< Ezekiyel 16 >

1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
ויהי דבר יהוה אלי לאמר
2 “Ɗan mutum, ka sa Urushalima ta san ayyukanta masu banƙyama
בן אדם הודע את ירושלם את תועבתיה
3 ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wa Urushalima, Asalinki da haihuwarki daga ƙasar Kan’ana ne; mahaifinki mutumin Amoriyawa ne, mahaifiyarki kuma mutuniyar Hitti ce.
ואמרת כה אמר אדני יהוה לירושלם מכרתיך ומלדתיך מארץ הכנעני אביך האמרי ואמך חתית
4 A ranar da aka haife ki ba a yanke cibiyarki ba, ba a kuma yi miki wanka don a tsabtacce ki ba, ba a kuma goge ki da gishiri ba ko a naɗe ki cikin tsummoki.
ומולדותיך ביום הולדת אותך לא כרת שרך ובמים לא רחצת למשעי והמלח לא המלחת והחתל לא חתלת
5 Ba wanda ya dube ki da tausayi ko ya nuna miki isashen jinƙai don yă yi miki ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa. A maimako, sai aka jefar da ke a fili, gama a ranar da aka haife ki an ji ƙyamarki.
לא חסה עליך עין לעשות לך אחת מאלה--לחמלה עליך ותשלכי אל פני השדה בגעל נפשך ביום הלדת אתך
6 “‘Sa’an nan na wuce na ga kina birgima cikin jininki, yayinda kike kwance can cikin jininki sai na ce miki, “Ki rayu!”
ואעבר עליך ואראך מתבוססת בדמיך ואמר לך בדמיך חיי ואמר לך בדמיך חיי
7 Na sa kin yi girma kamar tsiro a fili. Kin yi girma kika kuma yi tsayi kika zama mafiya kyau na kayan ado. Nononki suka fito, gashinki kuwa suka yi girma, duk da haka tsirara kike tik.
רבבה כצמח השדה נתתיך ותרבי ותגדלי ותבאי בעדי עדיים שדים נכנו ושערך צמח ואת ערם ועריה
8 “‘Daga baya na wuce, da na dube ki sai na ga cewa kin yi girma sosai har kin kai a ƙaunace ki, na yafa gefen tufafina a kanki na kuma rufe tsiraincinki. Na rantse miki, na ƙulla alkawari da ke, kin kuwa zama tawa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
ואעבר עליך ואראך והנה עתך עת דדים ואפרש כנפי עליך ואכסה ערותך ואשבע לך ואבוא בברית אתך נאם אדני יהוה--ותהיי לי
9 “‘Na yi miki wanka na wanke miki jini daga gare ki na kuma shafa miki mai.
וארחצך במים ואשטף דמיך מעליך ואסכך בשמן
10 Na rufe ki da rigar da aka yi wa ado na kuma sa miki takalman fata. Na sa miki riga ta lilin mai kyau na kuma rufe ki da riguna masu tsada.
ואלבישך רקמה ואנעלך תחש ואחבשך בשש ואכסך משי
11 Na yi miki ado da kayan ado masu daraja, na sa miki mundaye a hannuwanki da abin wuya a wuyanki,
ואעדך עדי ואתנה צמידים על ידיך ורביד על גרונך
12 na kuma sa miki zobe a hancinki, abin kunne a kunnuwanki da rawani mai kyau a kanki.
ואתן נזם על אפך ועגילים על אזניך ועטרת תפארת בראשך
13 Haka kuwa aka caɓa miki zinariya da azurfa; tufafinki kuwa na lilin mai kyau da riguna masu tsada waɗanda aka yi musu ado. Abincinki na gari mai laushi ne, zuma da man zaitun. Kika zama kyakkyawa har kika kuma zama sarauniya.
