< Ezekiyel 19 >

1 “Ka yi makoki game da sarakunan Isra’ila
Moreover, take thou up a lamentation for the princes of Israel,
2 ka ce, “‘Mahaifiyarki zakanya ce cikin zakoki! Takan kwanta cikin’yan zakoki ta kuma yi renon kwiyakwiyanta.
and say: —How lay thy mother at ease, a lioness among lions! Among young lions she nourished her whelps;
3 Ta goyi ɗaya daga cikin kwiyakwiyanta, ya yi girma ya zama zaki mai ƙarfi. Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta yakan kuma cinye mutane.
And she brought up one of her whelps; He became a young lion, And he learned to seize the prey; he devoured men.
4 Al’ummai suka ji labarinsa, aka kuma kama shi cikin raminsu. Suka ja shi da ƙugiyoyi zuwa ƙasar Masar.
And when the nations heard of him, he was taken in their pit, And they brought him with nose-rings to the land of Egypt.
5 “‘Sa’ad da ta ga sa zuciyarta bai cika ba, abin da take fata gani ya tafi, sai ta ɗauki wani daga cikin kwiyakwiyanta ta mai da shi zaki mai ƙarfi.
And when she saw that she waited in vain, and that her hope was lost, She took another of her whelps, and she made him a young lion.
6 Ya yi ta yawo a cikin zakoki, gama yanzu shi zaki ne mai ƙarfi. Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta yakan kuma cinye mutane.
And he went up and down among the lions; he became a young lion, And he learned to seize the prey; he devoured men.
7 Ya rurrushe kagaransu ya kuma ragargaza biranensu. Ƙasar da dukan waɗanda suke cikinta sun tsorata da jin rurinsa.
He knew their widows, and laid waste their cities, And the land was desolate, and all that was therein, before the voice of his roaring.
8 Sai al’ummai suka tayar masa, waɗannan daga yankunan da suke kewaye. Suka yafa raga dominsa ya kuwa fāɗa cikin raminsu.
Then the nations set themselves against him on every side from the provinces, And spread their net over him; He was taken in their pit.
9 Da ƙugiyoyi suka ja shi cikin keji suka kawo shi wurin sarkin Babilon. Suka sa shi cikin kurkuku, saboda haka ba a ƙara jin rurinsa a kan duwatsun Isra’ila ba.
And they put him with nose rings into a cage, And carried him to the king of Babylon. And they carried him to a stronghold, That his voice might be heard no more Upon the mountains of Israel.
10 “‘Mahaifiyarku kamar kuringa ce a cikin gonar inabi da aka shuka kusa da ruwa; ta ba da’ya’ya da kuma cikakkun rassa saboda yalwan ruwa.
Thy mother was like a vine planted like thyself by the waters; She was fruitful and full of branches by reason of many waters;
11 Rassanta suka yi ƙarfi, suka dace da sandar mai mulki. Ta yi tsayi zuwa sama ana ganin ta saboda tsayinta da kuma saboda yawan rassanta.
She had strong rods for sceptres of rulers, And her stature was high among the thick branches, So that she was conspicuous in her height, And the multitude of her branches.
12 Amma aka tumɓuke ta cikin fushi aka jefar da ita a ƙasa. Iskar gabas ta sa ta yanƙwane, aka kakkaɓe’ya’yanta; rassanta masu ƙarfi suka bushe wuta kuma ta cinye su.
But she was plucked up in fury, She was cast down to the ground, And the east wind dried up her fruit. Her strong rods were broken and withered; The fire consumed them.
13 Yanzu an shuka ta a hamada, a busasshiyar ƙasa marar ruwa.
And now she is planted in the desert, In a dry and thirsty land.
14 Wuta ta fito daga jikin rassanta ta cinye’ya’yanta. Babu sauran reshe mai ƙarfin da ya rage a kanta da ya dace da sandar mai mulki.’ Wannan waƙa ce kuma za a yi amfani da ita a matsayin makoki.”
And a fire is gone forth out of a rod of her branches, Which hath devoured her fruit, So that she hath no strong rod for a ruler's sceptre. This is a lamentation, and it shall be for a lamentation.

< Ezekiyel 19 >