< Ezekiyel 28 >

1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
ויהי דבר יהוה אלי לאמר
2 “Ɗan mutum, ka faɗa wa mai mulkin Taya cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “‘Cikin alfarmar zuciyarka ka ce, “Ni allah ne; ina zama a kan kursiyin allah a tsakiyar tekuna.” Amma kai mutum ne ba allah ba, ko da yake ka ɗauka kana da hikima kamar allah.
בן אדם אמר לנגיד צר כה אמר אדני יהוה יען גבה לבך ותאמר אל אני--מושב אלהים ישבתי בלב ימים ואתה אדם ולא אל ותתן לבך כלב אלהים
3 Ka fi Daniyel hikima ne? Ba asirin da yake ɓoye a gare ka?
הנה חכם אתה מדנאל (מדניאל) כל סתום לא עממוך
4 Ta wurin hikimarka da ganewarka ka sami dukiya wa kanka ka kuma tara zinariya da azurfa cikin wuraren ajiyarka.
בחכמתך ובתבונתך עשית לך חיל ותעש זהב וכסף באוצרותיך
5 Ta wurin dabararka mai girma cikin kasuwanci ka ƙara dukiyarka, kuma saboda dukiyarka zuciyarka ta cika da alfarma.
ברב חכמתך ברכלתך הרבית חילך ויגבה לבבך בחילך
6 “‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “‘Domin ka ɗauka kai mai hikima ne, mai hikima kamar allah,
לכן כה אמר אדני יהוה יען תתך את לבבך כלב אלהים
7 zan kawo baƙi a kanka, waɗanda suka fi mugunta cikin sauran al’ummai; za su zāre takubansu a kan kyakkyawar hikimarka su kuma ɓarke darajarka mai walƙiya.
לכן הנני מביא עליך זרים--עריצי גוים והריקו חרבותם על יפי חכמתך וחללו יפעתך
8 Za su jefar da kai cikin rami, za ka kuwa yi muguwar mutuwa a tsakiyar tekuna.
לשחת יורדוך ומתה ממותי חלל בלב ימים
9 Za ka iya ce yanzu, “Ni allah ne,” a gaban waɗanda suka kashe ka? Za ka zama mutum kurum, ba allah ba, a hannuwan waɗanda suka kashe ka.
האמר תאמר אלהים אני לפני הרגך ואתה אדם ולא אל ביד מחלליך
10 Za ka yi mutuwar marar kaciya a hannuwan baƙi. Na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’”
מותי ערלים תמות ביד זרים כי אני דברתי נאם אדני יהוה
11 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
ויהי דבר יהוה אלי לאמר
12 “Ɗan mutum, ka yi makoki domin sarkin Taya ka kuma ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “‘Ka kasance hatimin cikakke, cike da hikima da cikakke a kyau.
בן אדם שא קינה על מלך צור ואמרת לו כה אמר אדני יהוה אתה חותם תכנית מלא חכמה וכליל יפי
13 Ka kasance a Eden, a lambun Allah; aka yi maka ado da kowane dutse mai daraja, yakutu, tofaz, da zumurrudu, kirisolit, onis da yasfa, saffaya, turkuwoyis da beril. Tsare-tsare da shirye-shiryenka an yi su da zinariya ne; a ranar da aka halicce ka an shirya su.
בעדן גן אלהים היית כל אבן יקרה מסכתך אדם פטדה ויהלם תרשיש שהם וישפה ספיר נפך וברקת וזהב מלאכת תפיך ונקביך בך ביום הבראך כוננו
14 An shafe ka kamar kerub mai tsaro, gama haka na naɗa ka. Kana a tsattsarkan dutsen Allah; ka yi tafiya a tsakiyar duwatsun wuta.
