< Ezekiyel 6 >

1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
La parole du Seigneur me fut adressée en ces termes:
2 “Ɗan mutum, ka kafa idonka a kan duwatsun Isra’ila; ka yi annabci a kansu
"Fils de l’homme, tourne ta face vers les montagnes d’Israël et prophétise sur elles.
3 ka ce, ‘Ya ku duwatsun Isra’ila, ku ji maganar Ubangiji Mai Iko Duka. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce wa duwatsu da tuddai, ga rafuffuka da kuma kwaruruka. Ina shirin kawo takobi a kanku, kuma zan hallaka masujadanku.
Tu diras: Montagnes d’Israël, écoutez la parole du Seigneur Dieu! Ainsi parle le Seigneur Dieu aux montagnes et aux collines, aux torrents et aux vallées: Voici, je vais amener sur vous le glaive et je ruinerai vos hauts-lieux.
4 Za a ragargaza bagadanku a kuma farfasa bagadanku na ƙone turare; zan kuma kashe mutanenku a gaban gumakanku.
Vos autels seront dévastés, vos statues solaires seront brisées, et je ferai tomber vos morts devant vos idoles.
5 Zan shimfiɗa gawawwakin Isra’ilawa a gaban gumakansu, in kuma watsar da ƙasusuwanku kewaye da bagadanku.
Et je mettrai les cadavres des enfants d’Israël devant leurs idoles et je disperserai vos ossements autour de vos autels.
6 Duk inda kuke zama, garuruwa za su zama kango, za a kuma ragargaza masujadai, saboda bagadanku su rurrushe su zama kango, a kuma farfasa gumakanku su lalace, za a rurrushe bagadan ƙone turarenku, a kuma shafe dukan abin da kuka yi.
Dans tous vos établissements, les villes seront dévastées, et les hauts-lieux désolés, afin que soient ruinés et désolés vos autels, que soient brisées et anéanties vos idoles, que soient rasées vos statues solaires, et que soient effacées vos oeuvres.
7 Za a kashe mutanenku a cikinku, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.
Des morts tomberont au milieu de vous, et vous saurez que je suis le Seigneur.
8 “‘Amma zan bar waɗansu, gama waɗansunku za su tsere wa takobi sa’ad da aka watsar da ku a cikin ƙasashe da al’ummai.
Et si j’en épargne parmi vous qui échapperont au glaive parmi les nations, quand vous serez dispersés dans les pays,
9 Sa’an nan a cikin al’ummai inda aka kai ku zaman bauta, waɗanda suka a tsere za su tuna da ni, yadda raina ya ɓaci ta wurin zukatansu marasa imani, waɗanda suka rabu da ni, da kuma ta wurin idanunsu, waɗanda suka yi sha’awace-sha’awacen gumakansu. Za su ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwan da suka aikata.
ces survivants parmi vous se souviendront de moi chez les nations où ils seront captifs, de moi qui aurai brisé leur coeur infidèle, qui s’est détourné de moi, et leurs yeux qui s’égaraient vers leurs idoles; et ils éprouveront le dégoût d’eux-mêmes à cause des méfaits qu’ils ont commis, par toutes leurs abominations.
10 Za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji; ba a banza na ce zan kawo musu wannan masifa ba.
Ils sauront que je suis le Seigneur, que je n’ai pas parlé en vain en les menaçant de ce malheur."
11 “‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce ku tafa hannuwanku tare ku kuma taka ƙafafunku ku yi ihu ku ce, “Kaito!” Saboda dukan mugaye da kuma abubuwan banƙyama na gidan Isra’ila, gama za su mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba.
Ainsi a dit le Seigneur Dieu: "Frappe de la main et tape du pied et dis: "Hélas!" Au sujet de toutes les horreurs impies des gens de la maison d’Israël, qui tomberont par le glaive, par la famine et par la peste.
12 Wanda yake da nisa zai mutu da annoba, shi da yake kusa kuma zai mutu ta takobi, wanda kuma ya tsira aka kuma bari zai mutu da yunwa. Ta haka zan aukar da fushina a kansu.
Celui qui est loin mourra par la peste, celui qui est proche tombera sous le glaive, survivants et assiégés périront par la famine, et j’épuiserai ma fureur sur eux.
13 Za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da gawawwakin mutanensu suna kwance a kusa da gumakansu da kewaye da bagadansu, a kowane kan tudu mai tsawo da kuma a kan dukan kan duwatsu, a ƙarƙashin kowane inuwar itace da kuma kowane oak mai ganye, wuraren da suke ƙone turare masu ƙanshi wa dukan gumakansu.
Et vous saurez que je suis le Seigneur, quand leurs cadavres seront couchés au milieu de leurs idoles, autour de leurs autels, sur chaque haute colline, sur toutes les cimes des montagnes, sous chaque arbre verdoyant et sous chaque chêne touffu, en tout endroit où ils offraient une odeur agréable à toutes leurs idoles.
14 Zan kuma miƙa hannuna a kansu in mai da ƙasarsu kango daga hamadan Dibila, a duk inda suke zama. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.’”
J’Étendrai ma main sur eux et je ferai du pays une solitude et une ruine pire que le désert de Diblat, partout où ils seront établis, et ils sauront que je suis l’Eternel."

< Ezekiyel 6 >