< Fitowa 23 >

1 “Kada ku baza rahoton ƙarya. Kada kuma ku haɗa baki da mugayen mutane har da ku zama munafukai ta wurin ba da shaidar ƙarya.
לא תשא שמע שוא אל תשת ידך עם רשע להית עד חמס׃
2 “Kada ku yi abin da ba daidai ba, don galibin mutane suna yin haka. Sa’ad da kuke ba da shaida a gaban shari’a, kada ku ba da shaidar ƙarya a kauce wa gaskiya don ku faranta wa taron jama’a rai.
לא תהיה אחרי רבים לרעת ולא תענה על רב לנטת אחרי רבים להטת׃
3 Kada ku yi wa matalauci sonkai a gaban shari’a.
ודל לא תהדר בריבו׃
4 “In ka ga saniyar abokin gābanka, ko jakinsa ya ɓace, ka yi ƙoƙari ka mai da shi wurinsa.
כי תפגע שור איבך או חמרו תעה השב תשיבנו לו׃
5 In ka ga jakin wani maƙiyinka ya fāɗi a ƙarƙashin kayan da ya ɗauka, kada ka bar shi can, ka yi ƙoƙari ka taimake shi.
כי תראה חמור שנאך רבץ תחת משאו וחדלת מעזב לו עזב תעזב עמו׃
6 “Kada ku kāsa yin adalci ga matalauci a wurin shari’a.
לא תטה משפט אבינך בריבו׃
7 Ku yi nesa da ƙage. Kada ku kashe marar laifi tare da mai adalci, gama ba zan bar mugun yă tafi haka kawai ba.
מדבר שקר תרחק ונקי וצדיק אל תהרג כי לא אצדיק רשע׃
8 “Kada ka karɓi cin hanci, gama cin hanci yakan makanta waɗanda suke gani, yakan kuma karkatar da maganar masu adalci.
ושחד לא תקח כי השחד יעור פקחים ויסלף דברי צדיקים׃
9 “Kada ka zalunci baƙo, ku kanku kun san halin baƙunci, gama dā ku baƙi ne a Masar.
וגר לא תלחץ ואתם ידעתם את נפש הגר כי גרים הייתם בארץ מצרים׃
10 “Shekara shida za ku nome gonakinku ku girbe amfanin gonar,
ושש שנים תזרע את ארצך ואספת את תבואתה׃
11 amma a shekara ta bakwai za ku bar ƙasa tă huta. Sa’an nan matalautan da suke cikinku za su sami abinci daga cikinta, namun jeji kuma za su ci abin da aka bari. Ku yi haka da gonakinku na inabi, da na itatuwan zaitun.
והשביעת תשמטנה ונטשתה ואכלו אביני עמך ויתרם תאכל חית השדה כן תעשה לכרמך לזיתך׃
12 “Kwana shida za ku yi aikinku, amma a rana ta bakwai, kada ku yi aiki, saboda saniyarku da jakinku su huta, haka kuma bawan da aka haifa a gidanku, da kuma baƙon da yake a cikinku yă wartsake.
ששת ימים תעשה מעשיך וביום השביעי תשבת למען ינוח שורך וחמרך וינפש בן אמתך והגר׃
13 “Ku mai da hankali, ku yi biyayya da duk abin da na faɗa muku. Kada ku kira sunaye waɗansu alloli; kada a ji su a bakinku.
ובכל אשר אמרתי אליכם תשמרו ושם אלהים אחרים לא תזכירו לא ישמע על פיך׃
14 “Sau uku a shekara za ku yi mini biki.
שלש רגלים תחג לי בשנה׃
15 “Ku yi Bikin Burodi Marar Yisti, kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti, kamar yadda na umarce ku. Ku yi wannan a lokacin da aka ayana a watan Abib, gama a watan ne kuka fito daga Masar. “Kada wani yă zo a gabana hannu wofi.
את חג המצות תשמר שבעת ימים תאכל מצות כאשר צויתך למועד חדש האביב כי בו יצאת ממצרים ולא יראו פני ריקם׃
16 “Ku yi Bikin Girbi da nunan fari na amfanin shuke-shuken gonarku. “Ku yi Bikin Tattarawa a ƙarshen shekara, sa’ad da kuka tattara amfani daga gonarku.
וחג הקציר בכורי מעשיך אשר תזרע בשדה וחג האסף בצאת השנה באספך את מעשיך מן השדה׃
17 “Sau uku a shekara, maza duka za su bayyana a gaban Ubangiji Mai Iko Duka.
