< Ezekiyel 42 >
1 Sai mutumin ya kai ni wajen arewa zuwa cikin filin da yake waje ya kuma kawo ni ɗakunan da suke ɗaura da filin haikalin da yake a gefen arewa.
2 Tsawon ginin da yake fuskantar arewa kamu ɗari ne fāɗinsa kuma kamu hamsin.
3 A gaban kamu ashirin na filin da yake can ciki da kuma a gaban daɓen filin da yake waje, akwai rumfuna a jere waɗanda suke fuskantar juna hawa uku-uku.
4 A gaban ɗakunan akwai hanya a can ciki mai fāɗin kamu goma, tsawonta kuma kamu ɗari. Ƙofofinsu suna wajen arewa.
5 Ɗakunan da suke bisa ba su da fāɗi, gama mataki hawan benen ya cinye wuri fiye da a ɗakunan da suke a hawa na ƙasa da na tsakiya.
6 Ɗakunan da suke a hawa na uku ba su da ginshiƙai, yadda filayen suka kasance da su, saboda haka suka matsu fiye da waɗanda suke a hawa na ƙasa da na tsakiya.
7 Akwai katanga wadda take waje, wadda ta yi hannun riga da ɗakunan filin waje; ta miƙe a gaban ɗakunan, tsawonta kamu hamsin ne.
8 Yayinda tsawon jerin ɗakunan da suke a gefe kusa da filin da yake waje kamu hamsin ne, tsawon jerin ɗakunan da suke a gefen da yake kurkusa da wuri mai tsarki kamu ɗari ne.
9 Ɗakunan da suke can ƙasa suna da ƙofar shiga a wajen gabas in za a shiga cikinsu daga filin da yake waje.
10 A wajen kudu a ta katangar filin da yake waje, kusa da filin haikali da yake ɗaura da katangar waje, akwai ɗakuna
11 da hanya a gabansu. Waɗannan sun yi kama da ɗakunan da suke wajen arewa; tsawonsu da fāɗinsu duk iri ɗaya ne, da irin mafita ɗaya da kuma yadda aka shirya su. Sun yi kama da ƙofofin da suke wajen arewa
12 haka ma ƙofofin ɗakunan a wajen kudu. Akwai ƙofa a farkon hanyar da ta yi hannun riga da ɗayan katangar da ta miƙe wajen gabas, inda za a iya shiga ɗakunan.
13 Sai ya ce mini, “Ɗakunan arewa da na kudu waɗanda suke fuskantar filin haikali ɗakunan firistoci ne, inda firistocin da suke kusaci Ubangiji za su ci hadayu mafi tsarki. A can za su ajiye hadayu mafi tsarki, hadayu na gari, hadayu na zunubi da hadayu na laifi, gama wuri mai tsarki ne.
14 Da zarar firistoci suka shiga wuri mai tsarki, ba za su fita zuwa filin da yake waje ba sai sun tuɓe rigunan da suka yi hidima da su, gama waɗannan masu tsarki ne. Za su sa waɗansu riguna kafin su kusaci wuraren da mutane suke.”
15 Da ya gama auna filin da yake cikin haikali, sai ya fitar da ni ta ƙofar gabas ya auna dukan filin kewaye.
16 Ya auna gefen gabas da karan awo; ya samu kamu ɗari biyar.
17 Ya auna gefen arewa da karan awon; ya samu kamu ɗari biyar.
18 Ya auna gefen kudu da karan awon; ya samu kamu ɗari biyar.
19 Sa’an nan ya juya zuwa gefen yamma ya auna shi da karan awon, ya samu kamu ɗari biya.
20 Ta haka ya auna dukan kusurwoyi huɗu. Filin yana da katanga kewaye da shi, tsawon kamu ɗari biyar, fāɗin kuma kamu ɗari biyar don yă raba wuri mai tsarki daga wuri marar tsarki.