ותעדי זהב וכסף ומלבושך ששי (שש) ומשי ורקמה סלת ודבש ושמן אכלתי (אכלת) ותיפי במאד מאד ותצלחי למלוכה
14 Sunanki ya yaɗu a cikin al’ummai saboda kyanki, domin darajar da na ba ki ya sa kyanki ya zama cikakke, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
ויצא לך שם בגוים ביפיך כי כליל הוא בהדרי אשר שמתי עליך--נאם אדני יהוה
15 “‘Amma kika dogara ga kyanki kika kuma yi amfani da sunan da kika yi don ki zama karuwa. Kin yi ta jibga alherai a kan kowa da ya wuce, sai kyanki ya zama naki.
ותבטחי ביפיך ותזני על שמך ותשפכי את תזנותיך על כל עובר לו יהי
16 Kin ɗauki waɗansu tufafinki don ki yi wa kanki masujadai masu ado, inda kike karuwancinki. Irin waɗannan abubuwa bai kamata su faru ba, bai kuma kamata su taɓa faruwa ba.
ותקחי מבגדיך ותעשי לך במות טלאות ותזני עליהם לא באות ולא יהיה
17 Kika kuma ɗauki kayan ado masu kyau da na ba ki, kayan adon da aka yi da zinariya da azurfa, kika yi wa kanki gumakan maza kika kuma yi ta yin karuwanci da su.
ותקחי כלי תפארתך מזהבי ומכספי אשר נתתי לך ותעשי לך צלמי זכר ותזני בם
18 Kika ɗauki rigunanki masu ado don ki sa a kansu, kika kuma miƙa maina da turarena a gabansu.
ותקחי את בגדי רקמתך ותכסים ושמני וקטרתי נתתי (נתת) לפניהם
19 Haka ma abincin da na tanada miki, lallausan gari, man zaitun, da zuman da na ba ki ki ci, kin miƙa su kamar turare mai ƙanshi a gabansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
ולחמי אשר נתתי לך סלת ושמן ודבש האכלתיך ונתתיהו לפניהם לריח ניחח ויהי נאם אדני יהוה
20 “‘Kika kuma kwashe’ya’yanki maza da mata waɗanda kin haifa mini kika miƙa su kamar abinci ga gumakanki. Karuwancinki bai isa ba ne?
ותקחי את בניך ואת בנותיך אשר ילדת לי ותזבחים להם לאכול--המעט מתזנותך (מתזנותיך)
21 Kin kashe’ya’yana kika kuma miƙa su ga gumaka.
ותשחטי את בני ותתנים בהעביר אותם להם
22 Cikin dukan ayyukan banƙyamarki da karuwancinki ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba, sa’ad da kike tsirara tik, kina birgima cikin jininki.
ואת כל תועבתיך ותזנתיך לא זכרתי (זכרת) את ימי נעוריך--בהיותך עירם ועריה מתבוססת בדמך היית
23 “‘Kaito! Kaitonki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Bugu da ƙari a kan dukan waɗansu muguntarki,
ויהי אחרי כל רעתך אוי אוי לך נאם אדני יהוה
24 kin gina wa kanki ɗakunan sama da gidajen tsafi a kowane dandali.
ותבני לך גב ותעשי לך רמה בכל רחוב
25 A kowane titi kin gina ɗakin tsafi kika kuma wulaƙanta kyanki, kina miƙa jikinki da ƙarin fasikanci ga duk mai wucewa.
אל כל ראש דרך בנית רמתך ותתעבי את יפיך ותפשקי את רגליך לכל עובר ותרבי את תזנותך (תזנותיך)
26 Kin yi karuwanci da Masarawa, maƙwabtanki masu kwaɗayi, kika tsokane ni har na yi fushi da ƙarin fasikancinki.
ותזני אל בני מצרים שכניך גדלי בשר ותרבי את תזנתך להכעיסני
27 Saboda haka na miƙa hannuna gāba da ke na kuma rage iyakarki; na ba da ke ga abokan gābanki masu haɗama,’yan matan Filistiyawa, waɗanda suka sha mamaki saboda halinki na lalata.
