< Ezekiyel 44 >
1 Sai mutumin ya komo da ni zuwa ƙofar waje na wuri mai tsarki, wadda take fuskantar gabas, tana kuwa a rufe.
領我回到聖殿朝東的外門,門卻關著。
2 Ubangiji ya ce mini, “Wannan ƙofar za tă kasance a rufe. Ba za a buɗe ta ba; ba wanda zai shiga ta wurinta. Za tă kasance a rufe domin Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya shiga ta wurinta.
他對我說:「這門必關閉不開,任何人不得由此門而入,因為上主以色列的天主已由此門而入,為此常應關閉。
3 Sarki kansa ne kaɗai zai zauna a hanyar shiga don yă ci a gaban Ubangiji. Zai shiga ta hanyar shirayin hanyar shiga yă kuma fita a wannan hanya.”
至於元首,因為他是元首,惟有他可坐在裏面,在上主前進食;他由門廊的路而入,亦由原路而出。」
4 Sa’an nan mutumin ya kawo ni ta hanyar ƙofar arewa zuwa gaban haikali. Na duba na kuma ga ɗaukakar Ubangiji tana cika haikalin Ubangiji, sai na fāɗi rubda ciki.
以後,他領我由北門到聖殿,我一看,看見上主的光榮上主的殿,我便伏地掩面。
5 Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, ka lura sosai, ka saurara sosai ka kuma mai da hankali ga kome da na faɗa maka game da dukan ƙa’idodi game da haikalin Ubangiji. Ka lura sosai da ƙofar shigar haikali da kuma dukan ƙofofin wuri mai tsarki.
上主對我說:「人子,我對你所說上主殿內的所有定和法律,你要留心,要眼看耳聽,又要注意准入聖殿的規則。
6 Faɗa wa’yan tawayen gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ayyukan banƙyamarku sun isa haka, ya gidan Isra’ila!
你對叛逆的以色列家族說:吾主上主這樣說:以色列家族,你們所行的一切醜惡之事,該夠了吧!
7 Ban da dukan sauran ayyukanku na banƙyama, kun kawo baƙi marasa kaciya a zuciya da jiki a wurina mai tsarki, kun kuma ƙazantar da haikalina yayinda kuke miƙa mini abinci, kitse da kuma jini, kun kuma karya alkawarina.
當你們奉獻給我食品、脂肪和牲血時,竟引領心身未受割損的外方人進入我的聖所,褻瀆我的殿宇;這樣以你們的一切醜惡,破壞了我的盟約。
8 A maimakon yin ayyukanku bisa ga abubuwana masu tsarki, kun sa waɗansu su lura da wurina mai tsarki.
你們的既不在我聖所內供職,卻派他們代你們在我聖所內供職。
9 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ba baƙo marar kaciya a zuciya da jiki da zai shiga wurina mai tsarki, kai, har ma da baƙin da suke zama a cikin Isra’ila.
為此吾主上主這樣說:一切心身未受割損的外邦人,以及所有在以色列子民中的外邦人,不得進入我的聖所。
10 “‘Lawiyawan da suka yi nesa da ni sa’ad da Isra’ila suka kauce da kuma waɗanda suka karkata daga gare ni suka bi gumakansu, dole su ɗauki alhakin zunubinsu.
至於肋未人,當以色列墮落,離開我而追隨他們的偶像時,他們也脫離了我,他們必要承認自己的罪債。
11 Za su iya yin hidima a wurina mai tsarki, suna lura da ƙofofin haikali suna kuma hidima a cikinsu; za su iya yankan hadayun ƙonawa da sadaka don mutane su kuma tsaya a gaban mutane su yi musu hidima.
他們在我聖所內供職,只能充當看守殿門的,作的侍役,為百姓宰殺全燔祭和其他祭牲,站在他們面前,給他們服務。
12 Amma domin sun yi musu hidima a gaban gumakansu suka sa gidan Isra’ila ya yi zunubi, saboda haka na ɗaga hannu na rantse cewa dole su ɗauki alhakin zunubinsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
因為他們曾在百姓的偶像前給他們服務過,做了以色列家族的胖腳石,為此我必舉手反對他們──吾主上主的斷語──他們必要承擔自己的罪債。
13 Ba za su yi kusa don su yi hidima kamar firistoci ko su zo kusa da abubuwana masu tsarki ko hadayuna mafi tsarki ba; dole su sha kunya saboda ayyukansu na banƙyama.
他們不得走近我,也不得接我的的一切聖物,和至聖之物;反要自己的羞辱和所行的一切醜惡。
14 Duk da haka zan sa su su lura da ayyukan haikali da kuma dukan ayyukan da za a yi a cikinsa.
我只委派他們在聖殿供職,服各種勞役,做其中應做的一切事務。
15 “‘Amma firistoci, waɗanda suke Lawiyawa kuma zuriyar Zadok waɗanda suka yi aminci ta wurin yin ayyukansu a wurina mai tsarki sa’ad da Isra’ilawa suka kauce daga gare ni, su ne za su zo kusa don hidima a gabana; za su tsaya a gabana don miƙa hadayun kitse da jini, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
惟有那些在以色列子民墮落我時,仍然為我的聖所供職的匝多克的兒子,肋未司祭們,可走近我,服事我,侍立我前,給我奉獻脂油與牲血──吾主上主的斷語──
16 Su ne kaɗai za su shiga wurina mai tsarki; su ne kaɗai za su zo kusa da teburina don yin hidima a gabana su kuma yi hidimata.
