< Ezekiyel 22 >
1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
耶和华的话又临到我说:
2 “Ɗan mutum, za ka shari’anta ta? Za ka shari’anta wannan birni mai kisankai? To, sai ka kalubalance ta da dukan ayyukanta na banƙyama
“人子啊,你要审问审问这流人血的城吗?当使她知道她一切可憎的事。
3 ka kuma ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce ya birnin da take kawo wa kansa hallaka ta wurin kisankai a cikinta kina kuma ƙazantar da kanki ta wurin yin gumaka,
你要说,主耶和华如此说:哎!这城有流人血的事在其中,叫她受报的日期来到,又做偶像玷污自己,陷害自己。
4 kin zama mai laifi saboda jinin da kika zubar kika kuma zama ƙazantacciya ta wurin gumakan da kika yi. Kin kawo kwanakinki ga ƙarshe, kuma ƙarshen shekarunki sun zo. Saboda haka zan mai da ke abar ba’a ga al’ummai da abin dariya ga dukan ƙasashe.
你因流了人的血,就为有罪;你做了偶像,就玷污自己,使你受报之日临近,报应之年来到。所以我叫你受列国的凌辱和列邦的讥诮。
5 Waɗanda suke kusa da waɗanda suke nesa za su yi miki ba’a, ya ke birni marar kunya, cike da rigima.
你这名臭、多乱的城啊,那些离你近、离你远的都必讥诮你。
6 “‘Duba yadda kowane yerima Isra’ila waɗanda suke cikinki yake yin amfani da ikonsa yana kisankai.
“看哪,以色列的首领各逞其能,在你中间流人之血。
7 A cikinki sun rena mahaifi da mahaifiya; a cikinki sun zalunci baƙo suka wulaƙanta maraya da gwauruwa.
在你中间有轻慢父母的,有欺压寄居的,有亏负孤儿寡妇的。
8 Kin rena abubuwana masu tsarki kika kuma ƙazantar da Asabbataina.
你藐视了我的圣物,干犯了我的安息日。
9 A cikinki akwai mutane waɗanda suka nace su yi kisankai; a cikinki akwai waɗanda suke ci a dutsen tsafi suna yin ayyukan lalata.
在你中间有谗谤人、流人血的;有在山上吃过祭偶像之物的,有行淫乱的。
10 A cikinki akwai waɗanda suke kwana da matan mahaifansu; a cikinki akwai waɗanda suke kwana da mata a lokacin da suke al’adarsu, sa’ad da suke da rashin tsarki.
在你中间有露继母下体羞辱父亲的,有玷辱月经不洁净之妇人的。
11 A cikinki mutum guda yakan yi laifi abin ƙyama da matar maƙwabcinsa, wani cikin rashin kunya ya ƙazantar da matar ɗansa, wani kuma ya kwana da’yar’uwansa,’yar mahaifinsa.
这人与邻舍的妻行可憎的事;那人贪淫玷污儿妇;还有玷辱同父之姊妹的。
12 A cikinki mutane suna karɓan cin hanci don su yi kisankai; kina ba da rance da ruwa da ƙari, kina kuma cin riba a kan maƙwabcinki ta wurin ƙwace. Kina kuma manta da ni, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
在你中间有为流人血受贿赂的;有向借钱的弟兄取利,向借粮的弟兄多要的。且因贪得无厌,欺压邻舍夺取财物,竟忘了我。这是主耶和华说的。
13 “‘Tabbatacce zan tafa hannuwana a kan ƙazamar riba da kika ci da jinin da kin zubar a cikinki.
“看哪,我因你所得不义之财和你中间所流的血,就拍掌叹息。
14 Ƙarfin halinki zai jure ko kuwa hannuwanki za su yi ƙarfi a ranar da na gamu da ke? Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata.
到了我惩罚你的日子,你的心还能忍受吗?你的手还能有力吗?我—耶和华说了这话,就必照着行。
15 Zan watsar da ke cikin al’ummai in warwatsa ke cikin ƙasashe; zan kuma kawo ƙarshen rashin tsarkinki.
我必将你分散在列国,四散在列邦。我也必从你中间除掉你的污秽。
16 Sa’ad da ki ƙazantu a idanun al’umma, za ki san cewa ni ne Ubangiji.’”
你必在列国人的眼前因自己所行的被亵渎,你就知道我是耶和华。”
17 Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
耶和华的话临到我说:
18 “Ɗan mutum, gidan Isra’ila ta zama ƙwan maƙera a gare ni; dukansu tagulla ne, kuza, ƙarfe da darma da suka rage a tanderu. Su ƙwan maƙerar azurfa ne kawai.