והנה נטיתי ידי עליך ואגרע חקך ואתנך בנפש שנאותיך בנות פלשתים--הנכלמות מדרכך זמה
28 Kin kuma yi karuwanci da Assuriyawa, domin ba kya ƙoshi; kai ko bayan wannan, ba ki ƙoshi ba.
ותזני אל בני אשור מבלתי שבעתך ותזנים וגם לא שבעת
29 Sai kika ƙara fasikancinki da ya haɗa da ƙasar cinikin Babilon, amma duk da haka ba ki ƙoshi ba.
ותרבי את תזנותך אל ארץ כנען כשדימה וגם בזאת לא שבעת
30 “‘Kina da rashin ƙarfi a zuci, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, sa’ad da kika yi duk waɗannan abubuwa, kina yi kamar karuwar da aka watsa!
מה אמלה לבתך נאם אדני יהוה--בעשותך את כל אלה מעשה אשה זונה שלטת
31 Sa’ad da kika gina ɗakunan samanki a kowane gefen titi kika kuma gina ɗakunan tsafinki a kowane dandali, ba kamar karuwa kike ba, domin kin karɓi kuɗi.
בבנותיך גבך בראש כל דרך ורמתך עשיתי (עשית) בכל רחוב ולא הייתי (היית) כזונה לקלס אתנן
32 “‘Ke mazinaciyar mace! Kin gwammace baƙi a maimakon mijinki!
האשה המנאפת--תחת אישה תקח את זרים
33 Kowace karuwa kan karɓi kuɗi, amma kina ba da kyautai ga dukan kwartayenki, kina ba su cin hanci don su zo wurinki daga ko’ina don alherai marasa ƙa’ida.
לכל זנות יתנו נדה ואת נתת את נדניך לכל מאהביך ותשחדי אותם לבוא אליך מסביב בתזנותיך
34 Saboda haka cikin karuwancinki kin sha bamban da saura; babu wanda yake binki saboda alheranki. Ke dai dabam ce, gama kikan biya kuma ba mai biyanki.
ויהי בך הפך מן הנשים בתזנותיך ואחריך לא זונה ובתתך אתנן ואתנן לא נתן לך--ותהי להפך
35 “‘Saboda haka, ke karuwa, ki ji maganar Ubangiji!
לכן זונה שמעי דבר יהוה
36 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kin zubar da dukiyarki kika bayyana tsiraicinki cikin fasikancinki da kwartayenki, kuma saboda dukan gumakan banƙyamarki, kuma saboda kin ba su jinin’ya’yansu,
כה אמר אדני יהוה יען השפך נחשתך ותגלה ערותך בתזנותיך על מאהביך ועל כל גלולי תועבותיך וכדמי בניך אשר נתת להם
37 saboda haka zan tattara dukan kwartayenki, waɗanda kike jin daɗinsu, waɗanda kike ƙauna da waɗanda kike ƙi. Zan tattara su gāba da ke daga dukan kewaye zan kuma tuɓe ki a gabansu, za su kuwa ga dukan tsiraicinki.
לכן הנני מקבץ את כל מאהביך אשר ערבת עליהם ואת כל אשר אהבת על כל אשר שנאת וקבצתי אתם עליך מסביב וגליתי ערותך אלהם וראו את כל ערותך
38 Zan hukunta ki da hukuncin matan da suke zina da kuma waɗanda suke zub da jini; zan kawo hakkin jini na fushina da kuma fushin kishina.
ושפטתיך משפטי נאפות ושפכת דם ונתתיך דם חמה וקנאה
39 Sa’an nan zan miƙa ki ga kwartayenki, za su kuwa rurrushe ɗakunan samanki su kuma farfashe ɗakunan tsafinki. Za su tuɓe miki tufafinki su kuma kwashe kayan adonki masu kyau su bar ki tsirara tik.
ונתתי אתך בידם והרסו גבך ונתצו רמתיך והפשיטו אותך בגדיך ולקחו כלי תפארתך והניחוך עירם ועריה
40 Za su kawo taron jama’a a kanki, waɗanda za su jajjefe ki da dutse su sassare ki gunduwa-gunduwa da takubansu.
והעלו עליך קהל ורגמו אותך באבן ובתקוך בחרבותם
41 Za su ƙone gidajenki su kuma hukunta ki a idon mata masu yawa. Zan kawo ƙarshen karuwancinki, ba za ki kuma ƙara biyan kwartayenki ba.
