< Fitowa 35 >
1 Musa ya tara dukan jama’ar Isra’ilawa ya ce musu, “Waɗannan su ne abubuwan da Ubangiji ya umarce ku, ku yi.
And all the multitude of the children of Israel being gathered together, he said to them: These are the things which the Lord hath commanded to be done.
2 Kwana shida za ku yi aiki, amma rana ta bakwai za tă zama rana mai tsarki, Asabbaci ne na hutu ga Ubangiji. Duk wanda ya yi aiki a wannan rana dole a kashe shi.
Six days you shall do work: the seventh day shall be holy unto you, the sabbath, and the rest of the Lord: he that shall do any work on it, shall be put to death.
3 Kada ku hura wuta a cikin duk mazauninku a ranar Asabbaci.”
You shall kindle no fire in any of your habitations on the sabbath day.
4 Musa ya ce wa dukan jama’ar Isra’ilawa, “Ga abin da Ubangiji ya umarta.
And Moses said to all the assembly of the children of Israel: This is the word the Lord hath commanded, saying:
5 Daga cikin abin da kuke da shi, ku ɗauki kyauta domin Ubangiji, duk wanda yana niyya, sai yă kawo wa Ubangiji kyauta ta, “zinariya, azurfa da tagulla;
Set aside with you firstfruits to the Lord. Let every one that is willing and hath a ready heart, offer them to the Lord: gold, and silver, and brass,
6 shuɗi, shunayya da jan zare, lallausan lilin, da gashin akuya;
Violet and purple, and scarlet twice dyed, and fine linen, goats’ hair,
7 fatun rago da aka rina ja, da fatun shanun teku; da itacen ƙirya
And rams’ skins dyed red, and violet coloured skins, setim wood,
8 da man zaitun don fitila; da kayan yaji don man shafewa, da kuma turare mai ƙanshi;
And oil to maintain lights, and to make ointment, and most sweet incense.
9 duwatsun onis, da sauran duwatsu masu daraja waɗanda za a mammanne a efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
Onyx stones, and precious stones, for the adorning of the ephod and the rational.
10 “Duk waɗanda suke da fasaha a cikinku, su zo su yi dukan abin da Ubangiji ya umarta,
Whosoever of you is wise, let him come, and make that which the Lord hath commanded:
11 “wato, aikin tabanakul da tentinsa tare da murfinsa, maɗauransa, katakansa, sandunansa da tussansa;
To wit, the tabernacle and the roof thereof, and the cover, the rings, and the board work with the oars, the pillars, and the sockets:
12 akwatin alkawari da sandunansa, murfin kafara da labulen da ya rufe shi;
The ark and the staves, the propitiatory, and the veil that is drawn before it:
13 tebur da sandunansa, da dukan kayansa da kuma burodin kasancewa;
The table with the bars and the vessels, and the loaves of proposition:
14 wurin ajiye fitila da yake don fitilu da kayayyakinsa, fitilu da mai don fitila;
The candlestick to bear up the lights, the vessels thereof and the lamps, and the oil for the nourishing of fires:
15 bagaden turare da sandunansa, man shafewa da turare mai ƙanshi; da labulen ƙofar shiga tabanakul;
The altar of incense, and the bars, and the oil of unction and the incense of spices: the hanging at the door of the tabernacle:
16 bagaden hadaya ta ƙonawa da rigarsa ta tagulla da sandunansa da duk kayayyakinsa, daron tagulla da wurin ajiye shi.
The altar of holocaust, and its grate of brass, with the bars and vessels thereof: the laver and its foot:
17 Labulen filin tenti da sandunansa da tussansa, da kuma labulen ƙofar shiga fili;
The curtains of the court with the pillars and the sockets, the hanging in the doors of the entry,
18 turakun tenti don tabanakul da kuma don filin, da igiyoyinsu;
The pins of the tabernacle and of the court with their little cords:
19 saƙaƙƙun riguna na sawa don hidima cikin wuri mai tsarki da tsarkakakkun riguna na Haruna firist, da riguna don’ya’yansa maza lokacin da suke aiki a matsayin firistoci.”
The vestments that are to be used in the ministry of the sanctuary, the vesture of Aaron the high priest, and of his sons, to do the office of priesthood to me.