他們可進入我的聖所,起近我的祭桌,服事我,奉行給我供職的事。
17 “‘Sa’ad da suka shiga ƙofofin fili na can ciki, dole su sa tufafin lilin; kada su sa wani rigar da aka yi da ulu yayinda suke hidima a ƙofofin fili na can ciki da cikin haikali.
幾時他們進入內院的門,應身穿麻衣;當他們在內院門內或在聖殿供職時,不可穿羊毛衣。
18 Za su naɗa rawunan lilin a kawunansu, su kuma sa wandunan lilin. Kada su sa wani abin da zai sa su yi zuffa.
他們頭上應戴麻布頭巾,腰間應穿麻巾褲子,不可穿容易出汗的衣服。
19 Sa’ad da suka fita daga haikali zuwa fili na waje inda mutane suke, sai su tuɓe rigunan da suka yi hidima da su su bar su a tsarkakan ɗakuna, su sa waɗansu riguna, don kada su tsarkake mutane ta wurin rigunansu.
但他們幾時要出去到外院百姓那裏時,應脫去供職的衣服,放在聖所的廂房內,穿上別的衣服,免得因自己的祭服使百姓沾污聖潔。
20 “‘Ba za su aske kawunansu ko su bar gashin kansu ya yi tsayi ba, amma sai su sausaye gashin kansu.
你們不可剃頭,也不可讓頭髮自由生長,應該修剪頭髮。
21 Kada firist ya sha ruwan inabi sa’ad da zai shiga fili na can ciki.
任何司祭要進入內院時,不可飲酒。
22 Kada su auri gwauruwa ko macen da aka sāke; za su auri budurwai ne kaɗai na Isra’ilawa ko gwaurayen firistoci.
他們不可娶寡婦或棄婦為妻,應娶以色列家族的處女為妻;或娶司祭的寡婦。
23 Za su koyar da mutanena bambanci tsakanin tsarki da rashin tsarki su kuma nuna musu yadda za su bambanta marar tsarki da mai tsarki.
廿應教訓我的百姓 區別聖與俗,知道潔與不潔。
24 “‘A duk wani rashin jituwa, firistoci za su zama alƙalai su kuma yanke magana bisa ga farillaina. Za su kiyaye dokokina da ƙa’idodina a dukan ƙayyadaddun bukukkuwana, su kuma kiyaye Asabbataina da tsarki.
在訴訟上,他們應充任裁判,按我的法律定斷;他們在我的各種慶節上,應遵守規我的法律和規律,又應聖化我的安息日。
25 “‘Firist ba zai ƙazantar da kansa ta wurin zuwa kusa da gawa ba; amma, in gawar mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ko ɗansa ko’yarsa, ko ɗan’uwansa ko’yar’uwarsa ce, to, ba zai ƙazantar da kansa ba.
他們不可走近死人,免得沾染不潔;但為父母子女、兄弟和未嫁的姊妹,可自染不潔。
26 Bayan ya tsarkaka, dole yă jira har kwana bakwai.
在他取潔以後,再過七天,
27 A ranar da ya shiga fili na can ciki na wuri mai tsarki don hidima a wuri mai tsarki, zai miƙa hadaya don zunubi saboda kansa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
他要進入聖所,進內院,為在聖所內供職的那一天,應奉獻贖罪祭──吾主上主的斷語──
28 “‘Ni ne kaɗai zan zama abin gādon da firistoci za su kasance da shi. Kada ka ba su wani mallaka a Isra’ila; zan zama mallakarsu.
他們不可有產業;在以色列也不可分給他們地業我是他們的地業。
29 Za su ci hadaya ta gari, hadaya don zunubi da hadaya don laifi; da kuma kowane keɓaɓɓen abu a Isra’ila da za a ba wa Ubangiji zai zama nasu.
他們可以吃素餐,贖罪祭和贖過祭:凡在以色列所獻的禁物,都應歸於他們。
30 Mafi kyau na nunan farinku da kuma dukan kyautanku na musamman za su zama na firistoci. Za ku ba su rabo na fari na ɓarzajjen hatsinku saboda albarka ta kasance a gidanku.
各種初熟之物,和你們藉舉祭所獻的一切祭物,都應歸於司祭;此外,將你們粗麥麵中最好的一份,分與司祭,好叫祝福降在你們家庭中。
31 Firistoci ba za su ci mushen tsuntsu ko na dabba ba, ba kuwa za su ci waɗanda namun jeji suka kashe ba.
凡自然死或被猛獸撕裂的飛禽走獸,司祭都不可吃。」