< Ezekiyel 39 >
1 “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan Gog ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin Meshek da Tubal.
"You, son of man, prophesy against Gog, and say, 'Thus says YHWH: "Look, I am against you, Gog, chief prince of Meshech and Tubal:
2 Zan juya ka in kuma ja ka. Zan kawo ka daga can arewa in aike ka don ka fāɗa wa duwatsun Isra’ila.
and I will turn you around, drag you along, and bring you up from the remotest parts of the north, and bring you against the mountains of Israel.
3 Sa’an nan zan karya bakan da take a hannun hagunka, in sa kibiyoyin da suke a hannun damanka su fāɗi.
Then I will strike your bow out of your left hand, and will make your arrows fall from your right hand.
4 A kan duwatsun Isra’ila za ka fāɗi, kai da sojojinka da kuma al’ummai da suke tare da kai. Zan bayar da kai ka zama abinci ga tsuntsaye da namun jeji masu cin nama.
You will fall on the mountains of Israel, you and all your troops and the people who are with you. I will give you to birds of prey of every king and to the beasts of the field to be devoured.
5 Za ka mutu a fili, gama haka ni na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
You will fall in the open field; for I have spoken," says YHWH.
6 Zan aika da wuta a kan Magog da kuma a kan waɗanda suke zama lafiya a bakin teku, za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.
And I will send a fire on Magog and on those who dwell securely in the coastlands; then they will know that I am YHWH.
7 “‘Zan sanar da sunana mai tsarki a cikin mutanena Isra’ila. Ba zan ƙara bari a ɓata sunana mai tsarki ba, kuma al’ummai za su san cewa Ni Ubangiji Mai Tsarki ne a cikin Isra’ila.
"'And I will make my holy name known in the midst of my people Israel, and I will not allow my holy name to be profaned anymore. And the nations shall know that I am YHWH, the Holy One in Israel.
8 Yana zuwa! Tabbatacce zai faru, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ranar da na yi magana ke nan.
Look, it is coming and it will happen, says YHWH. This is the day I have spoken about.
9 “‘Sa’an nan waɗanda suke zama a garuruwan Isra’ila za su fita su tattara makamai su hura wuta da su su kuma ƙone su, manya da ƙanana garkuwoyi, bakkuna da kibiyoyi, kulake da māsu. Shekara bakwai za su yi amfani da su don hura wuta.
"'Then those who dwell in the cities of Israel shall go out and make fires of the weapons and burn them, both the shields and bucklers, bows and the arrows, war clubs and spears, and they shall make fires of them for seven years,
10 Ba za su yi wahalar zuwa jeji don neman itacen hura wuta ba, domin za su yi amfani da makamai don hura wuta. Za su kuma washe waɗanda suka washe su ganima, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
so that they shall no need to take wood out of the field or gather firewood from the forests, because they shall make fires of the weapons; and they will take the spoil from those who despoiled them, and plunder those who plundered them, says YHWH.
11 “‘A ranar zan yi wa Gog makabarta a cikin Isra’ila, a kwarin waɗanda suke tafiya wajen gabashin Teku. Za tă tare hanyar matafiya, domin za a binne Gog da dukan mutanensa a can. Ta haka za a kira wurin Kwarin Haman Gog.
"'And it shall happen on that day that I will give to Gog a place for burial in Israel, the Valley of the Travelers east of the sea; and it shall block the way of the travelers. So they shall bury Gog and all his multitude; and they shall call it The Valley of Hamon Gog.
12 “‘Watanni bakwai gidan Isra’ila zai yi ta binne su don a tsarkake ƙasar.
For seven months the house of Israel will be burying them, in order to cleanse the land.
13 Dukan mutanen ƙasar za su binne su, kuma ranar da za a ɗaukaka ni za tă zama ranar tuni a gare su, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Yes, all the people of the land shall bury them, and it shall be a memorial for them on the day that I show my glory, says YHWH.
14 “‘Za a ɗauki mutane kullum don tsabtacce ƙasar. Waɗansu za su ratsa ƙasar, ƙari da waɗannan, waɗansu za su binne gawawwakin da suka ragu a ƙasar. A ƙarshen watanni bakwai ɗin za su fara bincikensu.
And they shall designate men to travel through the land regularly, burying those who remain on the face of the land, in order to cleanse it. At the end of seven months they shall make a search.
15 Yayinda suke ratsa ƙasar, in waninsu ya ga ƙashin mutum, zai kafa shi kamar alama a gefe sai masu haƙa kabari sun binne shi a Kwarin Haman Gog.
