< Ezekiyel 24 >
1 A shekara ta tara, a wata na goma, a rana ta goma, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
In the ninth year, on the tenth day of the tenth month, the word of the LORD came to me, saying,
2 “Ɗan mutum, ka rubuta wannan rana, wannan rana, domin sarkin Babilon ya yi ƙawanya wa Urushalima a wannan rana.
“Son of man, write down today’s date, for on this very day the king of Babylon has laid siege to Jerusalem.
3 Ka faɗa wa wannan gidan’yan tawaye wani misali ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “‘Ka sa tukunyar dahuwa; ka sa ta a kan wuta ka kuma zuba ruwa a cikinta.
Now speak a parable to this rebellious house and tell them that this is what the Lord GOD says: ‘Put the pot on the fire; put it on and pour in the water.
4 Ka sa gunduwoyin nama a cikinta dukan gunduwoyi masu kyau, cinya da kafaɗa. Ka cika ta da waɗannan ƙasusuwa mafi kyau;
Put in the pieces of meat, every good piece— thigh and shoulder— fill it with choice bones.
5 ka kama mafi kyau daga cikin garken. Ka tara itace a ƙarƙashinta saboda ƙasusuwan; ka sa ta tafasa ka kuma dafa ƙasusuwan a cikinta.
Take the choicest of the flock and pile the fuel beneath it. Bring it to a boil and cook the bones in it.’
6 “‘Gama wannan shi ne abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “‘Kaito birnin nan mai zubar da jini, ga tukunya wadda take da tsatsa, wadda tsatsarta ba za tă fita ba! Ka fitar da shi gunduwa-gunduwa ba tare da jefa ƙuri’a a kansu ba.
Therefore this is what the Lord GOD says: ‘Woe to the city of bloodshed, to the pot now rusted, whose rust will not come off! Empty it piece by piece; cast no lots for its contents.
7 “‘Gama zubar da jini yana a tsakiyarta, ta zubar da shi a dutsen da yake a fili; ba tă zubar da shi a ƙasa ba, inda ƙura za tă rufe shi.
For the blood she shed is still within her; she poured it out on the bare rock; she did not pour it on the ground to cover it with dust.
8 Don a zuga hasala a kuma yi sakayya na sa jininta a dutsen da ba a rufe ba, saboda kada a rufe.
In order to stir up wrath and take vengeance, I have placed her blood on the bare rock, so that it would not be covered.’
9 “‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “‘Kaito birnin nan mai zubar da jini! Ni ma zan jibge itace da yawa.
Yes, this is what the Lord GOD says: ‘Woe to the city of bloodshed! I, too, will pile the kindling high.
10 Ka tula gumagumai ka kuma ƙuna wuta. Ka dafa naman da kyau, kana haɗawa da yaji; ka kuma bar ƙasusuwan su ƙone.
Pile on the logs and kindle the fire; cook the meat well and mix in the spices; let the bones be burned.
11 Sa’an nan ka sa tukunyan nan da babu kome a kan garwashi sai ta yi zafi har darmarta ta yi ja wur domin dattinta ya narke tsatsarta kuma ta ƙone.
Set the empty pot on its coals until it becomes hot and its copper glows. Then its impurity will melt within; its rust will be consumed.
12 Ta gajiyar da dukan ƙoƙari; ba a fid da tsatsarta nan mai yawa ba, kai, ko a wuta ma.
It has frustrated every effort; its thick rust has not been removed, even by the fire.
13 “‘Yanzu ƙazantarki ita ce lalaci. Domin na yi ƙoƙari in tsabtacce ke amma ba ki tsabtattu daga ƙazantarki ba, ba za ki ƙara yin tsabta ba sai hasalata a kanki ya kwanta.
Because of the indecency of your uncleanness I tried to cleanse you, but you would not be purified from your filthiness. You will not be pure again until My wrath against you has subsided.
