< Ezekiyel 43 >

1 Sai mutumin ya kawo ni ƙofar da take fuskantar gabas,
Afterward he brought me to the gate, even the gate that looks towards the east.
2 sai na ga ɗaukakar Allah na Isra’ila tana tahowa daga gabas. Muryarsa ta yi kamar rurin ruwaye masu gudu, ƙasa kuma ta haskaka da ɗaukakarsa.
Behold, the glory of the God of Israel came from the way of the east. His voice was like the sound of many waters; and the earth was illuminated with his glory.
3 Wahayin da na gani ya yi kamar wahayin da na gani sa’ad da ya zo don yă hallaka birnin, kamar kuma wahayin da na gani kusa da Kogin Kebar, na kuwa fāɗi rubda ciki.
It was like the appearance of the vision which I saw, even according to the vision that I saw when I came to destroy the city; and the visions were like the vision that I saw by the river Chebar; and I fell on my face.
4 Ɗaukakar Ubangiji ta shiga haikali ta ƙofar da take fuskantar gabas.
The LORD’s glory came into the house by the way of the gate which faces towards the east.
5 Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama ya kawo ni cikin fili na can ciki, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika haikalin.
The Spirit took me up and brought me into the inner court; and behold, the LORD’s glory filled the house.
6 Yayinda mutumin yana tsaye kusa da ni, na ji wani yana magana da ni daga cikin haikalin.
I heard one speaking to me out of the house, and a man stood by me.
7 Ya ce, “Ɗan mutum, wannan shi ne kursiyina da wurin tafin ƙafafuna. A nan ne zan zauna a cikin Isra’ilawa har abada. Gidan Isra’ila ba zai ƙara ɓata sunana mai tsarki ba, ko su ko sarakunansu, ta wurin karuwanci da gumakan da ba su da rai, sarakunansu a masujadan kan tudu.
He said to me, “Son of man, this is the place of my throne and the place of the soles of my feet, where I will dwell amongst the children of Israel forever. The house of Israel will no more defile my holy name, neither they nor their kings, by their prostitution and by the dead bodies of their kings in their high places;
8 Sa’ad da suka sa madogarar ƙofarsu kusa da madogarar ƙofata, da katanga kawai a tsakanina da su, sun ɓata sunana mai tsarki ta wurin ayyukansu masu banƙyama. Saboda haka na hallaka su cikin fushina.
in their setting of their threshold by my threshold and their door post beside my door post. There was a wall between me and them; and they have defiled my holy name by their abominations which they have committed. Therefore I have consumed them in my anger.
9 Yanzu bari su kawar da karuwancinsu da gumakansu waɗanda ba su da rai na sarakunansu daga gabana, zan kuwa zauna a cikinsu har abada.
Now let them put away their prostitution, and the dead bodies of their kings far from me. Then I will dwell amongst them forever.
10 “Ɗan mutum, ka bayyana haikalin ga mutanen Isra’ila, don su ji kunya saboda zunubansu. Bari su yi la’akari da fasalin,
“You, son of man, show the house to the house of Israel, that they may be ashamed of their iniquities; and let them measure the pattern.
11 kuma in suka ji kunyar abubuwan da suka aikata, sai ka sanar musu fasalin haikalin da shirye-shiryensa, ƙofofinsa na shiga da fita, dukan fasalinsa da dukan ƙa’idodinsa da dokokinsa. Ka rubuta waɗannan a gabansu saboda su yi aminci da fasalinsa su kuma kiyaye dukan ƙa’idodinsa.
If they are ashamed of all that they have done, make known to them the form of the house, its fashion, its exits, its entrances, its structure, all its ordinances, all its forms, and all its laws; and write it in their sight, that they may keep the whole form of it, and all its ordinances, and do them.
12 “Wannan ita ce dokar haikalin. Dukan filin da yake kewaye a kan dutsen, zai zama wuri mafi tsarki. Dokar haikalin ke nan.
“This is the law of the house. On the top of the mountain the whole limit around it shall be most holy. Behold, this is the law of the house.
13 “Waɗannan su ne aune-aunen bagade a tsawon kamu, wannan kamu shi ne kamun tafin hannu. Zurfin magudanar ruwansa kamu ɗaya ne fāɗinsa kuma kamu ɗaya, tare da da’ira kamun tafi ɗaya kewaye da gefensa. Wannan kuma shi ne tsayin bagaden.
“These are the measurements of the altar by cubits (the cubit is a cubit and a hand width): the bottom shall be a cubit, and the width a cubit, and its border around its edge a span; and this shall be the base of the altar.