ושרפו בתיך באש ועשו בך שפטים לעיני נשים רבות והשבתיך מזונה וגם אתנן לא תתני עוד
42 Sa’an nan fushina a kanki zai huce fushin kishina kuma ya kwanta; zan huce ba kuwa zan ƙara yin fushi ba.
והנחתי חמתי בך וסרה קנאתי ממך ושקטתי ולא אכעס עוד
43 “‘Domin ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba amma kika husatar da ni da waɗannan abubuwa, tabbatacce zan sāka miki alhakin ayyukanki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ba kin ƙara lalata ga dukan waɗansu ayyuka masu banƙyamarki ba?
יען אשר לא זכרתי (זכרת) את ימי נעוריך ותרגזי לי בכל אלה וגם אני הא דרכך בראש נתתי נאם אדני יהוה ולא עשיתי (עשית) את הזמה על כל תועבתיך
44 “‘Duk mai yin amfani da karin magana zai faɗi wannan karin magana a kanki cewa, “Kamar yadda mahaifiya take haka’yar take.”
הנה כל המשל עליך ימשל לאמר כאמה בתה
45 Ke’yar mahaifiyarki ce da gaske, wadda ta ƙi mijinta da’ya’yanta; ke kuma’yar’uwar’yar’uwanki mata ce da gaske, waɗanda suka ƙi mazansu da’ya’yansu. Mahaifiyarki mutuniyar Hitti ce, mahaifinki kuma mutumin Amoriyawa ne.
בת אמך את געלת אישה ובניה ואחות אחותך את אשר געלו אנשיהן ובניהן--אמכן חתית ואביכן אמרי
46 Babbar’yar’uwarki mutuniyar Samariya ce, wadda take zaune da’ya’yanta mata wajen arewa da ke; ƙanuwarki ita ce Sodom wadda take zaune kudu da ke tare da’ya’yanta mata.
ואחותך הגדולה שמרון היא ובנותיה היושבת על שמאולך ואחותך הקטנה ממך היושבת מימינך--סדם ובנותיה
47 Ba ki bi hanyoyinsu da abubuwansu na banƙyama kaɗai ba, sai ka ce wannan ya yi miki kaɗan, amma kin lalace fiye da su.
ולא בדרכיהן הלכת וכתועבותיהן עשיתי (עשית) כמעט קט ותשחתי מהן בכל דרכיך
48 Muddin in raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka,’yar’uwarki Sodom da’ya’yanta mata ba su yi abin da’ya’yanki mata suka yi ba.
חי אני נאם אדני יהוה אם עשתה סדם אחותך היא ובנותיה--כאשר עשית את ובנותיך
49 “‘To, fa, ga zunubin’yar’uwarki Sodom. Ita da’ya’yanta mata sun yi girman kai, sun ƙoshi fiye da kima kuma ba su kula da wani abu ba; ba su taimaki matalauta da kuma masu bukata ba.
הנה זה היה עון סדם אחותך גאון שבעת לחם ושלות השקט היה לה ולבנותיה ויד עני ואביון לא החזיקה
50 Su masu girman kai ne kuma suka aikata abubuwa masu banƙyama a gabana. Saboda haka na kau da su kamar yadda ka gani.
ותגבהינה ותעשינה תועבה לפני ואסיר אתהן כאשר ראיתי
51 Samariya ba tă aikata ko rabin zunubanki ba. Kin aikata abubuwa masu banƙyama fiye da su, suka kuma sa’yan’uwanki mata suka zama kamar masu adalci ta wurin dukan waɗannan abubuwa da kika aikata.