14 “‘Ni Ubangiji na faɗa. Lokaci ya zo da zan aikata. Ba zan janye ba; ba zan ji tausayi ba, ba kuwa zan bari ba. Za a hukunta ki bisa ga hali da ayyukanki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’”
I, the LORD, have spoken; the time is coming, and I will act. I will not refrain or show pity, nor will I relent. I will judge you according to your ways and deeds,’
15 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
Then the word of the LORD came to me, saying,
16 “Ɗan mutum, da farat ɗaya ina gab da ɗauke abin da idanunka suke jin daɗin gani. Duk da haka kada ka yi makoki ko ka yi kuka ko ka zub da hawaye.
“Son of man, behold, I am about to take away the desire of your eyes with a fatal blow. But you must not mourn or weep or let your tears flow.
17 Ka yi nishi shiru; kada ka yi makoki saboda matacciyar. Ka naɗa rawaninka ka kuma sa takalmanka a ƙafa; kada ka rufe sashen fuskarka daga ƙasa ko ka ci abincin da masu kuka sukan ci.”
Groan quietly; do not mourn for the dead. Put on your turban and strap your sandals on your feet; do not cover your lips or eat the bread of mourners.”
18 Da gari ya waye, sai na yi magana da mutane, da yamma kuwa matata ta rasu. Kashegari na yi yadda aka umarce ni.
So I spoke to the people in the morning, and in the evening my wife died. And the next morning I did as I had been commanded.
19 Sai mutane suka tambaye ni suka ce, “Ba za ka faɗa mana abin da waɗannan abubuwa suke nufi a gare mu ba?”
Then the people asked me, “Won’t you tell us what these things you are doing mean to us?”
20 Sai na ce musu, “Maganar Ubangiji ta zo mini cewa
So I answered them, “The word of the LORD came to me, saying:
21 faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da ƙazantar da wuri mai tsarkina, kagarar da kuke taƙama, abin da idanunku suke jin daɗin gani, abin faranta zuciyarku.’Ya’yanku maza da mata waɗanda kun bari a baya za su mutu ta wurin takobi.
Tell the house of Israel that this is what the Lord GOD says: ‘I am about to desecrate My sanctuary, the pride of your power, the desire of your eyes, and the delight of your soul. And the sons and daughters you left behind will fall by the sword.’
22 Za ku kuma yi yadda na yi. Ba za ku rufe sashe ƙasa na fuskarku ko ku ci abinci da masu kuka sukan ci ba.
Then you will do as I have done: You will not cover your lips or eat the bread of mourners.
23 Za ku naɗa rawunanku a kai ku sa takalmanku a ƙafafunku. Ba za ku yi kuka ko makoki ba amma za ku lalace saboda zunubanku ku kuma yi ta yin nishi.
Your turbans will remain on your heads and your sandals on your feet. You will not mourn or weep, but you will waste away because of your sins, and you will groan among yourselves.
24 Ezekiyel zai zama alama gare ku; za ku yi daidai yadda ya yi. Sa’ad da wannan ya faru, za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.’
‘Thus Ezekiel will be a sign for you; you will do everything that he has done. When this happens, you will know that I am the Lord GOD.’
25 “Kai kuma ɗan mutum, a ranar da zan ɗauke musu kagararsu, farin cikinsu da darajarsu, abin da idanunsu ke jin daɗin gani, abin da yake faranta musu zuciya, da kuka’ya’yansu maza da mata,
And you, son of man, know that on the day I take away their stronghold, their pride and joy—the desire of their eyes which uplifted their souls—and their sons and daughters as well,
26 a ranan nan wanda ya tsere zai zo don yă ba ka labari.
on that day a fugitive will come and tell you the news.
27 A lokacin bakinka zai buɗe, za ka yi magana da shi ba kuwa za ka ƙara yin shiru ba. Ta haka za ka zama alama gare su, za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.”
On that day your mouth will be opened to him who has escaped; you will speak and no longer be mute. So you will be a sign to them, and they will know that I am the LORD.”