את כרוב--ממשח הסוכך ונתתיך בהר קדש אלהים היית--בתוך אבני אש התהלכת
15 Ka kasance marar laifi cikin dukan hanyoyinka daga ranar da aka halicce ka sai da aka sami mugunta a cikinka.
תמים אתה בדרכיך מיום הבראך עד נמצא עולתה בך
16 Ta wurin yawan kasuwancinka ka cika da rikici, ka kuma yi zunubi. Saboda haka na kore ka da kunya daga dutsen Allah, na kore ka, ya kerub mai tsaro, daga cikin duwatsun wuta.
ברב רכלתך מלו תוכך חמס--ותחטא ואחללך מהר אלהים ואבדך כרוב הסכך מתוך אבני אש
17 Zuciyarka ta cika da alfarma saboda kyanka, ka kuma lalace hikimarka saboda darajarka. Saboda haka na jefar da kai zuwa ƙasa; na sa ka zama abin kallo a gaban sarakuna.
גבה לבך ביפיך שחת חכמתך על יפעתך על ארץ השלכתיך לפני מלכים נתתיך--לראוה בך
18 Ta wurin yawan zunubanka da kasuwancinka na cuta ka ƙazantar da wuri mai tsarkinka. Saboda haka na sa wuta ta fito daga cikinka, ta cinye ka, na maishe ka toka a bisa ƙasa a kan idon dukan waɗanda suke kallonka.
מרב עוניך בעול רכלתך חללת מקדשיך ואוצא אש מתוכך היא אכלתך ואתנך לאפר על הארץ לעיני כל ראיך
19 Dukan al’umman da suka san ka sun giggice saboda masifar da ta auko maka; ka zo ga mummunar ƙarshe ba za ka ƙara kasancewa ba har abada.’”
כל יודעיך בעמים שממו עליך בלהות היית ואינך עד עולם
20 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
ויהי דבר יהוה אלי לאמר
21 “Ɗan mutum, ka fuskanci Sidon; ka yi annabci a kanta
בן אדם שים פניך אל צידון והנבא עליה
22 ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “‘Ina gāba da ke, ya Sidon, zan sami ɗaukaka a cikinki. Za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na zartar da hukunci a kanta na kuma nuna kaina mai tsarki a cikinta.
ואמרת כה אמר אדני יהוה הנני עליך צידון ונכבדתי בתוכך וידעו כי אני יהוה בעשותי בה שפטים--ונקדשתי בה
23 Zan aika da annoba a kanta in kuma sa jini ya zuba a titunanta. Kisassu za su fāɗi a cikinta, da takobi yana gāba da ita a kowane gefe. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.
ושלחתי בה דבר ודם בחוצותיה ונפלל חלל בתוכה בחרב עליה מסביב וידעו כי אני יהוה
24 “‘Mutanen Isra’ila ba za su ƙara kasance da mugayen maƙwabta waɗanda za su zama sarƙaƙƙiya masu zafi da ƙaya mai tsini ba. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.
ולא יהיה עוד לבית ישראל סלון ממאיר וקוץ מכאב מכל סביבתם השאטים אותם וידעו כי אני אדני יהוה
25 “‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa sa’ad da na tattara mutanen Isra’ila daga al’ummai inda suke a warwatse, zan nuna kaina mai tsarki a cikinsu a idon al’ummai. Sa’an nan za su zauna a ƙasarsu, wadda na ba wa bawana Yaƙub.
כה אמר אדני יהוה בקבצי את בית ישראל מן העמים אשר נפצו בם ונקדשתי בם לעיני הגוים וישבו על אדמתם אשר נתתי לעבדי ליעקב
26 Za su zauna a can lafiya su kuma gina gidaje su nome gonakin inabi; za su zauna lafiya sa’ad da zan zartar da hukunci a kan dukan maƙwabtansu da suka wulaƙanta su. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu.’”
וישבו עליה לבטח ובנו בתים ונטעו כרמים וישבו לבטח בעשותי שפטים בכל השאטים אתם מסביבותם--וידעו כי אני יהוה אלהיהם

< Ezekiyel 28 >