< Fitowa 25 >
1 Ubangiji ya ce wa Musa,
locutusque est Dominus ad Mosen dicens
2 “Ka faɗa wa Isra’ilawa su kawo mini hadaya. Za ka karɓi hadaya daga hannun kowane mutum wanda zuciyarsa ta yarda yă bayar.
loquere filiis Israhel ut tollant mihi primitias ab omni homine qui offert ultroneus accipietis eas
3 “Ga iri jerin kayan da za ka karɓo daga hannunsu, “zinariya, da azurfa, tagulla,
haec sunt autem quae accipere debetis aurum et argentum et aes
4 shuɗi, shunayya da jan zare, lallausan lilin, da gashin akuya,
hyacinthum et purpuram coccumque bis tinctum et byssum pilos caprarum
5 fatun ragunan da aka wanke, fatun awaki masu kyau, itacen akashiya,
et pelles arietum rubricatas pelles ianthinas et ligna setthim
6 mai domin fitila, kayan yaji domin man keɓewa da kuma turare mai ƙanshi,
oleum ad luminaria concinnanda aromata in unguentum et thymiama boni odoris
7 da duwatsun Onis, da duwatsun da za a mammanne a efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
lapides onychinos et gemmas ad ornandum ephod ac rationale
8 “Sa’an nan ka sa su yi mini wuri mai tsarki, domin in zauna a cikinsu.
facientque mihi sanctuarium et habitabo in medio eorum
9 Ka ƙera wannan tabanakul da duk kayan da suke ciki da waje, daidai yadda zan nuna maka.
iuxta omnem similitudinem tabernaculi quod ostendam tibi et omnium vasorum in cultum eius sicque facietis illud
10 “Ka sa a yi akwatin alkawarin da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi.
arcam de lignis setthim conpingite cuius longitudo habeat duos semis cubitos latitudo cubitum et dimidium altitudo cubitum similiter ac semissem
11 Ka dalaye shi da zinariya zalla ciki da waje, za ka yi wa gefe-gefensa ado da gurun zinariya.
et deaurabis eam auro mundissimo intus et foris faciesque supra coronam auream per circuitum
12 Ka kewaye akwatin da zoban zinariya huɗu ka kuma haɗa su da ƙafafunsa huɗu, zobai biyu a kowane gefe.
et quattuor circulos aureos quos pones per quattuor arcae angulos duo circuli sint in latere uno et duo in altero
13 Sa’an nan ka yi sanduna da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya.
facies quoque vectes de lignis setthim et operies eos auro
14 Ka sa sandunan a cikin zoban, a gefen akwatin domin ɗaukansa.
inducesque per circulos qui sunt in arcae lateribus ut portetur in eis
15 Sanduna za su kasance a cikin waɗannan zoban akwatin alkawarin; ba za a cire su ba.
qui semper erunt in circulis nec umquam extrahentur ab eis
16 Sa’an nan ka sa Shaidar da zan ba ka, a cikin akwatin.
ponesque in arcam testificationem quam dabo tibi
17 “Ka yi murfin kafara da zinariya zalla, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi.
facies et propitiatorium de auro mundissimo duos cubitos et dimidium tenebit longitudo eius cubitum ac semissem latitudo
18 Ka kuma yi kerubobi biyu da zinariyar da aka ƙera, ka sa a gefen nan biyu na murfin.
duos quoque cherubin aureos et productiles facies ex utraque parte oraculi
19 Ka yi kerubobi biyu, ɗaya a wannan gefe, ɗaya kuma a ɗayan gefen; za ka manne su a kan murfin, su zama abu ɗaya.
cherub unus sit in latere uno et alter in altero
20 Kerubobin su kasance da fikafikansu a buɗe, domin su inuwantar da murfin, za su fuskanci juna, suna duba murfin.
utrumque latus propitiatorii tegant expandentes alas et operientes oraculum respiciantque se mutuo versis vultibus in propitiatorium quo operienda est arca
21 Ka sa murfin a bisa akwatin ka kuma sa allunan dokokin alkawarin da zan ba ka a ciki.
in qua pones testimonium quod dabo tibi
22 Can, a bisa murfin da yake tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari na Shaida, zan sadu da kai, in kuma ba ka dukan umarnai domin Isra’ilawa.
inde praecipiam et loquar ad te supra propitiatorio scilicet ac medio duorum cherubin qui erunt super arcam testimonii cuncta quae mandabo per te filiis Israhel
23 “Ka yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi.
