< Ezra 1 >

1 A shekara ta farko ta mulkin sarkin Farisa, wato, sarki Sairus, domin a cika maganar Ubangiji da aka yi ta bakin Irmiya, sai Ubangiji ya taɓa zuciyar Sairus sarkin Farisa ya yi shela a duk fāɗin ƙasarsa, ya kuma rubuta cewa,
ובשנת אחת לכורש מלך פרס לכלות דבר יהוה מפי ירמיה העיר יהוה את רוח כרש מלך פרס ויעבר קול בכל מלכותו וגם במכתב לאמר
2 “Ga abin da Sairus sarkin Farisa yake shela, “‘Ubangiji Allah na sama ya ba ni iko in yi mulkin duniya duka, ya kuma zaɓe ni in gina masa haikali a Urushalima cikin Yahuda.
כה אמר כרש מלך פרס--כל ממלכות הארץ נתן לי יהוה אלהי השמים והוא פקד עלי לבנות לו בית בירושלם אשר ביהודה
3 Duk wanda yake nasa a cikinku bari Allahnsa yă kasance tare da shi, bari yă tafi Urushalima cikin Yahuda yă gina haikalin Ubangiji, Allah na Isra’ila, Allah wanda yake a Urushalima.
מי בכם מכל עמו יהי אלהיו עמו ויעל לירושלם אשר ביהודה ויבן את בית יהוה אלהי ישראל--הוא האלהים אשר בירושלם
4 Duk inda akwai mutumin Yahuda da ya rage, sai mutanen da suke zama kusa da shi, su taimake shi da azurfa, da zinariya, da kaya, da kuma dabbobi, tare da kyautai na yardar rai saboda Gidan Allah wanda yake a Urushalima.’”
וכל הנשאר מכל המקמות אשר הוא גר שם--ינשאוהו אנשי מקמו בכסף ובזהב וברכוש ובבהמה עם הנדבה--לבית האלהים אשר בירושלם
5 Sai shugabannin zuriyar Yahuda da na Benyamin, da firistoci da Lawiyawa, duk wanda Allah ya taɓa zuciyarsa, suka shirya don su je su gina haikalin Ubangiji a Urushalima.
ויקומו ראשי האבות ליהודה ובנימן והכהנים והלוים לכל העיר האלהים את רוחו לעלות לבנות את בית יהוה אשר בירושלם
6 Dukan maƙwabtansu kuwa suka taimake su da gudummawa na kayan azurfa da na zinariya, da kaya, da dabbobi, da kuma kyautai masu daraja bisa bayarwar yardar rai da suka yi.
וכל סביבתיהם חזקו בידיהם בכלי כסף בזהב ברכוש ובבהמה ובמגדנות--לבד על כל התנדב
7 Sai sarki Sairus ya fitar da kayan da suke na haikalin Ubangiji waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga Urushalima ya sa a haikalin allahnsa.
והמלך כורש הוציא את כלי בית יהוה אשר הוציא נבוכדנצר מירושלם ויתנם בבית אלהיו
8 Sairus sarkin Farisa ya sa Mitredat ma’aji ya ƙirga su a gaban Sheshbazzar ɗan sarkin Yahuda.
ויוציאם כורש מלך פרס על יד מתרדת הגזבר ויספרם לששבצר הנשיא ליהודה
9 Ga lissafin kayan. Manyan kwanonin zinariya guda 30 Manyan kwanonin azurfa guda 1,000 Wuƙaƙe guda 29
ואלה מספרם אגרטלי זהב שלשים אגרטלי כסף אלף מחלפים תשעה ועשרים
10 Waɗansu kwanonin zinariya guda 30 Waɗansu kwanonin azurfa guda 410 da waɗansu kayayyaki guda 1,000
כפורי זהב שלשים-- כפורי כסף משנים ארבע מאות ועשרה כלים אחרים אלף
11 Dukan kayayyakin zinariya da na azurfa sun kai 5,400. Sheshbazzar ya kawo kayayyakin nan duka tare da shi lokacin da kamammun suka hauro daga Babilon zuwa Urushalima.
כל כלים לזהב ולכסף חמשת אלפים וארבע מאות הכל העלה ששבצר עם העלות הגולה--מבבל לירושלם

< Ezra 1 >