< Ezekiyel 2 >

1 Ya ce mini, “Ɗan mutum, tashi ka tsaya a ƙafafunka zan kuma yi maka magana.”
“Son of man,” He said to me, “stand up on your feet and I will speak to you.”
2 Yayinda yake magana, sai Ruhu ya sauko mini ya kuma tā da ni a ƙafafuna, na kuma ji shi yana mini magana.
And as He spoke to me, the Spirit entered me and set me on my feet, and I heard Him speaking to me.
3 Ya ce, “Ɗan mutum, ina aikan ka zuwa ga Isra’ilawa, zuwa ga al’ummar’yan tawayen nan da suka yi mini tayarwa; su da kakanninsu sun yi mini tawaye har yă zuwa yau.
“Son of man,” He said to me, “I am sending you to the Israelites, to a rebellious nation that has rebelled against Me. To this very day they and their fathers have rebelled against Me.
4 Mutanen da nake aikan ka masu ƙin ji ne da kuma taurinkai. Ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’
They are obstinate and stubborn children. I am sending you to them, and you are to say to them, ‘This is what the Lord GOD says.’
5 Kuma ko su ji ko kada su ji, gama su gida ne mai tawaye, za su san cewa akwai annabi a cikinsu.
And whether they listen or refuse to listen—for they are a rebellious house—they will know that a prophet has been among them.
6 Kai kuwa, ɗan mutum, kada ka ji tsoro, ko da sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa duk sun kewaye ka kana kuma zama a cikin kunamai. Kada ka ji tsoron abin da za ka faɗa ko ka firgita ta wurinsu, ko da yake su gida ne mai tawaye.
But you, son of man, do not be afraid of them or their words. Do not be afraid, though briers and thorns surround you, and you dwell among scorpions. Do not be afraid of their words or dismayed by their presence, though they are a rebellious house.
7 Dole ka yi maganata gare su, ko su ji ko kada su ji, gama su’yan tawaye ne.
But speak My words to them, whether they listen or refuse to listen, for they are rebellious.
8 Amma kai, ɗan mutum, ka saurari abin da zan faɗa maka. Kada ka yi tawaye kamar wannan gidan’yan tawaye; ka buɗe bakinka ka kuma ci abin da na ba ka.”
And you, son of man, listen to what I tell you. Do not be rebellious like that rebellious house. Open your mouth and eat what I give you.”
9 Sai na duba, na kuma ga hannu ya miƙe zuwa wurina. A cikinsa akwai littafi,
Then I looked and saw a hand reaching out to me, and in it was a scroll,
10 wanda ya nannaɗe a gabana. A kowane gefensa akwai rubutun kalmomin makoki da kuka da kuma kaito.
which He unrolled before me. And written on the front and back of it were words of lamentation, mourning, and woe.

< Ezekiyel 2 >