< Fitowa 3 >
1 Ana nan wata rana Musa yana kiwon tumakin Yetro surukinsa, firist na Midiyan, sai ya bi da tumaki zuwa gefe mai nisa a cikin hamada, har ya zo Horeb, dutsen Allah.
2 A can mala’ikan Ubangiji ya bayyana a gare shi cikin harshen wuta, a ƙaramin itace. Musa ya lura cewa ko da yake wuta na ci ƙaramin itacen, amma bai ƙone ba.
3 Sai Musa ya ce, “Wannan abin mamaki ne, don me wannan itace bai ƙone ba? Bari in matso kusa in gani.”
4 Da Ubangiji ya ga Musa ya matso don yă duba, sai Allah ya yi kira daga cikin ƙaramin itacen ya ce, “Musa! Musa!” Sai Musa ya amsa ya ce, “Ga ni.”
5 Allah ya ce, “Kada ka zo kusa, tuɓe takalmanka, gama inda kake tsaye, wuri ne mai tsarki.”
6 Sai Allah ya ce, “Ni ne Allah na kakanninka, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub.” Da jin wannan, sai Musa ya ɓoye fuskarsa, domin ya ji tsoro yă dubi Allah.
7 Ubangiji ya ce, “Tabbatacce na ga azabar mutanena a Masar. Na ji su suna kuka saboda matsin da shugabannin gandunsu suke musu, na kuma damu da wahalarsu.
8 Saboda haka na sauko domin in cece su daga hannun Masarawa, in kuma fitar da su daga ƙasar Masar, in kai su ƙasa mai kyau mai fāɗi, ƙasa mai zub da madara da zuma, inda Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa suke.
9 Yanzu kukan Isra’ilawa ya kai gare ni, na kuma ga yadda Masarawa suke wulaƙanta su
10 To, fa, sai ka tafi. Ina aikan ka wurin Fir’auna don ka fitar da mutanena Isra’ilawa daga Masar.”
11 Amma Musa ya ce wa Allah, “Wane ni in tafi wurin Fir’auna, in kuma fitar da Isra’ilawa daga Masar?”
12 Sai Allah ya ce, “Zan kasance da tare kai. Wannan kuwa za tă zama alama a gare ka cewa Ni na aike ka. Bayan ka fitar da mutanen daga Masar, za ku yi sujada ga Allah a kan dutsen nan.”
13 Musa ya ce wa Allah, “A ce ma na tafi wurin Isra’ilawa na ce musu, ‘Allah na kakanninku ya aiko ni wurinku,’ in suka tambaye ni, ‘Mene ne sunansa?’ Me zan ce?”
14 Allah ya ce wa Musa, “NI NE wanda NINE. Abin da za ka faɗa wa Isra’ilawa ke nan cewa, ‘NI NE, ya aiko ni wurinku.’”
15 Allah ya kuma ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ubangiji, Allah na kakanninka, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub, ya aiko ni wurinku.’ Wannan shi ne sunana har abada, sunan da za a tuna da ni daga tsara zuwa tsara ke nan.
16 “Tafi ka tattara dattawan Isra’ila, ka ce musu, ‘Ubangiji, Allah na kakanninku, Allah na Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, ya bayyana a gare ni ya ce, Na lura da ku, na kuma ga abubuwan da ake yi muku a Masar.
17 Na kuma yi alkawari, zan fitar da ku daga azabarku a Masar zuwa ƙasar Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, ƙasa mai zub da madara da zuma.’
18 “Dattawan Isra’ila za su saurare ka. Sa’an nan da kai da dattawan Isra’ila, za ku tafi wurin sarkin Masar, ku ce masa, ‘Ubangiji, Allah na Ibraniyawa, ya sadu da mu. Bari mu yi tafiyar kwana uku zuwa cikin hamada domin mu yi hadaya wa Ubangiji Allahnmu.’
19 Amma na san cewa sarkin Masar ba zai yarda ku tafi ba, sai hannu mai ƙarfi ya tilasta shi.
20 Saboda haka zan miƙa hannuna in bugi Masarawa da duk al’ajaban da zan aikata a cikinsu. Bayan haka zai bar ku, ku tafi.
21 “Zan kuma sa mutanen su sami tagomashi daga wurin Masarawa, saboda sa’ad da za ku fita, ba za ku fita hannu wofi ba.
22 Kowace mace ta tambayi maƙwabciyarta, da kuma duk wata macen da take cikin gidanta, kayayyakin azurfa da na zinariya da kuma na riguna, waɗanda za ku sa wa’ya’yanku maza da mata. Ta haka nan za ku washe Masarawa.”