< Ezekiyel 27 >

1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
ויהי דבר יהוה אלי לאמר
2 “Ɗan mutum, ka yi makoki domin Taya.
ואתה בן אדם שא על צר קינה
3 Ka ce wa Taya, wadda take zaune a hanyar shiga zuwa teku, kasuwar masu yawa mutane a bakin teku, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “‘Kin ce, ya Taya, “Ni kyakkyawa ce cikakkiya.”
ואמרת לצור הישבתי (הישבת) על מבואת ים רכלת העמים אל איים רבים כה אמר אדני יהוה צור את אמרת אני כלילת יפי
4 Manyan tekuna ne wurin zamanki; maginanki sun sa kyanki ya zama cikakke.
בלב ימים גבוליך בניך כללו יפיך
5 Sun yi dukan katakanki daga itatuwan fir daga Senir; sun kwaso itatuwan al’ul daga Lebanon don su yi miki jigon jirgin ruwa.
ברושים משניר בנו לך את כל לחתים ארז מלבנון לקחו לעשות תרן עליך
6 Da oak daga Bashan suka yi sandunan tuƙan jirgin ruwa da itatuwan kasharina daga bakin tekun Saifurus suka yi daɓe jirgin ruwanki, suka kuma manne masa hauren giwa.
אלונים מבשן עשו משוטיך קרשך עשו שן בת אשרים מאיי כתים
7 Lilin mai kyau mai ado daga Masar ne filafilan jirgin ruwanki suka kuma zama tutarki; an yi tutarki da shuɗi da shunayya daga bakin tekun Elisha.
שש ברקמה ממצרים היה מפרשך להיות לך לנס תכלת וארגמן מאיי אלישה היה מכסך
8 Mutanen Sidon da Arfad su ne matuƙan jirgin ruwanki; gwanayenki, ya Taya, suna ciki a matsayi matuƙan jiragen ruwa.
ישבי צידון וארוד היו שטים לך חכמיך צור היו בך המה חבליך
9 Masu hikima na Gebal suna ciki a matsayin masu tattoshe mahaɗan katakon jirginki. Dukan jiragen ruwa da matuƙansu sukan zo wurinki don kasuwanci.
זקני גבל וחכמיה היו בך מחזיקי בדקך כל אניות הים ומלחיהם היו בך לערב מערבך
10 “‘Mutanen Farisa, Lidiya da Fut su ne suka zama sojoji a cikin mayaƙanki. Sun rataye garkuwoyinsu da hulunan kwano a katangarki, suna kawo miki daraja.
פרס ולוד ופוט היו בחילך אנשי מלחמתך מגן וכובע תלו בך המה נתנו הדרך
11 Mutanen Arfad da Helek sun yi tsaron katangar a kowace gefe; mutanen Gammad su ne a hasumiyoyinki. Sun rataye garkuwoyinsu kewaye da katangarki; sun sa kyanki ya zama cikakke.
בני ארוד וחילך על חומותיך סביב וגמדים במגדלותיך היו שלטיהם תלו על חומותיך סביב--המה כללו יפיך
12 “‘Tarshish ta yi ciniki da ke saboda yawan wadatar kayayyakinki; sun sayi kayan cinikinki da azurfa, ƙarfe, kuza da dalma.
תרשיש סחרתך מרב כל הון בכסף ברזל בדיל ועופרת נתנו עזבוניך
13 “‘Girka, Tubal da Meshek sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki suka biya da bayi da kuma abubuwan da aka yi da tagulla.
יון תבל ומשך המה רכליך בנפש אדם וכלי נחשת נתנו מערבך
14 “‘Mutanen Bet Togarma sun sayi kayan cinikinki da dawakai, dawakan yaƙi da alfadarai.
מבית תוגרמה סוסים ופרשים ופרדים נתנו עזבוניך
15 “‘Mutanen Dedan sun yi kasuwanci da ke, bakin teku masu yawa abokan cinikinki ne; sun biya ki da hauren giwa da katakon kanya.
בני דדן רכליך איים רבים סחרת ידך קרנות שן והובנים (והבנים) השיבו אשכרך
16 “‘Mutanen Aram sun yi ciniki da ke saboda yawan kayanki; suka sayi kayan cinikinki da zumurrudu, da shunayya, da kayan ado, da lilin mai taushi, da murjani, da yakutu.
ארם סחרתך מרב מעשיך בנפך ארגמן ורקמה ובוץ וראמת וכדכד נתנו בעזבוניך
17 “‘Yahuda da Isra’ila sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki da alkama da Minnit da alawa, da zuma, da mai, da ganyaye masu ƙanshi.
יהודה וארץ ישראל המה רכליך בחטי מנית ופנג ודבש ושמן וצרי נתנו מערבך
18 “‘Mutanen Damaskus sun ga abin da za ki iya bayarwa sai suka yi ciniki da ke, ta sayi kayanki da ruwan inabi daga Helbon, da ulu daga Zahar.
