< Ezekiyel 37 >

1 Hannun Ubangiji yana a kaina, ya kuma fitar da ni ta wurin Ruhun Ubangiji ya sa ni a tsakiyar kwarin; yana cike da ƙasusuwa.
היתה עלי יד יהוה ויוצאני ברוח יהוה ויניחני בתוך הבקעה והיא מלאה עצמות
2 Ya sa na kai na komo a ciki, na kuma ga ƙasusuwa masu girma da yawa a ƙasar kwarin, ƙasusuwan da suka bushe ƙwarai.
והעבירני עליהם סביב סביב והנה רבות מאד על פני הבקעה והנה יבשות מאד
3 Sai ya tambaye ni cewa, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa za su iya rayu?” Ni kuwa na ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai kaɗai ka sani.”
ויאמר אלי--בן אדם התחיינה העצמות האלה ואמר אדני יהוה אתה ידעת
4 Sai ya ce mini, “Ka yi wa waɗannan ƙasusuwa annabci ka ce musu, ‘Busassun ƙasusuwa, ku ji maganar Ubangiji!
ויאמר אלי הנבא על העצמות האלה ואמרת אליהם--העצמות היבשות שמעו דבר יהוה
5 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce wa waɗannan ƙasusuwa. Zan sa numfashi ya shiga muku, za ku kuwa rayu.
כה אמר אדני יהוה לעצמות האלה הנה אני מביא בכם רוח--וחייתם
6 Zan harhaɗa muku jijiyoyi in sa muku tsoka in kuma rufe ku da fata; zan sa numfashi a cikinku, za ku kuwa rayu. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.’”
ונתתי עליכם גידים והעלתי עליכם בשר וקרמתי עליכם עור ונתתי בכם רוח וחייתם וידעתם כי אני יהוה
7 Saboda haka sai na yi annabci yadda aka umarce ni. Da nake annabcin, sai aka ji motsi, ƙarar girgiza, sai ƙasusuwan suka harhaɗu, ƙashi ya haɗu da ƙashi.
ונבאתי כאשר צויתי ויהי קול כהנבאי והנה רעש ותקרבו עצמות עצם אל עצמו
8 Na duba, sai ga jijiyoyi da nama suka bayyana a kansu fata kuma ta rufe su, amma ba numfashi a cikinsu.
וראיתי והנה עליהם גדים ובשר עלה ויקרם עליהם עור מלמעלה ורוח אין בהם
9 Sa’an nan ya ce mini, “Ka yi annabci wa numfashi; ka yi annabci, ɗan mutum, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ka fito daga kusurwoyi huɗu, ya numfashi, ka kuma numfasa cikin waɗannan matattu, don su rayu.’”
ויאמר אלי הנבא אל הרוח הנבא בן אדם ואמרת אל הרוח כה אמר אדני יהוה מארבע רוחות באי הרוח ופחי בהרוגים האלה ויחיו
10 Saboda haka na yi annabci yadda aka umarce ni, sai numfashi ya shiga musu; suka rayu suka kuma miƙe tsaye a ƙafafunsu babbar runduna ce ƙwarai.
והנבאתי כאשר צוני ותבוא בהם הרוח ויחיו ויעמדו על רגליהם--חיל גדול מאד מאד
11 Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa su ne dukan gidan Isra’ila. Suna cewa, ‘Ƙasusuwanmu sun bushe, sa zuciyarmu duk ya tafi; an share mu ƙaf.’
ויאמר אלי בן אדם העצמות האלה כל בית ישראל המה הנה אמרים יבשו עצמותינו ואבדה תקותנו--נגזרנו לנו
12 Saboda haka yi annabci ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ya mutanena, zan buɗe kaburburanku in fitar da ku daga cikinsu; zan mai da ku ƙasar Isra’ila.
לכן הנבא ואמרת אליהם כה אמר אדני יהוה הנה אני פתח את קברותיכם והעליתי אתכם מקברותיכם עמי והבאתי אתכם אל אדמת ישראל
13 Sa’an nan ku, mutanena, za ku san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na buɗe kaburburanku na fitar da ku daga cikinsu.
וידעתם כי אני יהוה בפתחי את קברותיכם ובהעלותי אתכם מקברותיכם--עמי
14 Zan sa Ruhuna a cikinku za ku kuwa rayu, zan kuma zaunar da ku a ƙasarku. Sa’an nan za ku san cewa Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata, in ji Ubangiji.’”