“人子啊,以色列家在我看为渣滓。他们都是炉中的铜、锡、铁、铅,都是银渣滓。
19 Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin ku duka kun zama ƙwan maƙera, zan tattara ku a Urushalima.
所以主耶和华如此说:因你们都成为渣滓,我必聚集你们在耶路撒冷中。
20 Kamar yadda mutane sukan tattara azurfa, tagulla, ƙarfe, darma da kuza a cikin tanderu don su narkar da su da wuta, haka zan tattara ku cikin fushina da kuma hasalata in sa ku cikin birnin in narkar da ku.
人怎样将银、铜、铁、铅、锡聚在炉中,吹火熔化;照样,我也要发怒气和忿怒,将你们聚集放在城中,熔化你们。
21 Zan tattara ku zan kuma hura muku wutar hasalata, za ku kuma narke a cikinta.
我必聚集你们,把我烈怒的火吹在你们身上,你们就在其中熔化。
22 Kamar yadda azurfa kan narke a tanderu, haka za ku narke a cikinta, kuma za ku san cewa Ni Ubangiji na zubo muku da zafin fushina.’”
银子怎样熔化在炉中,你们也必照样熔化在城中,你们就知道我—耶和华是将忿怒倒在你们身上了。”
23 Har yanzu maganar Ubangiji ta zo gare ni cewa,
耶和华的话临到我说:
24 “Ɗan mutum, ka faɗa wa ƙasar, ‘Ke ƙasa ce marar ruwan sama ko yayyafi a ranar hasala.’
“人子啊,你要对这地说:你是未得洁净之地,在恼恨的日子也没有雨下在你以上。
25 Akwai haɗin bakin sarakunanki a cikinki kamar rurin zaki mai yayyage ganimarsa; suna cin mutane, suna kwashe dukiya da abubuwa masu daraja suna mai da yawanci gwauraye a cikinki.
其中的先知同谋背叛,如咆哮的狮子抓撕掠物。他们吞灭人民,抢夺财宝,使这地多有寡妇。
26 Firistocinki suna karya dokokina, sun ƙazantar da tsarkakan abubuwana; ba sa bambanta tsakanin tsarki da marar tsarki; suna koyarwa cewa babu bambanci tsakanin marar tsarki da mai tsarki; suna kuma rufe idanunsu ga kiyaye Asabbataina, da haka suke saɓon sunana.
其中的祭司强解我的律法,亵渎我的圣物,不分别圣的和俗的,也不使人分辨洁净的和不洁净的,又遮眼不顾我的安息日;我也在他们中间被亵慢。
27 Shugabanninki a cikinki suna kama da kyarketai masu yayyage ganimarsu; suna kisa suna kuma kashe mutane don samun ƙazamar riba.
其中的首领仿佛豺狼抓撕掠物,杀人流血,伤害人命,要得不义之财。
28 Annabawanki sun yi wa waɗannan ayyuka shafe da farar ƙasa ta wurin wahayin ƙarya da duban ƙarya. Suna cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa’ alhali kuwa Ubangiji bai faɗa ba.
其中的先知为百姓用未泡透的灰抹墙,就是为他们见虚假的异象,用谎诈的占卜,说:‘主耶和华如此说’,其实耶和华没有说。
29 Mutanen ƙasar na yin ƙwace suna yin fashi; suna cin zalin matalauta da mabukata suna wulaƙanta baƙo suna hana musu adalci.
国内众民一味地欺压,惯行抢夺,亏负困苦穷乏的,背理欺压寄居的。
30 “Na nemi mutum guda a cikinsu wanda zai gina katanga ya tsaya a gabana a tsakani a madadin ƙasar don kada in hallaka ta, amma ban sami ko ɗaya ba.
我在他们中间寻找一人重修墙垣,在我面前为这国站在破口防堵,使我不灭绝这国,却找不着一个。
31 Saboda haka zan zuba hasalata a kansu in cinye su da wutar fushina, ina ɗora alhakin ayyukansu a bisa kawunansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
所以我将恼恨倒在他们身上,用烈怒的火灭了他们,照他们所行的报应在他们头上。这是主耶和华说的。”