< Fitowa 33 >

1 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka bar wannan wuri, kai da mutanen da ka fito da su daga Masar, ka haura zuwa ƙasar da na alkawarta da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da Yaƙub cewa, ‘Zan ba zuriyarka.’
וידבר יהוה אל משה לך עלה מזה--אתה והעם אשר העלית מארץ מצרים אל הארץ אשר נשבעתי לאברהם ליצחק וליעקב לאמר לזרעך אתננה
2 Zan aika da mala’ika a gabanka in kuma kori Kan’aniyawa, Amoriyawa, Hittiyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa.
ושלחתי לפניך מלאך וגרשתי את הכנעני האמרי והחתי והפרזי החוי והיבוסי
3 Ka haura zuwa ƙasar da take zub da madara da zuma. Amma ba zan tafi tare da ku ba, saboda ku mutane ne masu taurinkai domin mai yiwuwa in hallaka ku a hanya.”
אל ארץ זבת חלב ודבש כי לא אעלה בקרבך כי עם קשה ערף אתה--פן אכלך בדרך
4 Da mutane suka ji wannan mugun magana, sai suka fara makoki. Ba kuma wanda ya sa kayan ado.
וישמע העם את הדבר הרע הזה--ויתאבלו ולא שתו איש עדיו עליו
5 Gama Ubangiji ya riga ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ku mutane ne masu taurinkai. In na yi tafiya da ku ko na ɗan lokaci, mai yiwuwa in hallaka ku. Yanzu sai ku tuɓe kayan adonku, zan kuwa yanke shawara a kan abin da zan yi da ku.’”
ויאמר יהוה אל משה אמר אל בני ישראל אתם עם קשה ערף--רגע אחד אעלה בקרבך וכליתיך ועתה הורד עדיך מעליך ואדעה מה אעשה לך
6 Saboda haka Isra’ilawa suka tuttuɓe kayan adonsu a Dutsen Horeb.
ויתנצלו בני ישראל את עדים מהר חורב
7 Musa fa ya saba ɗaukan tenti yă kafa shi a bayan sansani da ɗan nisa, yana kiransa “Tentin Sujada.” Duk wanda yake neman wani abu daga wurin Ubangiji sai yă tafi Tentin Sujada a bayan sansani.
ומשה יקח את האהל ונטה לו מחוץ למחנה הרחק מן המחנה וקרא לו אהל מועד והיה כל מבקש יהוה יצא אל אהל מועד אשר מחוץ למחנה
8 A sa’ad da kuma Musa ya fita zuwa Tentin, dukan mutanen sukan tashi su tsaya a ƙofofin tentinsu, suna kallon Musa, sai ya shiga tentin.
והיה כצאת משה אל האהל יקומו כל העם ונצבו איש פתח אהלו והביטו אחרי משה עד באו האהלה
9 Yayinda Musa ya shiga cikin tentin, sai al’amudin girgije yă sauko, yă tsaya a ƙofar yayinda Ubangiji yana magana da Musa.
והיה כבא משה האהלה ירד עמוד הענן ועמד פתח האהל ודבר עם משה
10 Lokacin da mutane suka ga al’amudin girgije a tsaye a ƙofar tentin, sai duk su miƙe tsaye su yi sujada, kowa a ƙofar tentinsa.
וראה כל העם את עמוד הענן עמד פתח האהל וקם כל העם והשתחוו איש פתח אהלו
11 Ubangiji yakan yi magana da Musa fuska da fuska, kamar yadda mutum yake magana da abokinsa. Sa’an nan Musa yă koma sansani, amma saurayin nan Yoshuwa ɗan Nun mai taimakonsa ba ya barin tentin.
ודבר יהוה אל משה פנים אל פנים כאשר ידבר איש אל רעהו ושב אל המחנה ומשרתו יהושע בן נון נער לא ימיש מתוך האהל
12 Musa ya ce wa Ubangiji, “Kana ta faɗa mini cewa, ‘Ka jagoranci mutane nan,’ amma ba ka faɗa mini wanda zai tafi tare da ni ba. Ga shi ka ƙara ce mini, ‘Na san ka, na san sunanka, ka kuma sami tagomashi a wurina.’
ויאמר משה אל יהוה ראה אתה אמר אלי העל את העם הזה ואתה לא הודעתני את אשר תשלח עמי ואתה אמרת ידעתיך בשם וגם מצאת חן בעיני
13 In ka ji daɗina, ka koya mini hanyarka don in san ka, in kuma ci gaba da samun tagomashi daga gare ka. Ka tuna cewa wannan al’umma mutanenka ne.”
ועתה אם נא מצאתי חן בעיניך הודעני נא את דרכך ואדעך למען אמצא חן בעיניך וראה כי עמך הגוי הזה
14 Ubangiji ya amsa ya ce, “Zan tafi tare da kai, zan kuma rage maka nauyin kaya.”
ויאמר פני ילכו והנחתי לך
15 Musa kuwa ya ce masa, “In ba za tă tafi tare da mu ba, to, kada ka ɗaga mu daga nan.
ויאמר אליו אם אין פניך הלכים אל תעלנו מזה
16 Yaya wani zai sani ko ka ji daɗina da kuma mutanenka, in ba ka tafi tare da mu ba? Mene ne kuma zai bambanta ni da mutanenka daga sauran jama’ar da suke a duniya?”
ובמה יודע אפוא כי מצאתי חן בעיניך אני ועמך--הלוא בלכתך עמנו ונפלינו אני ועמך מכל העם אשר על פני האדמה
17 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan yi yadda ka faɗa, gama ka sami tagomashi a wurina, na san ka, na kuma san sunanka.”
ויאמר יהוה אל משה גם את הדבר הזה אשר דברת אעשה כי מצאת חן בעיני ואדעך בשם
18 Musa kuwa ya ce, “To, ka nuna mini ɗaukakarka.”
ויאמר הראני נא את כבדך
19 Sai Ubangiji ya ce, “Zan wuce a gabanka, Ni Ubangiji zan yi shelar sunana a gabanka. Zan yi alheri ga duk wanda na so in yi masa alheri, zan nuna jinƙai ga duk wanda na so in yi masa jinƙai.
ויאמר אני אעביר כל טובי על פניך וקראתי בשם יהוה לפניך וחנתי את אשר אחן ורחמתי את אשר ארחם
20 Amma ya ce, ba za ka ga fuskata ba, don ba mutumin da zai gan ni yă rayu.”
ויאמר לא תוכל לראת את פני כי לא יראני האדם וחי
21 Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ga wani wuri kusa da ni inda za ka tsaya bisa dutsen.
ויאמר יהוה הנה מקום אתי ונצבת על הצור
22 A sa’ad da ɗaukakata tana wucewa, zan sa ka a cikin tsaguwar dutsen, in rufe ka da hannuna har sai na wuce.
והיה בעבר כבדי ושמתיך בנקרת הצור ושכתי כפי עליך עד עברי
23 Sa’an nan zan ɗauke hannuna, ka kuwa ga bayana; amma fuskata, ba za ka gani ba.”
והסרתי את כפי וראית את אחרי ופני לא יראו

< Fitowa 33 >