< Fitowa 6 >

1 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Yanzu za ka gan abin da zan yi da Fir’auna. Zan sa shi dole yă bar su su tafi, har ma yă iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!”
And the Lord said to Moses: “Now you will see what I shall do to Pharaoh. For through a strong hand he will release them, and by a mighty hand he will cast them from his land.”
2 Allah ya kuma ce wa Musa, “Ni ne Ubangiji.
And the Lord spoke to Moses, saying: “I am the Lord,
3 Na bayyana ga Ibrahim, ga Ishaku da kuma ga Yaƙub a matsayin Allah Maɗaukaki, amma sunan nan nawa Ubangiji, ban bayyana kaina a gare su ba.
who appeared to Abraham, to Isaac, and to Jacob as Almighty God. And I did not reveal to them my name: ADONAI.
4 Na kuma kafa alkawari da su don in ba su ƙasar Kan’ana, inda suka yi zaman baƙunci.
And I formed a covenant with them, in order to give them the land of Canaan, the land of their sojourning, in which they were newcomers.
5 Ban da haka ma, na ji nishe-nishen Isra’ilawa, waɗanda Masarawa suka bautar, na kuma tuna da alkawarina.
I have heard the groaning of the sons of Israel, with which the Egyptians have oppressed them. And I have remembered my covenant.
6 “Saboda haka, ka ce wa Isra’ilawa, ‘Ni ne Ubangiji, zan kuma fitar da ku daga bauta ta Masarawa. Zan’yantar da ku daga zama bayinsu, da ƙarfina zan fanshe ku, in kawo hukunci mai zafi a kansu, don in cece ku.
For this reason, say to the sons of Israel: I am the Lord who will lead you away from the work house of the Egyptians, and rescue you from servitude, and also redeem you with an exalted arm and great judgments.
7 Zan ɗauke ku tamƙar mutanena, in kuma zama Allahnku. Sa’an nan za ku sani Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga wahalar Masarawa.
And I will take you to myself as my people, and I will be your God. And you will know that I am the Lord your God, who led you away from the work house of the Egyptians,
8 Zan kuwa kawo ku a ƙasar da na rantse da hannun da na ɗaga sama, cewa zan ba wa Ibrahim, wa Ishaku, da kuma wa Yaƙub. Zan ba da ita gare ku gādo. Ni ne Ubangiji.’”
and who brought you into the land, over which I lifted up my hand in order to grant it to Abraham, Isaac, and Jacob. And I will grant it to you as a possession. I am the Lord.”
9 Musa ya faɗa wa Isra’ilawa wannan magana, amma ba su kasa kunne a gare shi ba, don ɓacin rai saboda tsananin aikin bauta.
And so, Moses explained all these things to the sons of Israel, who did not agree with him, because of their anguish of spirit and very difficult work.
10 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,
And the Lord spoke to Moses, saying:
11 “Koma ka ce wa Fir’auna sarkin Masar, yă bar Isra’ilawa su fita daga ƙasarsa.”
“Enter and speak to Pharaoh, king of Egypt, so that he may release the sons of Israel from his land.”
12 Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “In Isra’ilawa ba su ji ni ba, yaya Fir’auna zai ji ni, da yake ina magana da ƙyar?”
Moses responded in the sight the Lord: “Behold, the sons of Israel do not listen to me. And how will Pharaoh listen to me, especially since I am of uncircumcised lips?”
13 Ubangiji ya yi magana da Musa da Haruna game da Isra’ilawa da Fir’auna sarkin Masar, ya umarce su su fitar da Isra’ilawa daga Masar.
And the Lord spoke to Moses and Aaron, and he gave them a commandment for the sons of Israel, and for Pharaoh, the king of Egypt, that they should lead the sons of Israel away from the land of Egypt.
14 Waɗannan su ne shugabannin iyalansu.’Ya’yan Ruben maza ɗan farin Isra’ila su ne, Hanok da Fallu, Hezron da Karmi. Waɗannan su ne dangin Ruben.
These are the leaders of the houses by their families. The sons of Reuben, the firstborn of Israel: Hanoch and Pallu, Hezron and Carmi.
