< Fitowa 16 >

1 Dukan taron Isra’ila suka tashi daga Elim suka zo hamadar Sin, wadda take tsakanin Elim da Sinai, a rana ta goma sha biyar ga wata biyu, bayan sun fito daga Masar.
ויסעו מאילם ויבאו כל עדת בני ישראל אל מדבר סין אשר בין אילם ובין סיני--בחמשה עשר יום לחדש השני לצאתם מארץ מצרים
2 A hamadan, dukan taro suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna.
וילינו (וילונו) כל עדת בני ישראל על משה ועל אהרן--במדבר
3 Isra’ilawa suka ce musu, “Da ma a hannun Ubangiji ne muka mutu a Masar, inda muka zauna kewaye da tukwanen nama, muna cin duk abincin da muke so, amma kun kawo mu cikin wannan hamada don ku kashe dukan wannan taro da yunwa.”
ויאמרו אלהם בני ישראל מי יתן מותנו ביד יהוה בארץ מצרים בשבתנו על סיר הבשר באכלנו לחם לשבע כי הוצאתם אתנו אל המדבר הזה להמית את כל הקהל הזה ברעב
4 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan zubo muku burodi kamar ruwa daga sama. Mutanen za su fita kowace rana su tattara abin da zai ishe su na ranan. Ta haka zan gwada su in ga ko za su bi umarnaina.
ויאמר יהוה אל משה הנני ממטיר לכם לחם מן השמים ויצא העם ולקטו דבר יום ביומו למען אנסנו הילך בתורתי אם לא
5 A rana ta shida za su shirya abin da suka kwaso, wannan kuwa zai zama ninki biyu na abin da sukan tattara na sauran ranaku.”
והיה ביום הששי והכינו את אשר יביאו והיה משנה על אשר ילקטו יום יום
6 Saboda haka Musa da Haruna suka ce wa dukan Isra’ila, “Da yamma za ku sani Ubangiji ne ya fitar da ku daga Masar.
ויאמר משה ואהרן אל כל בני ישראל ערב--וידעתם כי יהוה הוציא אתכם מארץ מצרים
7 Da safe za ku ga ɗaukakar Ubangiji, saboda ya ji gunaguninku a kansa. Wane mu, da za ku yi gunaguni a kanmu?”
ובקר וראיתם את כבוד יהוה בשמעו את תלנתיכם על יהוה ונחנו מה כי תלונו (תלינו) עלינו
8 Musa ya kuma ce, “Za ku san cewa shi ne Ubangiji, sa’ad da ya ba ku nama ku ci da yamma, da kuma duk burodin da kuke so da safe, saboda ya ji gunagunin da kuka yi a kansa. Namu a wane? Ai, gunaguninku ba a kanmu ba, amma a kan Ubangiji ne.”
ויאמר משה בתת יהוה לכם בערב בשר לאכל ולחם בבקר לשבע בשמע יהוה את תלנתיכם אשר אתם מלינם עליו ונחנו מה לא עלינו תלנתיכם כי על יהוה
9 Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ka faɗa wa dukan taron Isra’ila, ‘Ku zo gaban Ubangiji, gama ya ji gunaguninku.’”
ויאמר משה אל אהרן אמר אל כל עדת בני ישראל קרבו לפני יהוה כי שמע את תלנתיכם
10 Yayinda Haruna yake magana da dukan taron Isra’ila, sai suka duba wajen hamada, sai ga ɗaukakar Ubangiji tana bayyana a girgije.
ויהי כדבר אהרן אל כל עדת בני ישראל ויפנו אל המדבר והנה כבוד יהוה נראה בענן
11 Ubangiji ya ce wa Musa,
וידבר יהוה אל משה לאמר
12 “Na ji gunagunin Isra’ilawa. Ka faɗa musu, ‘A tsakanin fāɗuwar rana da almuru, za ku ci nama, da safe kuma za ku ƙoshi da burodi. Sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku.’”
שמעתי את תלונת בני ישראל--דבר אלהם לאמר בין הערבים תאכלו בשר ובבקר תשבעו לחם וידעתם כי אני יהוה אלהיכם
13 Da yamman wannan rana, sai makware suka rufe dukan sansani, da safe kuma sai ga raɓa ta kewaye sansani.
ויהי בערב--ותעל השלו ותכס את המחנה ובבקר היתה שכבת הטל סביב למחנה
14 Lokacin da raɓar ta watse, sai ga wani abu kamar tsaki, falle-falle kuma da laushi, fari, kamar hazo, a ƙasa.
ותעל שכבת הטל והנה על פני המדבר דק מחספס--דק ככפר על הארץ
15 Sa’ad da Isra’ilawa suka ga wannan, sai suka ce wa junansu, “Mene ne wannan?” Gama ba su san ko mene ne ba. Musa ya ce musu, “Wannan shi ne burodin da Ubangiji ya ba ku ku ci.
ויראו בני ישראל ויאמרו איש אל אחיו מן הוא--כי לא ידעו מה הוא ויאמר משה אלהם הוא הלחם אשר נתן יהוה לכם לאכלה
16 Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta, ‘Kowane mutum zai tattara bisa ga bukatarsa. Ku tara rabin gallon don mutum guda da yake cikin tentinku.’”