שלש פעמים בשנה יראה כל זכורך אל פני האדן יהוה׃
18 “Kada ku miƙa mini hadayar jini tare da wani abu mai yisti. “Ba za a bar kitsen bikin hadayata yă kwana ba.
לא תזבח על חמץ דם זבחי ולא ילין חלב חגי עד בקר׃
19 “Dole ne ku kawo mafi kyau daga nunan fari na gonakinku a gidan Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madarar mahaifiyarsa.
ראשית בכורי אדמתך תביא בית יהוה אלהיך לא תבשל גדי בחלב אמו׃
20 “Ga shi, zan aika mala’ika a gabanku, yă tsare ku a tafiyarku, yă kuma kawo ku wurin da na shirya.
הנה אנכי שלח מלאך לפניך לשמרך בדרך ולהביאך אל המקום אשר הכנתי׃
21 Ku saurare shi, ku kuma kasa kunne ga abin da yake faɗa. Kada ku yi masa tawaye; ba zai gafarta tawayenku ba, gama shi wakilina ne.
השמר מפניו ושמע בקלו אל תמר בו כי לא ישא לפשעכם כי שמי בקרבו׃
22 In kun kasa kunne sosai ga abin da yake faɗi, kuka kuma yi abin da na faɗa, zan zama magabci ga abokan gābanku, zan kuma yi hamayya da abokan hamayyanku.
כי אם שמע תשמע בקלו ועשית כל אשר אדבר ואיבתי את איביך וצרתי את צרריך׃
23 Mala’ikana zai sha gabanku, yă kawo ku cikin ƙasar Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Kan’aniyawa, da Hiwiyawa, da kuma Yebusiyawa, zan kuma kawar da su.
כי ילך מלאכי לפניך והביאך אל האמרי והחתי והפרזי והכנעני החוי והיבוסי והכחדתיו׃
24 Kada ku durƙusa wa allolinsu, ko ku yi musu sujada, ko kuma ku bi al’adunsu. Za ku hallaka dukan allolinsu, ku kuma farfasa keɓaɓɓun duwatsunsu.
לא תשתחוה לאלהיהם ולא תעבדם ולא תעשה כמעשיהם כי הרס תהרסם ושבר תשבר מצבתיהם׃
25 Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, albarkansa kuwa za tă kasance a kan abincinku da ruwan shanku. Zan ɗauke cuta daga cikinku.
ועבדתם את יהוה אלהיכם וברך את לחמך ואת מימיך והסרתי מחלה מקרבך׃
26 A ƙasarku, mace ba za tă yi ɓari ba, ba kuma za a sami marar haihuwa ba. Zan ba ku tsawon rai.
לא תהיה משכלה ועקרה בארצך את מספר ימיך אמלא׃
27 “Zan aiki razanata a gabanku, in kuma sa ruɗami a cikin kowace al’ummar da za ku sadu da ita. Zan sa duk abokan gābanku su juye da baya, su gudu.
את אימתי אשלח לפניך והמתי את כל העם אשר תבא בהם ונתתי את כל איביך אליך ערף׃
28 Zan aiki rina a gabanku, su kori Hiwiyawa, Kan’aniyawa da kuma Hittiyawa.
ושלחתי את הצרעה לפניך וגרשה את החוי את הכנעני ואת החתי מלפניך׃
29 Amma ba a shekara guda zan kore muku su ba, don kada ƙasar tă zama kufai har namun jeji su fi ƙarfinku.
לא אגרשנו מפניך בשנה אחת פן תהיה הארץ שממה ורבה עליך חית השדה׃
30 Da kaɗan da kaɗan zan kore muku su, har yawanku yă kai yadda za ku mallaki ƙasar.
מעט מעט אגרשנו מפניך עד אשר תפרה ונחלת את הארץ׃
31 “Zan kafa iyakokinku daga Jan Teku zuwa Bahar Rum, daga hamada kuma zuwa Kogi. Zan ba da mazaunan ƙasar a hannunku, za ku kuwa kore su daga gabanku.
ושתי את גבלך מים סוף ועד ים פלשתים וממדבר עד הנהר כי אתן בידכם את ישבי הארץ וגרשתמו מפניך׃
32 Kada ku ƙulla yarjejjeniya da su, ko da allolinsu.
לא תכרת להם ולאלהיהם ברית׃
33 Kada ku bari su zauna a cikin ƙasarku, in har kuka bar su, za su ɓata ku da zunubinsu na bautar allolinsu, har zai yă zama muku tarko.”
לא ישבו בארצך פן יחטיאו אתך לי כי תעבד את אלהיהם כי יהיה לך למוקש׃

< Fitowa 23 >