< Fitowa 13 >

1 Ubangiji ya ce wa Musa,
וידבר יהוה אל משה לאמר
2 “Keɓe mini kowane ɗan fari. Ɗan fari wanda ya fara buɗe mahaifa a cikin Isra’ilawa nawa ne, ko na mutum ko na dabba.”
קדש לי כל בכור פטר כל רחם בבני ישראל--באדם ובבהמה לי הוא
3 Sai Musa ya ce wa mutane, “Ku tuna da wannan rana, ranar da kuka fito daga Masar, daga ƙasar bauta, gama Ubangiji ya fito da ku da hannu mai iko. Kada ku ci wani abin da yake da yisti.
ויאמר משה אל העם זכור את היום הזה אשר יצאתם ממצרים מבית עבדים כי בחזק יד הוציא יהוה אתכם מזה ולא יאכל חמץ
4 A wannan rana kuka fita, wato, a watan Abib.
היום אתם יצאים בחדש האביב
5 Sa’ad da Ubangiji ya kawo ku cikin ƙasar Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, ƙasar da ya rantse wa kakanninku cewa zai ba ku, ƙasar da take zub da madara da zuma, za ku kiyaye wannan biki a wannan wata.
והיה כי יביאך יהוה אל ארץ הכנעני והחתי והאמרי והחוי והיבוסי אשר נשבע לאבתיך לתת לך ארץ זבת חלב ודבש ועבדת את העבדה הזאת בחדש הזה
6 Kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti, a kan rana ta bakwai kuma za ku yi biki ga Ubangiji.
שבעת ימים תאכל מצת וביום השביעי חג ליהוה
7 Ku ci burodi marar yisti cikin kwana bakwai; kada a sami wani abu mai yisti a cikinku, ko a sami yisti a ko’ina a wurinku.
מצות יאכל את שבעת הימים ולא יראה לך חמץ ולא יראה לך שאר--בכל גבלך
8 A ranan nan kowa zai faɗa wa ɗanka, ‘Ina yin haka saboda abin da Ubangiji ya yi mini, sa’ad da na fita daga Masar.’
והגדת לבנך ביום ההוא לאמר בעבור זה עשה יהוה לי בצאתי ממצרים
9 Wannan abin tunawa zai zama muku alama a hannunku, da kuma a goshinku cewa dokar Ubangiji tana a bakinku. Gama Ubangiji ya fitar da ku daga Masar da hannu mai iko.
והיה לך לאות על ידך ולזכרון בין עיניך למען תהיה תורת יהוה בפיך כי ביד חזקה הוצאך יהוה ממצרים
10 Dole ku kiyaye wannan farilla kowace shekara a lokacinta.
ושמרת את החקה הזאת למועדה מימים ימימה
11 “Bayan Ubangiji ya kawo ku cikin ƙasar Kan’aniyawa, ya kuma ba da ita yadda ya alkawarta muku da rantsuwa, ku da kakanninku,
והיה כי יבאך יהוה אל ארץ הכנעני כאשר נשבע לך ולאבתיך ונתנה לך
12 sai ku miƙa kowane ɗan fari ga Ubangiji. Duk ɗan farin dabbobinku na Ubangiji ne.
והעברת כל פטר רחם ליהוה וכל פטר שגר בהמה אשר יהיה לך הזכרים--ליהוה
13 Amma a fanshi kowane ɗan farin jakinku da ɗan rago. In kuwa ba za ku fanshe shi ba, sai ku karye wuyansa. Sai ku fanshe kowane ɗan farin daga cikin’ya’yanku.
וכל פטר חמר תפדה בשה ואם לא תפדה וערפתו וכל בכור אדם בבניך תפדה
14 “A kwanaki masu zuwa, in ɗanka ya tambaye ka, ‘Mene ne manufar wannan?’ Ka faɗa masa cewa, ‘Da hannu mai iko Ubangiji ya fito da mu daga Masar, daga ƙasar bauta.
והיה כי ישאלך בנך מחר--לאמר מה זאת ואמרת אליו--בחזק יד הוציאנו יהוה ממצרים מבית עבדים
15 Sa’ad da Fir’auna ya taurare zuciyarsa, bai yarda ya sallame mu ba, sai Ubangiji ya kashe dukan’ya’yan farin ƙasar Masar, na mutum da na dabba, gaba ɗaya. Domin haka nake yin hadaya ga Ubangiji da’ya’yan fari, maza, da suka fara buɗe mahaifa, amma nakan fanshi dukan’ya’yan farina maza.’
ויהי כי הקשה פרעה לשלחנו ויהרג יהוה כל בכור בארץ מצרים מבכר אדם ועד בכור בהמה על כן אני זבח ליהוה כל פטר רחם הזכרים וכל בכור בני אפדה
16 Za tă kuma zama alama a hannunku da kuma shaida a goshinku cewa Ubangiji ya fito da mu daga Masar da hannunsa mai iko.”
והיה לאות על ידכה ולטוטפת בין עיניך כי בחזק יד הוציאנו יהוה ממצרים
17 Sa’ad da Fir’auna ya bar mutane su tafi, Allah bai bi da su a hanyar da ta bi ta iyakar Filistiyawa ba, ko da yake wannan hanya ce ta fi kusa. Gama Allah ya ce, “In suka fuskanci yaƙi, wataƙila su canja ra’ayinsu su koma Masar.”
ויהי בשלח פרעה את העם ולא נחם אלהים דרך ארץ פלשתים כי קרוב הוא כי אמר אלהים פן ינחם העם בראתם מלחמה--ושבו מצרימה
18 Saboda haka Allah ya kewaye da mutanen ta hamada zuwa Jan Teku. Isra’ilawa kuwa suka fita daga Masar da shirin yaƙi.
ויסב אלהים את העם דרך המדבר ים סוף וחמשים עלו בני ישראל מארץ מצרים
19 Musa ya ɗauki ƙasusuwan Yusuf tare da shi, gama Yusuf ya sa Isra’ilawa su rantse masa. Ya ce, “Tabbatacce Allah zai taimake ku, sai ku ɗibi ƙasusuwana tare da ku daga wannan wuri.”
ויקח משה את עצמות יוסף עמו כי השבע השביע את בני ישראל לאמר פקד יפקד אלהים אתכם והעליתם את עצמתי מזה אתכם
20 Bayan sun bar Sukkot sai suka kafa sansani a Etam a bakin hamada.
ויסעו מסכת ויחנו באתם בקצה המדבר
21 Da rana Ubangiji yakan ja gabansu a cikin al’amudin girgije domin yă bishe su a kan hanyarsu, da dare kuma a cikin al’amudin wuta domin yă ba su haske, domin su iya tafiya dare da rana.
ויהוה הלך לפניהם יומם בעמוד ענן לנחתם הדרך ולילה בעמוד אש להאיר להם--ללכת יומם ולילה
22 Al’amudan nan biyu, na girgije da na wuta, ba su daina yi wa jama’a jagora ba.
לא ימיש עמוד הענן יומם ועמוד האש לילה--לפני העם

< Fitowa 13 >