< Ezekiyel 35 >

1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
וַיְהִי דְבַר־יְהֹוָה אֵלַי לֵאמֹֽר׃
2 “Ɗan mutum, ka fuskanci Dutsen Seyir; ka yi annabci a kansa
בֶּן־אָדָם שִׂים פָּנֶיךָ עַל־הַר שֵׂעִיר וְהִנָּבֵא עָלָֽיו׃
3 ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, Dutsen Seyir, zan kuma miƙa hannuna gāba da kai in mai da kai kango.
וְאָמַרְתָּ לּוֹ כֹּה אָמַר אֲדֹנָי יֱהֹוִה הִנְנִי אֵלֶיךָ הַר־שֵׂעִיר וְנָטִיתִי יָדִי עָלֶיךָ וּנְתַתִּיךָ שְׁמָמָה וּמְשַׁמָּֽה׃
4 Zan mai da garuruwanka kufai za ka kuma zama kango. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.
עָרֶיךָ חׇרְבָּה אָשִׂים וְאַתָּה שְׁמָמָה תִֽהְיֶה וְיָדַעְתָּ כִּֽי־אֲנִי יְהֹוָֽה׃
5 “‘Domin ka riƙe ƙiyayya ta tun dā, ka kuma ba da mutanen Isra’ila domin a kashe su da takobi a lokacin masifarsu, lokacin da adadin horonsu ya cika,
יַעַן הֱיוֹת לְךָ אֵיבַת עוֹלָם וַתַּגֵּר אֶת־בְּנֵֽי־יִשְׂרָאֵל עַל־יְדֵי־חָרֶב בְּעֵת אֵידָם בְּעֵת עֲוֺן קֵֽץ׃
6 saboda haka muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan sa a zub da jininka zan kuwa fafare ka. Da yake ba ka ƙi zub da jini ba, zub da jini zai fafare ka.
לָכֵן חַי־אָנִי נְאֻם אֲדֹנָי יֱהֹוִה כִּֽי־לְדָם אֶעֶשְׂךָ וְדָם יִרְדְּפֶךָ אִם־לֹא דָם שָׂנֵאתָ וְדָם יִרְדְּפֶֽךָ׃
7 Zan mai da Dutsen Seyir kango in kuma yanke dukan waɗanda suke shiga da fita a cikinka.
וְנָֽתַתִּי אֶת־הַר שֵׂעִיר לְשִֽׁמְמָה וּשְׁמָמָה וְהִכְרַתִּי מִמֶּנּוּ עֹבֵר וָשָֽׁב׃
8 Zan cika duwatsunka da matattu; waɗanda aka kashe da takobi za su fāɗi a kan tuddanka, da cikin kwarurukanka, da cikin dukan kwazazzabanka.
וּמִלֵּאתִי אֶת־הָרָיו חֲלָלָיו גִּבְעוֹתֶיךָ וְגֵיאוֹתֶיךָ וְכׇל־אֲפִיקֶיךָ חַלְלֵי־חֶרֶב יִפְּלוּ בָהֶֽם׃
9 Zan mai da kai kango har abada; ba za a zauna a cikin garuruwanka ba. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.
שִֽׁמְמוֹת עוֹלָם אֶתֶּנְךָ וְעָרֶיךָ לֹא (תישבנה) [תָשֹׁבְנָה] וִידַעְתֶּם כִּֽי־אֲנִי יְהֹוָֽה׃
10 “‘Domin kun ce, “Waɗannan al’ummai biyu da ƙasashe za su zama namu za mu kuma mallake su,” ko da yake Ni Ubangiji ina a can,
יַעַן אֲמׇרְךָ אֶת־שְׁנֵי הַגּוֹיִם וְאֶת־שְׁתֵּי הָאֲרָצוֹת לִי תִהְיֶינָה וִֽירַשְׁנוּהָ וַיהֹוָה שָׁם הָיָֽה׃
11 saboda haka muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan sāka maka gwargwadon fushi da kuma kishin da ka nuna a ƙiyayyarsu da ka yi zan kuma sanar da kaina a cikinsu sa’ad da na hukunta ka.
לָכֵן חַי־אָנִי נְאֻם אֲדֹנָי יֱהֹוִה וְעָשִׂיתִי כְּאַפְּךָ וּכְקִנְאָתְךָ אֲשֶׁר עָשִׂיתָה מִשִּׂנְאָתֶיךָ בָּם וְנוֹדַעְתִּי בָם כַּאֲשֶׁר אֶשְׁפְּטֶֽךָ׃
12 Sa’an nan za ka san cewa Ni Ubangiji na ji duk abubuwan banzan da ka faɗa a kan duwatsun Isra’ila. Ka ce, “An mai da su kango an kuma ba mu su mu cinye.”
וְֽיָדַעְתָּ כִּי אֲנִי יְהֹוָה שָׁמַעְתִּי ׀ אֶת־כׇּל־נָאָֽצוֹתֶיךָ אֲשֶׁר אָמַרְתָּ עַל־הָרֵי יִשְׂרָאֵל לֵאמֹר ׀ [שָׁמֵמוּ] (שממה) לָנוּ נִתְּנוּ לְאׇכְלָֽה׃
13 Ka yi fariya a kaina, ka kuma yi magana a kaina ba gaggautawa, na ji shi sarai.
וַתַּגְדִּילוּ עָלַי בְּפִיכֶם וְהַעְתַּרְתֶּם עָלַי דִּבְרֵיכֶם אֲנִי שָׁמָֽעְתִּי׃
14 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa yayinda dukan duniya take farin ciki, zan mai da kai kango.
כֹּה אָמַר אֲדֹנָי יֱהֹוִה כִּשְׂמֹחַ כׇּל־הָאָרֶץ שְׁמָמָה אֶעֱשֶׂה־לָּֽךְ׃
15 Domin ka yi farin ciki sa’ad da gādon gidan Isra’ila ya zama kufai, haka zan yi da kai, ya Dutsen Seyir, kai da dukan Edom. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.’”
כְּשִׂמְחָתְךָ לְנַחֲלַת בֵּֽית־יִשְׂרָאֵל עַל אֲשֶׁר־שָׁמֵמָה כֵּן אֶעֱשֶׂה־לָּךְ שְׁמָמָה תִֽהְיֶה הַר־שֵׂעִיר וְכׇל־אֱדוֹם כֻּלָּהּ וְיָדְעוּ כִּי־אֲנִי יְהֹוָֽה׃

< Ezekiyel 35 >