14 Daga lambatun da yake a ƙasa har zuwa ƙaramin mahaɗin da yake ƙasa wanda ya kewaye bagade, tsayinsa kamu biyu ne, fāɗinsa kuma kamu guda. Daga ƙaramin mahaɗi zuwa babban mahaɗin wanda ya kewaye bagade, zai zama kamu huɗu, fāɗinsa kuwa kamu ɗaya.
From the bottom on the ground to the lower ledge shall be two cubits, and the width one cubit; and from the lesser ledge to the greater ledge shall be four cubits, and the width a cubit.
15 Murhun bagaden kamu huɗu ne, akwai ƙahoni guda huɗu sun miƙe sama daga murhun.
The upper altar shall be four cubits; and from the altar hearth and upward there shall be four horns.
16 Murhun bagaden murabba’i ne, tsawonsa kamu goma sha biyu, fāɗinsa kuma kamu goma sha biyu.
The altar hearth shall be twelve cubits long by twelve wide, square in its four sides.
17 Gefen bisa ma murabba’i ne, tsawonsa kamu goma sha huɗu fāɗinsa kuma kamu goma huɗu, da da’ira da yake da fāɗin rabin kamu da magudanan ruwa kamu guda kewaye. Matakan bagaden suna fuskantar gabas.”
The ledge shall be fourteen cubits long by fourteen wide in its four sides; and the border about it shall be half a cubit; and its bottom shall be a cubit around; and its steps shall look towards the east.”
18 Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa waɗannan su ne za su zama ƙa’idodi don yin hadaya ta ƙonawa da yayyafawar jini a kan bagaden sa’ad da aka gina shi.
He said to me, “Son of man, the Lord GOD says: ‘These are the ordinances of the altar in the day when they make it, to offer burnt offerings on it, and to sprinkle blood on it.
19 Za ka ba da ɗan bijimi a matsayin hadaya ta ƙonawa ga firistoci, waɗanda suke Lawiyawa, na iyalin Zadok, waɗanda suke zuwa kusa don hidima a gabana, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
You shall give to the Levitical priests who are of the offspring of Zadok, who are near to me, to minister to me,’ says the Lord GOD, ‘a young bull for a sin offering.
20 Za ka ɗibi jininsa ka zuba shi a ƙahoni huɗu na bagaden a gefen bisa da kuma kewaye da da’irar, ta haka za ka tsarkake bagaden ka kuma yi kafara dominsa.
You shall take of its blood and put it on its four horns, and on the four corners of the ledge, and on the border all around. You shall cleanse it and make atonement for it that way.
21 Za ka ɗauki bijimi na hadaya don zunubi ka ƙone shi a sashen da aka shirya na haikalin a wani wuri waje da wuri mai tsarki.
You shall also take the bull of the sin offering, and it shall be burnt in the appointed place of the house, outside of the sanctuary.
22 “A rana ta biyu za ka miƙa bunsuru marar lahani domin hadaya don zunubi, za a kuma tsarkake bagaden yadda aka yi da bijimin.
“On the second day you shall offer a male goat without defect for a sin offering; and they shall cleanse the altar, as they cleansed it with the bull.
23 Sa’ad da ka gama tsarkake shi, sai ka miƙa ɗan bijimi da kuma rago daga cikin garke, dukansu marasa lahani.
When you have finished cleansing it, you shall offer a young bull without defect and a ram out of the flock without defect.
24 Za ka miƙa su a gaban Ubangiji, firistoci kuma za su barbaɗe gishiri a kansu su kuma miƙa su kamar hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.
You shall bring them near to the LORD, and the priests shall cast salt on them, and they shall offer them up for a burnt offering to the LORD.
25 “Kwana bakwai za ka tanada bunsuru kullum domin hadaya don zunubi; za ka kuma tanada ɗan bijimi da rago daga garke, dukansu marasa lahani.
“Seven days you shall prepare every day a goat for a sin offering. They shall also prepare a young bull and a ram out of the flock, without defect.
26 Kwana bakwai za su yi kafara saboda bagaden su kuma tsarkake shi; ta haka za su keɓe shi.
Seven days shall they make atonement for the altar and purify it. So shall they consecrate it.
27 A ƙarshen waɗannan kwanaki, daga rana ta takwas zuwa gaba, firistoci za su miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama a kan bagade. Sa’an nan zan karɓe ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
When they have accomplished the days, it shall be that on the eighth day and onward, the priests shall make your burnt offerings on the altar and your peace offerings. Then I will accept you,’ says the Lord GOD.”

< Ezekiyel 43 >