezalel, Binnui, and Manasseh.
31 Daga zuriyar Harim, akwai Eliyezer, Isshiya, Malkiya, Shemahiya, Simeyon,
From the sons of Harim: Eliezer, Ishijah, Malkijah, Shemaiah, Shimeon,
32 Benyamin, Malluk da Shemariya.
Benjamin, Malluch, and Shemariah.
33 Daga zuriyar Hashum, akwai Mattenai, da Mattatta, Zabad, Elifelet, Irmai, Manasse, da Shimeyi.
From the sons of Hashum: Mattenai, Mattattah, Zabad, Eliphelet, Jeremai, Manasseh, and Shimei.
34 Daga zuriyar Bani, akwai Ma’adai, Amram, Yuwel,
From the sons of Bani: Maadai, Amram, Uel,
35 Benahiya, Bedeya, Keluhi,
Benaiah, Bedeiah, Keluhi,
36 Baniya, Meremot, Eliyashib,
Vaniah, Meremoth, Eliashib,
37 Mattaniya, Mattenai da Ya’asu.
Mattaniah, Mattenai, and Jaasu.
38 Daga zuriyar Binnuyi, akwai Shimeyi,
From the sons of Binnui: Shimei,
39 Shelemiya, Natan, Adahiya,
Shelemiah, Nathan, Adaiah,
40 Maknadebai, Shashai, Sharai,
Macnadebai, Shashai, Sharai,
41 Azarel, Shelemiya, da Shemariya,
Azarel, Shelemiah, Shemariah,
42 Shallum da Amariya da Yusuf.
Shallum, Amariah, and Joseph.
43 Daga zuriyar Nebo, akwai Yehiyel, Mattitiya, Zabad, Zebina, Yaddai, Yowel da Benahiya.
From the sons of Nebo: Jeiel, Mattithiah, Zabad, Zebina, Jaddai, Joel, and Benaiah.
44 Dukan waɗannan sun auri baƙin mata, waɗansunsu suna da’ya’ya.
All of these men listed had married foreign women. They divorced them and sent them away with their children.