20 Sai dukan jama’ar Isra’ilawa suka janye daga fuskar Musa,
And all the multitude of the children of Israel going out from the presence of Moses,
21 duk waɗanda suke da niyya, waɗanda kuma zukatansu suka motsa su, suka kawo kyautai wa Ubangiji, don aikin Tentin Sujada, don duk aikinsa, da don tsarkakakkun riguna.
Offered firstfruits to the Lord with a most ready and devout mind, to make the work of the tabernacle of the testimony. Whatsoever was necessary to the service, and to the holy vestments,
22 Duk waɗanda suke da niyya, maza da mata, gaba ɗaya, suka kawo kayan ado na zinariya na kowane iri.’Yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri-iri. Dukansu suka miƙa zinariyarsu a matsayin hadaya ga Ubangiji.
Both men and women gave bracelets and earrings, rings and tablets: every vessel of gold was set aside to be offered to the Lord.
23 Kowane mutumin da yake da shuɗi, shunayya ko jan zare, ko lallausan lilin, ko gashin akuya, ko fatun rago da aka rina ja, ko fatun shanun teku, suka kawo.
If any man had violet, and purple, and scarlet twice dyed, fine linen and goats’ hair, rams’ skins dyed red, and violet coloured skins,
24 Masu miƙa kyautar azurfa, ko tagulla suka kawo su a matsayin kyautai ga Ubangiji, kuma kowane mutumin da yake da itacen ƙirya don kowane sashin aikin, ya kawo.
Metal of silver and brass, they offered it to the Lord, and setim wood for divers uses.
25 Kowace mace mai fasaha ta kaɗa zare da hannuwanta, ta kuma kawo abin da ta kaɗa na shuɗi, shunayya, ko jan zare, ko lallausan lilin.
The skillful women also gave such things as they had spun, violet, purple, and scarlet, and fine linen,
26 Kuma dukan matan da suke da niyya, suke kuma da fasaha, suka kaɗa gashin akuya.
And goats’ hair, giving all of their own accord.
27 Shugabannin suka kawo duwatsun Onis. Da duwatsu masu daraja don a jera a kan efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
But the princes offered onyx stone, and precious stones, for the ephod and the rational,
28 Suka kawo kayan yaji da man zaitun don fitila da don man shafewa da kuma don turare mai ƙanshi.
And spices and oil for the lights, and for the preparing of ointment, and to make the incense of most sweet savour.
29 Dukan mazan Isra’ilawa da matan da suke da niyya suka kawo wa Ubangiji kyautai na yardar rai, domin dukan aikin da Ubangiji ya umarce su ta bakin Musa.
All both men and women with devout mind offered gifts, that the works might be done which the Lord had commanded by the hand of Moses. All the children of Israel dedicated voluntary offerings to the Lord.
30 Sa’an nan ya ce wa Isra’ilawa, “Duba Ubangiji ya zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, daga kabilar Yahuda,
And Moses said to the children of Israel: Behold the Lord hath called by name Beseleel the son of Uri the son of Hur of the tribe of Juda.
31 ya kuma cika shi da Ruhun Allah, da fasaha, azanci da kuma sani cikin dukan sana’ar hannu,
And hath filled him with the spirit of God, with wisdom and understanding and knowledge and all learning.
32 don yă ƙirƙiro zāne-zāne na gwaninta waɗanda za yi da zinariya, da azurfa da kuma tagulla.
To devise and to work in gold and silver and brass,
33 Haka kuma wajen sassaƙar duwatsu na jerawa, da sassaƙar itace, da kowane irin aiki na gwaninta.
And in engraving stones, and in carpenters’ work. Whatsoever can be devised artificially,
34 Ya kuma ba Bezalel da Oholiyab ɗan Ahisamak, daga kabilar Dan, iyawa don koya wa waɗansu.
He hath given in his heart: Ooliab also the son of Achisamech of the tribe of Dan:
35 Ya cika su da fasaha don yin kowane irin aikin sana’a, zāne-zāne, ɗinke-ɗinke shuɗi, shunayya da jan zare, da lallausan lilin, da kuma masu yin saƙa, sun gwaninta ƙwarai cikin kowane irin aikin hannu da kuma zāne-zāne.
Both of them hath he instructed with wisdom, to do carpenters’ work and tapestry, and embroidery in blue and purple, and scarlet twice dyed, and fine linen, and to weave all things, and to invent all new things.