ונתתי רוחי בכם וחייתם והנחתי אתכם על אדמתכם וידעתם כי אני יהוה דברתי ועשיתי--נאם יהוה
15 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
ויהי דבר יהוה אלי לאמר
16 “Ɗan mutum, ka ɗauki sanda ka rubuta a kansa, ‘Na Yahuda da Isra’ilawan da suke tare da shi.’ Sa’an nan ka ɗauki wani sanda, ka rubuta a kansa, ‘Sandan Efraim, na Yusuf da dukan gidan Isra’ilan da suke tare da shi.’
ואתה בן אדם קח לך עץ אחד וכתב עליו ליהודה ולבני ישראל חברו ולקח עץ אחד וכתוב עליו ליוסף עץ אפרים וכל בית ישראל חברו
17 Ka haɗa su su zama sanda guda saboda su kasance ɗaya a hannunka.
וקרב אתם אחד אל אחד לך--לעץ אחד והיו לאחדים בידך
18 “In mutanen ƙasarka suka tambaye ka cewa, ‘Ba za ka faɗa mana abin da kake nufi da wannan ba?’
וכאשר יאמרו אליך בני עמך לאמר הלוא תגיד לנו מה אלה לך
19 Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, Zan ɗauki sandan Yusuf, wanda yake a hannun Efraim, da na kabilan Isra’ilawan da suke tare da shi, in haɗa shi da sandan Yahuda, in mai da su sanda guda, za su kuwa zama ɗaya a hannuna.’
דבר אלהם כה אמר אדני יהוה הנה אני לקח את עץ יוסף אשר ביד אפרים ושבטי ישראל חברו ונתתי אותם עליו את עץ יהודה ועשיתם לעץ אחד והיו אחד בידי
20 Ka riƙe sandunan da ka yi rubutun a gabansu
והיו העצים אשר תכתב עליהם בידך--לעיניהם
21 ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan fitar da Isra’ilawa daga al’ummai inda suka tafi. Zan tattara su daga dukan kewaye in komo da su ƙasarsu.
ודבר אליהם כה אמר אדני יהוה הנה אני לקח את בני ישראל מבין הגוים אשר הלכו שם וקבצתי אתם מסביב והבאתי אותם אל אדמתם
22 Zan mai da su al’umma ɗaya a cikin ƙasar, a kan duwatsun Isra’ila. Za a kasance da sarki guda a kan dukansu ba za su ƙara zama al’ummai biyu ko su rabu su zama masarautai biyu ba.
ועשיתי אתם לגוי אחד בארץ בהרי ישראל ומלך אחד יהיה לכלם למלך ולא יהיה (יהיו) עוד לשני גוים ולא יחצו עוד לשתי ממלכות עוד
23 Ba za su ƙara ƙazantar da kansu da gumaka da mugayen siffofi ko kuma da wani daga laifofinsu ba, gama zan cece su daga dukan zunubinsu na ridda, zan kuma tsarkake su. Za su zama mutanena, ni kuma zan zama Allahnsu.
ולא יטמאו עוד בגלוליהם ובשקוציהם ובכל פשעיהם והושעתי אתם מכל מושבתיהם אשר חטאו בהם וטהרתי אותם והיו לי לעם ואני אהיה להם לאלהים
24 “‘Bawana Dawuda zai zama sarki a kansu, dukansu kuwa za su kasance da makiyayi guda. Za su bi dokokina su kuma kiyaye ƙa’idodina.
ועבדי דוד מלך עליהם ורועה אחד יהיה לכלם ובמשפטי ילכו וחקותי ישמרו ועשו אותם
25 Za su zauna a ƙasar da na ba wa bawana Yaƙub, ƙasar da kakanninsu suka zauna. Su da’ya’yansu da’ya’ya’ya’yansu za su zauna a can har abada, kuma Dawuda bawana zai zama sarkinsu har abada.
וישבו על הארץ אשר נתתי לעבדי ליעקב אשר ישבו בה אבותיכם וישבו עליה המה ובניהם ובני בניהם עד עולם ודוד עבדי נשיא להם לעולם
26 Zan yi alkawarin salama da su; zai zama madawwamin alkawari. Zan kafa su in ƙara yawansu, zan kuma sa wuri mai tsarkina a cikinsu har abada.
וכרתי להם ברית שלום ברית עולם יהיה אותם ונתתים והרביתי אותם ונתתי את מקדשי בתוכם לעולם
27 Mazaunina zai kasance da su; zan kuwa zama Allahnsu, za su kuma zama mutanena.
והיה משכני עליהם והייתי להם לאלהים והמה יהיו לי לעם
28 Sa’an nan al’ummai za su san cewa Ni Ubangiji na mai da Isra’ila mai tsarki, sa’ad da wuri mai tsarkina yana a cikinsu har abada.’”
וידעו הגוים כי אני יהוה מקדש את ישראל--בהיות מקדשי בתוכם לעולם

< Ezekiyel 37 >