< Fitowa 39 >

1 Daga zare mai ruwan shuɗi, da shuɗayya da kuma jan zare suka yi tsarkaken rigunan domin hidima a wuri mai tsarki. Suka kuma yi tsarkaken riguna don Haruna, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
With the blue, purple, and scarlet wool, they made finely-woven garments for service in the holy place. They made Aaron's garments for the holy place, as Yahweh had commanded Moses.
2 Suka yi efod na zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da kuma lallausan lilin.
Bezalel made the ephod of gold, of blue, purple, and scarlet wool, and of fine twined linen.
3 Suka bubbuga zinariya ta zama falle, suka yayyanka ta zare-zare don su yi saƙa da ita, tare da zane na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da na lallausan lilin, aikin gwani mai fasaha.
They hammered gold sheets and cut them into wires, to work them into the blue, purple, and scarlet wool, and into the fine linen, the work of a skillful workman.
4 Suka yi wa efod kafaɗu, sa’an nan suka haɗa su a gefenta biyu na sama, don a iya ɗaurawa.
They made shoulder pieces for the ephod, attached at its two upper corners.
5 Gwanin mai saƙa ya saƙa abin ɗamarar efod. Da irin kayan da aka saƙa efod ne aka saƙa abin ɗamarar, wato, da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da zaren lallausan lilin, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Its finely-woven waistband was like the ephod; it was made of one piece with the ephod, made of fine twined linen that was gold, blue, purple, and scarlet, just as Yahweh had commanded Moses.
6 Suka shimfiɗa duwatsun onis, suka jera su cikin tsaiko na zinariya, suka kuma zāna sunayen’ya’yan Isra’ila a kan duwatsun kamar yadda akan yi hatimi.
They crafted the onyx stones, enclosed in settings of gold, set with engravings as on a signet, and engraved with the names of Israel's twelve sons.
7 Sa’an nan suka ɗaura su a ƙyallen kafaɗun efod a matsayin duwatsun tuni wa’ya’yan Isra’ila, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Bezalel put them on the shoulder pieces of the ephod, as stones to remind Yahweh of Israel's twelve sons, as Yahweh had commanded Moses.
8 Suka yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji, aikin gwani. Suka yi shi kamar efod, na zinariya, da na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da kuma na lallausan lilin.
He made the breastpiece, the work of a skillful workman, fashioned like the ephod. He made it of gold, of blue, purple, and scarlet wool, and of fine linen.
9 Ƙyallen maƙalawa a ƙirjin murabba’i ne, aka ninka shi biyu, tsawonsa da fāɗinsa kamu ɗaya-ɗaya ne.
It was square. They folded the breastpiece double. It was one span long and one span wide.
10 Sa’an nan suka sa jeri huɗu na duwatsu masu daraja a bisansa. A jeri na farko akwai yakutu, da tofaz, da zumurrudu;
They set in it four rows of precious stones. The first row had a ruby, a topaz, and a garnet.
11 a jeri na biyu akwai turkuwoyis, da saffaya, da daimon;
The second row had an emerald, a sapphire, and a diamond.
12 a jeri na uku akwai yakinta, da idon mage, da ametis;
The third row had a jacinth, an agate, and an amethyst.
13 a jeri na huɗu akwai beril, da onis, da yasfa. Aka sa su cikin tsaiko na zinariya.
The fourth row had a beryl, an onyx, and a jasper. The stones were mounted in gold settings.
14 Aka zāna duwatsu goma sha biyu, ɗaya don kowane sunan’ya’yan Isra’ila goma sha biyu, kamar yadda akan yi hatimi.
The stones were arranged by the names of Israel's twelve sons, each in order by name. They were like the engraving on a signet ring, each name standing for one of the twelve tribes.
15 Sai suka yi tuƙaƙƙun sarƙoƙi na zinariya zalla a kan ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
On the breastpiece they made chains like cords, braided work of pure gold.
16 Suka yi tsaiko biyu na zinariya da zoban zinariya biyu, suka kuma ɗaura zoban a kusurwoyi biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
They made two settings of gold and two gold rings, and they attached the two rings to the two corners of the breastpiece.
17 Suka ɗaura sarƙoƙi biyu na zinariya da kusurwoyi na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
They put the two braided chains of gold in the two rings at the corners of the breastpiece.
18 Suka maƙala waɗancan bakin sarƙoƙin zinariya a tsaikon nan biyu, sa’an nan suka rataya su a kafaɗun efod daga gaba.
They attached the other two ends of the braided chains to the two settings. They attached them to the shoulder pieces of the ephod at its front.
19 Suka yi zobai biyu na zinariya suka haɗa, suka sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji daga ciki kusa da efod.
They made two rings of gold and put them on the two other corners of the breastpiece, on the edge next to the inner border.
20 Sa’an nan suka yi waɗansu ƙarin zobai biyu na zinariya, suka maƙale su daga ƙasa a gaban kafaɗu biyu na efod kusa da mahaɗin a bisa abin ɗamarar efod.
They made two more gold rings and attached them to the bottom of the two shoulder pieces of the front of the ephod, close to its seam above the finely-woven waistband of the ephod.
21 Suka ɗaura zoban ƙyallen maƙalawa a ƙirjin a zoban efod da shuɗiyar igiya don ƙyallen maƙalawa a ƙirji, ya kwanta lif a bisa kan abin ɗamarar efod don kada yă kunce daga efod, sun yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.