facies et mensam de lignis setthim habentem duos cubitos longitudinis et in latitudine cubitum et in altitudine cubitum ac semissem
24 Ka dalaye shi da zinariya zalla ka kuma yi masa ado kewaye da gurun zinariya.
et inaurabis eam auro purissimo faciesque illi labium aureum per circuitum
25 Ka yi dajiya mai fāɗin tafin hannu, ka kuma yi wa dajiyar ado da gurun zinariya.
et ipsi labio coronam interrasilem altam quattuor digitis et super illam alteram coronam aureolam
26 Ka yi zoban zinariya huɗu domin teburin, ka daure su a kusurwoyi huɗu, inda ƙafafu huɗun suke.
quattuor quoque circulos aureos praeparabis et pones eos in quattuor angulis eiusdem mensae per singulos pedes
27 Zoban za su kasance kusa da dajiyar don riƙe sandunan da za a yi amfani don ɗaukar teburin.
subter coronam erunt circuli aurei ut mittantur vectes per eos et possit mensa portari
28 Ka yi sandunan da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya, da sandunan ne za ku riƙa ɗaukan teburin.
ipsosque vectes facies de lignis setthim et circumdabis auro ad subvehendam mensam
29 Da zinariya zalla kuma za ka yi farantansa, da kwanoninsa na tuya, da butocinsa, da kwanoninsa domin zuban hadayu.
parabis et acetabula ac fialas turibula et cyatos in quibus offerenda sunt libamina ex auro purissimo
30 Ka sa burodin Kasancewa a kan wannan tebur, yă kasance a gabana kullum.
et pones super mensam panes propositionis in conspectu meo semper
31 “Ka yi wurin ajiye fitilar da zinariya zalla, ka kuma yi gindinsa tare da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya; kwafunansa da suka yi kamar furanni, tohonsa da furanninsa su yi yadda za su zama ɗaya da shi.
facies et candelabrum ductile de auro mundissimo hastile eius et calamos scyphos et spherulas ac lilia ex ipso procedentia
32 Wurin ajiye fitilar yă kasance da rassa shida, rassan nan za su miƙe daga kowane gefe na wurin ajiye fitilan, uku a gefe guda, uku kuma a ɗaya gefen.
sex calami egredientur de lateribus tres ex uno latere et tres ex altero
33 Kwafuna uku masu siffar furanni almon, da toho, da kuma furannin za su kasance a rashe guda, uku a kan rashe na biye, haka kuma a kan saura rassan shida da suka miƙe daga wurin ajiye fitilan.
tres scyphi quasi in nucis modum per calamos singulos spherulaque simul et lilium et tres similiter scyphi instar nucis in calamo altero spherulaque et lilium hoc erit opus sex calamorum qui producendi sunt de hastili
34 A bisa wurin ajiye fitilan kuwa za a kasance da kwafuna huɗu masu siffar furannin almon, da toho, da furanni.
in ipso autem candelabro erunt quattuor scyphi in nucis modum spherulaeque per singulos et lilia
35 Toho ɗaya zai kasance a ƙarƙashin rassa biyu na farkon da suka miƙe daga wurin ajiye fitilan, toho na biyu a ƙarƙashin rassa biyu na biye, toho na uku a ƙarƙashin rassa na uku, rassa shida ke nan duka.
spherula sub duobus calamis per tria loca qui simul sex fiunt procedentes de hastili uno
36 Tohon da kuma rassan za su kasance ɗaya da wurin ajiye fitilan da aka yi da ƙerarriyar zinariya.
et spherae igitur et calami ex ipso erunt universa ductilia de auro purissimo
37 “Sa’an nan ka yi fitilu bakwai, ka sa su a bisa wurin ajiye fitilan ta yadda za su haskaka wajen da suka fuskanta.
facies et lucernas septem et pones eas super candelabrum ut luceant ex adverso
38 Za a yi lagwaninsa da manyan farantansa da ƙerarriyar zinariya.
emunctoria quoque et ubi quae emuncta sunt extinguantur fient de auro purissimo
39 Da zinariya zalla na talenti ɗaya za ka yi wurin ajiye fitilan da waɗannan abubuwa duka.
omne pondus candelabri cum universis vasis suis habebit talentum auri mundissimi
40 Sai ka lura ka yi su daidai bisa ga fasalin da aka nuna maka a kan dutse.
inspice et fac secundum exemplar quod tibi in monte monstratum est