< Ezekiyel 31 >
1 A shekara ta goma sha ɗaya, a wata na uku a rana ta farko, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
On the first day of the third month of the eleventh year, a message from the Lord came to me, saying,
2 “Ɗan mutum, faɗa wa Fir’auna sarkin Masar da jama’arsa cewa, “‘Da wa za a kwatanta girmanka?
“Son of man, tell Pharaoh king of Egypt and all his many people: Who is as great as you?
3 Ka dubi Assuriya, ta taɓa zama kamar al’ul a Lebanon da rassa masu kyau suna inuwartar da kurmi; ya yi tsayi ainun kansa ya kai cikin gizagizai.
Look at Assyria. It was like a cedar in Lebanon, with its beautiful branches providing shade in the forest. It was so high that its top reached the clouds.
4 Ruwa ya sa ya yi girma, zurfafan maɓulɓulai sun sa ya yi tsayi; rafuffuka suna gudu kewaye da tushensa yana aika da rafuffukansa zuwa dukan itatuwan kurmi.
Deep springs of water made it grow tall and sent streams all around it to water all the other trees.
5 Saboda haka ya yi tsayi fiye da sauran itatuwan kurmi; rassansa suka ƙaru suka yi tsayi, suka bazu saboda yalwar ruwaye.
It became really tall, higher than any other tree in the forest. Its branches grew thick and long because it was so well-watered.
6 Dukan tsuntsayen sararin sama suka yi sheƙa a rassansa, dukan namun jeji suka haihu a ƙarƙashin rassansa; dukan al’ummai suka zauna a inuwarsa.
All kinds of birds nested in its branches, while underneath it different wild animals had their young, and all the powerful nations lived in its shade.
7 Yana da girma a kyau, da dogayen rassansa da ya baza, gama saiwoyinsa sun nutse can ƙasa har cikin yalwar ruwaye.
It was beautiful and majestic with its long branches, because its roots reached down to the plentiful water.
8 Al’ul a cikin lambun Allah ba su kai shi ba, balle itatuwan kasharina su kai rassansa, ko itatuwan durumi su kai rassansa, ko itace a lambun Allah ya kai kyansa.
The cedars in God's garden were no match for it. No pine tree had such great branches, nor did any plane tree. No tree in God's garden was as beautiful.
9 Na sa ya yi kyau da yalwar rassa, abin ƙyashi na dukan itatuwan Eden a lambun Allah.
I made it beautiful with its many branches. All the trees of Eden in God's garden envied it.
10 “‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin ya yi tsayi, kansa kuma ya kai cikin gizagizai, kuma domin ya yi fariya saboda tsayinsa,
So this is what the Lord God says: Since it became so tall, reaching up into the clouds, it grew proud because of its height.
11 na miƙa shi ga mai mulkin al’ummai, don yă sāka masa gwargwadon muguntarsa. Na jefar da shi a gefe,
So I handed it over to the leader of a foreign nation who will punish it for its wickedness. I have thrown it out.
12 kuma baƙi mafi mugunta na al’ummai suka sare shi suka bar shi. Rassansa sun fāɗi a kan duwatsun da suke cikin dukan kwaruruka; rassansa kuma sun kakkarye, sun fāɗi a cikin dukan magudanan ruwa na ƙasa. Dukan al’umman duniya suka fito daga ƙarƙashin inuwarsa suka bar shi.
Foreigners from the cruelest of all the nations chopped it down and left it lying there. Its branches lie fallen and broken in the mountains and valleys of the countryside. Everybody in earth came out of its shadow and abandoned it.
13 Dukan tsuntsaye sararin sama suka zauna a itacen da ya fāɗi, dukan namun jeji kuma suna cikin rassansa.
Birds came to live on its fallen trunk, and wild animals hid among its fallen branches.
14 Saboda haka ba wani daga cikin itatuwan da suke kusa da ruwan da zai taɓa yin fariyar tsawonsa, har kawunansu su kai cikin gizagizai. Ba wani daga cikin itatuwan da ya sha ruwa sosai da zai taɓa yi wannan tsayi; duk an bashe su ga mutuwa, zuwa can ƙasa, a cikin matattu, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.
This was in order that no other trees growing by the water would grow up so high and have their tops reach the clouds. This was so that no other trees, however much water they had, would be as tall as them, For they all will die and go down into earth, just like human beings who go down into the grave.
15 “‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da aka yi ƙasa da shi zuwa kabari na rufe zurfafa maɓulɓulai da makoki dominsa; na janye rafuffukansa, aka kuma hana yalwan ruwansa. Saboda shi na rufe Lebanon da baƙin ciki, dukan itatuwan kurmi suka bushe. (Sheol )
This is what the Lord God says: On the day it was brought down to Sheol, I had the deep waters mourn for it; I stopped its rivers flowing; I held back all its waters. I covered Lebanon in darkness, and all the trees in the forest withered. (Sheol )
16 Na sa al’ummai suka yi rawar jiki da jin ƙarar fāɗuwarsa sa’ad da na yi ƙasa da shi zuwa kabari tare da waɗanda suka gangara rami. Sai dukan itatuwan Eden, zaɓaɓɓu da kuma mafi kyau na Lebanon, dukan itatuwan da aka yi musu banruwa, sun ta’azantu a ƙarƙashin ƙasa. (Sheol )
I made the nations tremble when they heard it fall, when I threw it down into Sheol with those who die. Then all the trees of Eden, the finest and best in Lebanon, all the trees that had plenty of water, were happy that this tree joined them in the earth below. (Sheol )
17 Waɗanda suka zauna a inuwarsa, dukan masu tarayyarsa a cikin al’ummai, su ma sun gangara zuwa kabari tare da shi, sun haɗu da waɗanda aka kashe da takobi. (Sheol )
They also went down with it into Sheol, to those who had been killed by the sword. They had been part of its army living in its shade among the nations. (Sheol )
18 “‘Da wa cikin itatuwan Eden za a kwatanta da kai cikin girma da daraja? Duk da haka kai ma, za a yi ƙasa da kai tare da itatuwan Eden zuwa ƙarƙashin ƙasa; za ka kwanta a cikin marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi. “‘Fir’auna ke nan da dukan jama’arsa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’”
Who is as great and glorious as you among the trees of Eden? But you too will be brought down to the earth below to be with the trees of Eden. You will lie there with the heathen, with those killed by the sword. This is what will happen to Pharaoh and all his many people, declares the Lord God.”