They tied the breastpiece by its rings to the ephod's rings with a blue cord, so that it might be attached just above the ephod's finely-woven waistband. This was so that the breastpiece might not become unattached from the ephod. This was done as Yahweh had commanded Moses.
22 Suka kuma saƙa taguwa ta efod da shuɗi duka, aikin gwani mai saƙa,
Bezalel made the robe of the ephod entirely of blue fabric, the work of a weaver.
23 an yi wa taguwar wuyan wundi a tsakiya kamar sulke, aka daje wuyan don kada yă kece.
It had an opening for the head in the middle. The opening had a woven edge round about so that it did not tear.
24 Suka yi fasalin’ya’yan rumman da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da lallausan lilin kewaye da gefe-gefen taguwar.
On the bottom hem, they made pomegranates of blue, purple, and scarlet yarn and of fine linen.
25 Suka yi ƙararrawa da zinariya zalla, suka sa su a tsakanin fasalin’ya’yan rumman kewaye da gefe-gefen taguwa.
They made bells of pure gold, and they put the bells between the pomegranates all around on the bottom edge the robe, between the pomegranates—
26 Aka jera ƙararrawan da’ya’yan rumman bi da bi. Haka aka jera su kewaye da gefe-gefen taguwar aiki, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
a bell and a pomegranate, a bell and a pomegranate—on the edge of the robe for Aaron to serve in. This was as Yahweh had commanded Moses.
27 Suka saƙa doguwar riga da lallausan lilin don Haruna da’ya’yansa, aikin gwani mai saƙa,
They made the coats of fine linen for Aaron and for his sons.
28 suka yi rawanin da lallausan lilin, da hulan lilin da rigunan ciki na lallausan lilin.
They made the turban of fine linen, the ornate headbands of fine linen, the linen undergarments of fine linen,
29 Suka yi abin ɗamara da lallausan lilin da shuɗi, shunayya da jan zare, aikin gwanin mai ɗinki, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
and the sash of fine linen and of blue, purple, and scarlet yarn, the work of an embroiderer. This was as Yahweh had commanded Moses.
30 Suka yi allo tsattsarka da zinariya tsantsa, suka zāna rubutu irin na hatimi a kansa haka, Mai tsarki ga Ubangiji.
They made the plate of the holy crown of pure gold; they engraved on it, like the engraving on a signet, “Holy to Yahweh.”
31 Sa’an nan suka ɗaura shi da shuɗiyar igiya a gaban rawanin, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
They attached to the turban a blue cord to the top of the turban. This was as Yahweh had commanded Moses.
32 Ta haka aka gama dukan aikin tabanakul da Tentin Sujada. Isra’ilawa suka yi kome yadda Ubangiji ya umarci Musa.
So the work on the tabernacle, the tent of meeting, was finished. The people of Israel did everything. They followed all the instructions that Yahweh had given to Moses.
33 Sa’an nan suka kawo wa Musa tabanakul, tentin da dukan kayayyakinsa, ƙugiyoyinsa, katakansa, da sandunansa, da dogayen sandunansa da rammukansa;
They brought the tabernacle to Moses—the tent and all its equipment, its clasps, frames, bars, posts, and bases;
34 murfi na fatun rago wanda aka rina ja, da murfi na fatun shanun teku; da kuma laɓulen
the covering of ram skins dyed red, the covering of sea cow leather, and the curtain to conceal
35 akwatin Alkawari da sandunansa da murfin kafara;
the ark of the testimony, as well as the poles and the atonement lid.
36 tebur da dukan kayayyakinsa, da burodin Kasancewa;
They brought the table, all its utensils, and the bread of the presence;
37 wurin ajiye fitilu na zinariya zalla, da jerin fitilunsa da dukan kayayyakinsa, da man fitila,
the lampstand of pure gold and its lamps in a row, with its accessories and the oil for the lamps;
38 bagade na zinariya, da man shafewa, da turare mai ƙanshi, da labulen ƙofar shiga tenti,
the golden altar, the anointing oil and the fragrant incense; the hanging for the tabernacle entrance;
39 bagade na tagulla na raga, da sandunansa da kayan aikinsa; da daro da wurin ajiyarsa,
the bronze altar with its bronze grate and its poles and utensil and the large basin with its base.
40 labulen filin, sandunansa da rammukansa, labulen ƙofar shiga filin; igiyoyi da ƙarafan kafa filin; dukan kayan aikin tabanakul da Tentin Sujada;
They brought the hangings for the courtyard with its posts and bases, and the curtain for the courtyard entrance; its ropes and tent pegs; and all the equipment for the service of the tabernacle, the tent of meeting.
41 da kuma saƙaƙƙun rigunan da ake sawa don hidima a wuri mai tsarki, duk da tsarkakan riguna na Haruna firist da rigunan’ya’yansa maza, sa’ad da suke hidima a matsayin firistoci.
They brought the fine woven garments for serving in the holy place, the holy garments for Aaron the priest and his sons, for them to serve as priests.
42 Isra’ilawa suka yi dukan aikin nan yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Thus the people of Israel did all the work as Yahweh had commanded Moses.
43 Musa ya duba aikin, sai ya ga cewa sun yi shi daidai yadda Ubangiji ya umarta. Sai Musa ya sa musu albarka.
Moses examined all the work, and, behold, they had done it. As Yahweh had commanded, in that way they did it. Then Moses blessed them.

< Fitowa 39 >