זה הדבר אשר צוה יהוה לקטו ממנו איש לפי אכלו עמר לגלגלת מספר נפשתיכם--איש לאשר באהלו תקחו
17 Isra’ilawa suka yi kamar yadda aka faɗa musu, waɗansu suka tattara da yawa, waɗansu kuma kaɗan.
ויעשו כן בני ישראל וילקטו המרבה והממעיט
18 Da suka gwada a mudu, wanda ya tattara da yawa bai sami mafi yawa ba, wanda kuma ya tattara kaɗan bai sami ƙanƙani ba. Kowane mutum ya tattara daidai bukatarsa.
וימדו בעמר--ולא העדיף המרבה והממעיט לא החסיר איש לפי אכלו לקטו
19 Sa’an nan Musa ya ce musu, “Kada wani yă bar saura har safe.”
ויאמר משה אלהם איש אל יותר ממנו עד בקר
20 Duk da haka waɗansu ba su kula da umarnin Musa ba, suka bar saura har safe, kashegari kuwa ta yi tsutsotsi, ta ruɓe, sai Musa ya yi fushi da su.
ולא שמעו אל משה ויותרו אנשים ממנו עד בקר וירם תולעים ויבאש ויקצף עלהם משה
21 Kowace safiya, kowanne mutum yakan tattara daidai bukatarsa, lokacin da rana ta yi zafi, sai ta narke.
וילקטו אתו בבקר בבקר איש כפי אכלו וחם השמש ונמס
22 A rana ta shida, suka tattara ninki biyu, mudu biyu ga mutum guda, sai shugabannin taron suka zo suka kawo ƙara wurin Musa.
ויהי ביום הששי לקטו לחם משנה--שני העמר לאחד ויבאו כל נשיאי העדה ויגידו למשה
23 Shi kuma ya ce musu, “Wannan shi ne umarnin Ubangiji, ‘Gobe za tă zama ranar hutu, Asabbaci mai tsarki ga Ubangiji. Domin haka sai ku toya abin da kuke so ku toya, ku kuma dafa abin da kuke so ku dafa. Abin da ya rage ku ajiye har safe.’”
ויאמר אלהם הוא אשר דבר יהוה--שבתון שבת קדש ליהוה מחר את אשר תאפו אפו ואת אשר תבשלו בשלו ואת כל העדף הניחו לכם למשמרת עד הבקר
24 Sai suka bar saura har safe, kamar yadda Musa ya umarta, bai kuwa yi wari ko yă yi tsutsa ba.
ויניחו אתו עד הבקר כאשר צוה משה ולא הבאיש ורמה לא היתה בו
25 Musa ya ce, “Ku ci shi yau, saboda yau Asabbaci ne na Ubangiji. Ba za ku same shi a ƙasa a yau ba.
ויאמר משה אכלהו היום כי שבת היום ליהוה היום לא תמצאהו בשדה
26 Kwana shida za ku tattara shi, amma a rana ta bakwai, Asabbaci, ba za a same shi ba.”
ששת ימים תלקטהו וביום השביעי שבת לא יהיה בו
27 Duk da haka waɗansu mutane suka fita a ranar Asabbaci don su tattara, amma ba su sami kome ba.
ויהי ביום השביעי יצאו מן העם ללקט ולא מצאו
28 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe za ku ƙi bin dokokina da umarnaina?
ויאמר יהוה אל משה עד אנה מאנתם לשמר מצותי ותורתי
29 Ku lura fa, ai, Ubangiji ne ya ba ku Asabbaci; shi ya sa a kan ba ku burodi na kwana biyu, a rana ta shida. Kowa ya kamata yă kasance inda yake a rana ta bakwai; kada kowa yă fita.”
ראו כי יהוה נתן לכם השבת--על כן הוא נתן לכם ביום הששי לחם יומים שבו איש תחתיו אל יצא איש ממקמו--ביום השביעי
30 Sai mutanen suka huta a rana ta bakwai.
וישבתו העם ביום השבעי
31 Mutanen Isra’ila suka kira burodin Manna. Manna yana nan fari kamar farin riɗi, ɗanɗanonsa kuma yana kama da masa da aka yi da zuma.
ויקראו בית ישראל את שמו מן והוא כזרע גד לבן וטעמו כצפיחת בדבש
32 Musa ya ce, “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta, ‘Ku auna mudu guda na Manna, a adana ta dukan zamananku, domin kowane zamani yă ga irin abincin da na ba ku ku ci a hamada, yayinda na fitar da ku daga Masar.’”
ויאמר משה זה הדבר אשר צוה יהוה--מלא העמר ממנו למשמרת לדרתיכם למען יראו את הלחם אשר האכלתי אתכם במדבר בהוציאי אתכם מארץ מצרים
33 Saboda haka Musa ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki tulu, ka sa mudu guda na Manna a ciki. Sa’an nan ka sa shi a gaban Ubangiji, don a adana don tsararraki masu zuwa.”
ויאמר משה אל אהרן קח צנצנת אחת ותן שמה מלא העמר מן והנח אתו לפני יהוה למשמרת לדרתיכם
34 Sai Haruna ya ajiye Mannar a gaban Akwatin Alkawari, don a adana ta kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
כאשר צוה יהוה אל משה ויניחהו אהרן לפני העדת למשמרת
35 Isra’ilawa suka yi shekaru arba’in suna cin Manna, har sai da suka shiga cikin ƙasar da take da mutane, suka ci Manna har zuwa kan iyakar ƙasar Kan’ana.
ובני ישראל אכלו את המן ארבעים שנה--עד באם אל ארץ נושבת את המן אכלו--עד באם אל קצה ארץ כנען
36 (Omer guda, daidai ne da kashi ɗaya bisa goma na Efa.)
והעמר עשרית האיפה הוא

< Fitowa 16 >