ושמרון כחצי חטאתיך לא חטאה ותרבי את תועבותיך מהנה ותצדקי את אחותך (אחותיך) בכל תועבתיך אשר עשיתי (עשית)
52 Ki sha kunyarki, gama kin yi rangwame wa’yan’uwanki mata. Saboda zunubanki sun yi muni fiye da nasu, sai suka zama kamar sun fi ki adalci. Saboda haka, ki sha kunya ki kuma sha ƙasƙancinki, gama kin sa’yan’uwanki mata suka zama kamar su masu adalci ne.
גם את שאי כלמתך אשר פללת לאחותך בחטאתיך אשר התעבת מהן תצדקנה ממך וגם את בושי ושאי כלמתך בצדקתך אחיותך
53 “‘Amma fa, zan komo da nasarar Sodom da’ya’yanta mata da ta Samariya da’ya’yanta mata, nasararki kuma tare da su,
ושבתי את שביתהן--את שבית (שבות) סדם ובנותיה ואת שבית (שבות) שמרון ובנותיה ושבית (ושבות) שביתיך בתוכהנה
54 domin ki sha ƙasƙancinki ki kuma sha kunyar dukan abin da kika aikata ta wurin ta’azantar da su.
למען תשאי כלמתך ונכלמת מכל אשר עשית--בנחמך אתן
55 ’Yan’uwanki kuwa, Sodom da’ya’yanta mata da Samariya tare da’ya’yanta mata, za su koma kamar yadda suke a dā; ke kuma da’ya’yanki mata za ku koma kamar yadda kike a dā.
ואחותיך סדם ובנותיה תשבן לקדמתן ושמרון ובנותיה תשבן לקדמתן ואת ובנותיך תשבינה לקדמתכן
56 Ba za ki ma iya ambaci’yar’uwarki Sodom a ranar fariyarki ba,
ולוא היתה סדם אחותך לשמועה בפיך ביום גאוניך
57 kafin a tone muguntarki. Ko da ma haka, yanzu’ya’yan Arameyawa mata da dukan maƙwabtanta da kuma’ya’yan Filistiyawa mata suna miki dariyar, dukan waɗanda suke kewaye da ke da suka rena ki.
בטרם תגלה רעתך כמו עת חרפת בנות ארם וכל סביבותיה בנות פלשתים השאטות אותך מסביב
58 Za ki ɗauki hakkin lalatarki da kuma ayyukanki masu banƙyama, in ji Ubangiji.
את זמתך ואת תועבותיך את נשאתים--נאם יהוה
59 “‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan hukunta kamar yadda ya dace da ke, domin kin ƙyale rantsuwana ta wurin karya alkawari.
כי כה אמר אדני יהוה ועשית (ועשיתי) אותך כאשר עשית--אשר בזית אלה להפר ברית
60 Duk da haka zan tuna da alkawarin da na yi da ke a kwanakin ƙuruciyarki, zan kuma kafa madawwamin alkawari da ke.
וזכרתי אני את בריתי אותך בימי נעוריך והקימותי לך ברית עולם
61 Sa’an nan za ki tuna da hanyoyinki ki kuma ji kunya sa’ad da kika karɓi’yan’uwanki mata, waɗanda suka girme ki da kuma waɗanda kika girme su. Zan ba da su kamar’ya’ya mata gare ki, amma ba bisa alkawarina da ke ba.
וזכרת את דרכיך ונכלמת בקחתך את אחותיך הגדלות ממך אל הקטנות ממך ונתתי אתהן לך לבנות ולא מבריתך
62 Ta haka zan kafa alkawarina da ke, za ki kuma san cewa ni ne Ubangiji.
והקימתי אני את בריתי אתך וידעת כי אני יהוה
63 Sa’an nan, sa’ad da na yi kafara saboda ke domin dukan abin da kika aikata, za ki tuna ki kuma ji kunya har ki kāsa buɗe bakinki saboda kunya, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’”
למען תזכרי ובשת ולא יהיה לך עוד פתחון פה מפני כלמתך--בכפרי לך לכל אשר עשית נאם אדני יהוה

< Ezekiyel 16 >