15 ’Ya’yan Simeyon maza su ne, Yemuwel, Yamin, Ohad, Yakin, Zohar da Sha’ul ɗan mutuniyar Kan’ana. Waɗannan su ne dangin Simeyon.
These are the kindred of Reuben. The sons of Simeon: Jemuel and Jamin, and Ohad, and Jachin, and Zohar, and Shaul, the son of a Canaanite women. These are the progeny of Simeon.
16 Waɗannan su ne sunayen’ya’yan Lawi maza bisa ga abin da aka rubuta, Gershon, Kohat da Merari. Lawi ya yi shekara 137.
And these are the names of the sons of Levi by their kindred: Gershon, and Kohath, and Merari. Now the years of the life of Levi were one hundred and thirty-seven.
17 ’Ya’yan Gershon maza, bisa ga dangi su ne, Libni da Shimeyi.
The sons of Gershon: Libni and Shimei, by their kindred.
18 ’Ya’yan Kohat maza, su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel. Kohat ya yi shekara 133.
The sons of Kohath: Amram, and Izhar, and Hebron and Uzziel. Likewise, the years of the life of Kohath were one hundred and thirty-three.
19 ’Ya’yan Merari maza, su ne, Mali da Mushi. Waɗannan su ne dangin Lawi bisa ga abin da aka rubuta.
The sons of Merari: Mahli and Mushi. These are the kindred of Levi by their families.
20 Amram ya auri’yar’uwar mahaifinsa Yokebed, wadda ta haifa masa Haruna da Musa. Amram ya yi shekara 137.
Now Amram took as a wife Jochebed, his paternal aunt, who bore for him Aaron and Moses. And the years of the life of Amram were one hundred and thirty-seven.
21 ’Ya’yan Izhar maza, su ne, Kora, Nefeg da Zikri.
Likewise, the sons of Izhar: Korah, and Nepheg, and Zichri.
22 ’Ya’yan Uzziyel maza, su ne, Mishayel, Elzafan da Sitri.
Likewise, the sons of Uzziel: Mishael, and Elzaphan, and Sithri.
23 Haruna ya auri Elisheba,’yar Amminadab,’yar’uwar Nashon, sai ta haifa masa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar.
Now Aaron took as a wife Elizabeth, the daughter of Amminadab, sister of Nahshon, who bore for him Nadab, and Abihu, and Eleazar, and Ithamar.
24 ’Ya’yan Kora maza, su ne, Assir, Elkana da Abiyasaf. Waɗannan su ne dangin Kora.
Likewise, the sons of Korah: Assir, and Elkanah, and Abiasaph. These are the kindred of the Korahites.
25 Eleyazar ɗan Haruna, ya auri ɗaya daga cikin’yan matan Futiyel, sai ta haifa masa Finehas. Waɗannan su ne shugabannin iyalan Lawi, dangi, dangi.
And truly Eleazar, the son of Aaron, took a wife from the daughters of Putiel. And she bore him Phinehas. These are the heads of the Levitical families by their kindred.
26 Wannan Haruna da Musa ne, waɗanda Ubangiji ya yi musu magana ya ce, “Ku fitar da Isra’ilawa daga Masar ɓangare-ɓangare.”
These are Aaron and Moses, whom the Lord instructed to lead the sons of Israel away from the land of Egypt by their companies.
27 Su ne suka yi magana da Fir’auna sarkin Masar game da fitar da Isra’ilawa daga Masar, wannan Musa da Haruna.
These are those who speak to Pharaoh, king of Egypt, in order to lead the sons of Israel out of Egypt. These are Moses and Aaron,
28 Ana nan, sa’ad da Ubangiji ya yi magana da Musa a Masar,
in the day when the Lord spoke to Moses in the land of Egypt.
29 ya ce masa, “Ni ne Ubangiji. Sai ka faɗa wa Fir’auna sarkin Masar kome da na faɗa maka.”
And the Lord spoke to Moses, saying: “I am the Lord. Speak to Pharaoh, king of Egypt, all that I speak to you.”
30 Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ni mai nauyin baki ne, ina magana da ƙyar, ƙaƙa Fir’auna zai kasa kunne gare ni?”
And Moses said in the sight of the Lord: “Lo, I am of uncircumcised lips, how will Pharaoh listen to me?”

< Fitowa 6 >