< Ezekiyel 29 >
1 A shekara ta goma, a wata na goma, a rana ta goma sha biyu, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2 “Ɗan mutum, ka fuskanci Fir’auna sarkin Masar ka kuma yi annabci gāba da shi da dukan Masar.
3 Yi masa magana ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “‘Ina gāba da kai, Fir’auna sarkin Masar, kai babban mugun dodon ruwa kwance cikin rafuffukanka. Ka ce, “Nilu nawa ne; na yi shi wa kaina.”
4 Amma zan sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka in sa kifin rafuffukanka su manne wa kamɓorinka. Zan jawo ka daga cikin tsakiyar rafuffukanka, da dukan kifayen rafuffukanka, waɗanda suka manne a ƙamborinka,
5 Zan bar ka a cikin hamada, kai da dukan kifin rafuffukanka. Za ka fāɗi a fili ba kuwa za a tattara ka ko a kwashe ba. Zan ba da kai kamar abinci ga namun jeji na duniya da tsuntsayen sararin sama.
6 Ta haka dukan waɗanda suke zama a Masar za su san cewa ni ne Ubangiji. “‘Ka zama sandan iwa domin gidan Isra’ila.
7 Sa’ad da suka kama ka da hannuwansu, ka tsattsage, ka kuma buɗu a kafaɗunsu; sa’ad da suka jingina a kanka, sai ka karye, bayansu kuwa ya firgita.
8 “‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan kawo takobi a kanka in kashe mutane da dabbobi.
9 Masar za tă zama kufai. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji. “‘Domin ka ce, “Nilu nawa ne; ni na yi shi,”
10 saboda haka ina gāba da kai da rafuffukanka, zan kuma maishe ƙasar Masar ta lalace ta kuma zama kango daga Migdol zuwa Aswan, har iyakar Kush.
11 Ba ƙafar mutum ko ta dabbar da za tă ratsa ta; ba wanda zai zauna a can har shekaru arba’in.
12 Zan mai da ƙasar Masar kufai a cikin ƙasashen da aka ragargaza, biranenta kuma za su zama kango har shekaru arba’in a cikin biranen da aka lalace. Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe.
13 “‘Duk da haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ƙarshen shekaru arba’in ɗin zan tattara Masarawa daga al’ummai inda aka warwatsa su.
14 Zan komo da su daga zaman bauta in mai da su zuwa Masar ta Bisa, ƙasarsu ta ainihi. A can za su zama masarauta marar ƙarfi.
15 Za tă zama masarauta mafi rarrauna cikin masarautai, ba kuwa za tă ƙara ɗaga kanta a kan sauran al’ummai ba. Zan sa tă zama marar ƙarfi ƙwarai, har da ba za tă ƙara yin mulkin a kan al’ummai ba.
16 Masar ba za tă ƙara zama abin dogara ga mutanen Isra’ila ba amma za tă zama abin tunin zunubinsu na juyawa gare ta don taimako. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.’”
17 A shekara ta ashirin da bakwai, a wata na fari a rana ta farko, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
18 “Ɗan mutum, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya sa sojojinsa su matsa wa Taya; kowane kai ya koɗe, kowace kafaɗa kuma ta goge. Duk da haka shi da sojojinsa ba su sami wani lada daga matsin da suka yi a kan Taya ba.
19 Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan ba da Masar ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, zai washe dukiyarta. Zai kwashe ya washe ƙasar ganima a matsayin abin biyan sojojinsa.
20 Saboda haka na ba shi Masar a matsayin lada don ƙoƙarinsa domin shi da sojojinsa sun yi wannan domina ne, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
21 “A wannan rana zan sa ƙaho ya tsiro wa gidan Isra’ila, zan kuma buɗe bakinka a cikinsu. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”