דמשק סחרתך ברב מעשיך מרב כל הון ביין חלבון וצמר צחר
19 Wedan da Yaban kusa da Uzal, suka sayi kayanki; wato gyararren ƙarfe da kayan yaji.
ודן ויון מאוזל בעזבוניך נתנו ברזל עשות קדה וקנה במערבך היה
20 “‘Mutanen Dedan sun sayi kayanki da sirdin zama a kan dawakai.
דדן רכלתך בבגדי חפש לרכבה
21 “‘Mutanen Arabiya da dukan sarakunan Kedar abokan cinikinki ne; sun yi ciniki da ke suka sayi kayanki da’yan raguna, da raguna, da awaki.
ערב וכל נשיאי קדר המה סחרי ידך בכרים ואילם ועתודים בם סחריך
22 “‘’Yan kasuwan Sheba da Ra’ama sun yi ciniki da ke; suka sayi kayanki da kayan yaji mafi kyau iri-iri, da duwatsu masu daraja iri-iri, da zinariya.
רכלי שבא ורעמה המה רכליך בראש כל בשם ובכל אבן יקרה וזהב נתנו עזבוניך
23 “‘Haran, Kanne da Eden da kuma’yan kasuwan Sheba, Assuriya da Kilmad sun yi ciniki da ke.
חרן וכנה ועדן רכלי שבא אשור כלמד רכלתך
24 A kasuwarki sun yi ciniki da ke suka sayar miki tufafi masu tsada, da na shuɗi, da masu ado, da dardumai masu ƙyalƙyali da kirtani, da igiyoyi waɗanda aka tuƙa da kyau.
המה רכליך במכללים בגלומי תכלת ורקמה ובגנזי ברמים בחבלים חבשים וארזים במרכלתך
25 “‘Jiragen ruwan Tarshish sun zama masu jigilar kayanki. Kin cika da kaya masu nauyi a tsakiyar teku.
אניות תרשיש שרותיך מערבך ותמלאי ותכבדי מאד בלב ימים
26 Matuƙan jiragenki sun kai ki can cikin manyan tekuna. Amma iskar gabas za tă farfasa ki kucu-kucu a tsakiyar teku.
במים רבים הבאוך השטים אתך רוח הקדים שברך בלב ימים
27 Dukiyarki, cinikinki da kayan kasuwarki, ma’aikatanki na jirgi, matuƙan jiragenki da masu tattoshe mahaɗan katakan jiragenki,’yan kasuwarki da dukan sojojinki, da kuma kowa da yake cikin jirgi zai nutsa a tsakiyar teku a ranar da jirginki zai nutse.
הונך ועזבוניך מערבך מלחיך וחבליך מחזיקי בדקך וערבי מערבך וכל אנשי מלחמתך אשר בך ובכל קהלך אשר בתוכך יפלו בלב ימים ביום מפלתך
28 Ƙasashen bakin teku za su girgiza sa’ad da matuƙan jirginki suka yi kuka.
לקול זעקת חבליך ירעשו מגרשות
29 Dukan waɗanda suke riƙe da matuƙi za su ƙyale jiragensu; ma’aikatan jirage da dukan matuƙan jirage za su tsaya a bakin teku.
וירדו מאניותיהם כל תפשי משוט--מלחים כל חבלי הים אל הארץ יעמדו
30 Za su tā da muryarsu su yi kuka mai zafi a kanki; za su yayyafa ƙura a kawunansu, su yi ta birgima a cikin toka.
והשמיעו עליך בקולם ויזעקו מרה ויעלו עפר על ראשיהם באפר יתפלשו
31 Za su aske kawunansu saboda ke za su kuma sa tufafin makoki. Za su yi kuka dominki su yi ɓacin rai da kuma kuka mai zafi.
והקריחו אליך קרחה וחגרו שקים ובכו אליך במר נפש מספד מר
32 Yayinda suke kuka a kanki kuwa, za su yi makoki dominki suna cewa, “Wa ya taɓa yin shiru kamar Taya, kewaye da teku?”
ונשאו אליך בניהם קינה וקוננו עליך מי כצור כדמה בתוך הים
33 Sa’ad da kayan cinikinki suka tafi ƙasashen hayi, kin gamsar da al’ummai masu yawa; da dukiyarki masu yawa da kuma kayan cinikinki kin azurtar da sarakunan duniya.
בצאת עזבוניך מימים השבעת עמים רבים ברב הוניך ומערביך העשרת מלכי ארץ
34 Yanzu teku ta farfashe ki cikin zurfafan ruwaye; kayan cinikinki da dukan kamfaninki sun nutse tare da ke.
עת נשברת מימים במעמקי מים מערבך וכל קהלך בתוכך נפלו
35 Dukan mazaunan bakin teku sun giggice saboda masifarki; sarakunansu sun tsorata ƙwarai fuskokinsu kuwa sun yamutse don tsoro.
כל ישבי האיים שממו עליך ומלכיהם שערו שער רעמו פנים
36 ’Yan kasuwa a cikin al’ummai suna yin miki tsaki; kin zo ga mummunar ƙarshe ba za ki ƙara kasancewa ba har abada.’”
סחרים בעמים שרקו עליך בלהות היית ואינך עד עולם

< Ezekiyel 27 >