As they go through the land and anyone sees a human bone, he will put a marker next to it until the gravediggers have buried it in the Valley of Hamon Gog.
16 Akwai wani garin da ake kira Hamona zai kasance a can. Ta haka za su tsabtacce ƙasar.’
Moreover, Hamonah will be the name of a city. Thus they shall cleanse the land.'
17 “Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ka gayyato kowane irin tsuntsu da dukan namun jeji, ‘Ku taru ku kuma zo wuri ɗaya daga ko’ina don hadayar da nake shirya muku, babbar hadaya a kan duwatsun Isra’ila. A can za ku ci nama ku kuma sha jini.
"And as for you, son of man, thus says YHWH: Speak to every kind of bird and to all the wild animals, 'Assemble and come, gather from all around to my sacrifice which I am going to sacrifice for you, a great sacrifice on the mountains of Israel, that you may eat flesh and drink blood.
18 Za ku ci naman manyan mutane ku kuma sha jinin sarakunan duniya sai ka ce an yanka raguna da’yan tumaki, awaki da bijimai, dukansu turkakkun dabbobi daga Bashan.
You shall eat the flesh of the mighty, and drink the blood of the princes of the earth, of rams, of lambs, and of goats, of bulls, all of them fattened animals of Bashan.
19 A hadayar da nake shirya muku, za ku ci kitse sai kun ƙoshi ku kuma sha jini sai kun bugu.
And you shall eat fat until you are full, and drink blood until you are drunk, at my sacrifice which I have sacrificed for you.
20 A teburina za ku ci iya ƙoshiyarku da naman jama’a da kuma mahaya, manyan mutane da sojoji na kowane iri,’ in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
And you shall be filled at my table with horses and charioteers, with warriors and with all the soldiers,' says YHWH.
21 “Zan nuna ɗaukakata a cikin al’ummai, kuma dukan al’ummai za su ga hukuncin da zan yi da kuma hannu mai nauyin da zan ɗora a kansu.
"'And I will set my glory among the nations, and all the nations shall see my judgment when I have executed it and my hand when I lay it on them.
22 Daga wannan rana zuwa gaba gidan Isra’ila zai san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu.
So the house of Israel shall know that I am YHWH their God, from that day on.
23 Al’ummai kuma za su san cewa mutanen Isra’ila sun tafi zaman bauta saboda zunubinsu, domin sun yi rashin aminci gare ni. Saboda haka na kawar da fuskata daga gare su na miƙa su ga abokan gābansu, suka kuwa mutu ta takobi.
And the nations shall know that the house of Israel went into captivity for their iniquity, because they were unfaithful to me, so I hid my face from them, and I gave them into the hand of their adversaries, and all of them fell by the sword.
24 Na yi da su gwargwadon rashin tsabtarsu da laifofinsu, na kuma kawar da fuskata daga gare su.
I dealt with them according to their uncleanness and according to their transgressions, and I hid my face from them.'
25 “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan komo da Yaƙub daga zaman bauta zan kuma yi wa dukan Isra’ila jinƙai, zan kuma yi kishi saboda sunana mai tsarki.
"Therefore thus says YHWH: 'Now will I restore the fortunes of Jacob and have mercy on the whole house of Israel, and I will be jealous for my holy name.
26 Za su manta da kunyar da suka sha da dukan rashin amincin da suka nuna mini sa’ad da suke zama lafiya a ƙasarsu inda ba wanda zai tsorata su.
And they shall feel remorse for their disgrace and all the unfaithfulness they committed against me, when they dwell securely in their land with none to make them afraid.
27 Sa’ad da na komo da su daga al’ummai na kuma tattara su daga ƙasashen abokan gābansu, zan nuna kaina mai tsarki ta wurinsu a gaban al’ummai masu yawa.
When I have brought them back from the peoples and gathered them out of their enemies' lands, then I will be sanctified through them in the sight of the many nations.
28 Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu, gama ko da yake na tura su zaman bauta a cikin al’ummai, zan tattara su zuwa ƙasarsu, ba tare da barin wani a baya ba.
Then they will know that I am YHWH their God, because I sent them into exile among the nations, and then gathered them into their own land; and I will leave none of them there any more.
29 Ba zan ƙara kawar da fuskata daga gare su, gama zan zuba Ruhuna a kan gidan Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
And I will no longer hide my face from them, when I pour out my Spirit on the house of Israel,' says YHWH."