< Esta 9 >

1 A rana ta goma sha uku na watan goma sha biyu, wato, watan Adar ne za a aiwatar da dokar da sarki ya umarta. A wannan rana, abokan gāban Yahudawa suka sa zuciya za su sha ƙarfinsu, amma yanzu Zerzes ya canja, Yahudawa kuma suka yi galiba a bisa waɗanda suka ƙi jininsu.
아달월 곧 십이월 십삼일은 왕의 조명을 행하게 된 날이라 유다인의 대적이 저희를 제어하기를 바랐더니 유다인이 도리어 자기를 미워하는 자를 제어하게 된 그 날에
2 Yahudawa suka tattaru a cikin biranensu a dukan lardunan Sarki Zerzes don su kai wa waɗanda suka nemi a hallaka su hari. Babu wanda ya tasar musu domin mutanen dukan sauran al’ummai sun jin tsoronsu.
유다인들이 아하수에로 왕의 각 도, 각 읍에 모여 자기를 해하고자 하는 자를 죽이려 하니 모든 민족이 저희를 두려워하여 능히 막을 자가 없고
3 Dukan sarakuna larduna, da hakimai, da gwamnoni da kuma ma’aikatan sarki suka taimaki Yahudawa, domin tsoron Mordekai ya kama su.
각 도 모든 관원과 대신과 방백과 왕의 사무를 보는 자들이 모르드개를 두려워하므로 다 유다인을 도우니
4 Mordekai babban mutum ne a fada, sunansa ya kai ko’ina a lardunan, ikonsa ya yi ta ƙasaita gaba-gaba.
모르드개가 왕궁에서 존귀하여 점점 창대하매 이 사람 모르드개의 명성이 각 도에 퍼지더라
5 Yahudawa suka karkashe dukan abokan gābansu da takobi, suka karkashe waɗanda suka ƙi jininsu, suka kuma hallaka su yadda suka ga dama.
유다인이 칼로 그 모든 대적을 쳐서 도륙하고 진멸하고 자기를 미워하는 자에게 마음대로 행하고
6 A mazaunin masarautar a Shusha, Yahudawa suka karkashe, suka kuma hallaka mutum ɗari biyar.
유다인이 또 도성 수산에서 오백 인을 죽이고 멸하고
7 Suka kuma kashe Farshandata, da Dalfon, da Asfata,
또 바산다다와 달본과 아스바다와
8 da Forata, da Adaliya, da Aridata,
보라다와 아달리야와 아리다다와
9 da Farmashta, da Arisai, da Aridai da kuma Baizata,
바마스다와 아리새와 아리대와 왜사다
10 ’ya’ya maza goma na Haman ɗan Hammedata, abokin gāban Yahudawa. Amma ba su taɓa dukiyarsu ba.
곧 함므다다의 손자요 유다인의 대적 하만의 열 아들을 죽였으나 그 재산에는 손을 대지 아니하였더라
11 A wannan rana, aka ba wa sarki rahoton yawan mutanen da aka kashe a mazaunin masarauta, a Shusha.
그 날에 도성 수산에서 도륙한 자의 수효를 왕께 고하니
12 Sarki ya ce wa Sarauniya Esta, “Yahudawa sun karkashe, suka kuma hallaka mutum ɗari biyar, da kuma’ya’ya maza goma na Haman a mazaunin masarauta a Shusha. Me suka yi a sauran lardunan sarki? Yanzu kuma mene ne roƙonki? Za a ba ki. Mece ce bukatarki? Za a biya miki.”
왕이 왕후 에스더에게 이르되 유다인이 도성 수산에서 이미 오백 인을 죽이고 멸하고 또 하만의 열 아들을 죽였으니 왕의 다른 도에서는 어떠하였겠느뇨 이제 그대의 소청이 무엇이뇨 곧 허락하겠노라 그대의 요구가 무엇이뇨 또한 시행하겠노라
13 Esta ta ce, “In sarki ya yarda, yă ba wa Yahudawa da suke Shusha izini su aikata dokan nan gobe kuma, bari kuma a rataye’ya’ya maza goma na Haman a kan gumagumai.”
에스더가 가로되 왕이 만일 선히 여기시거든 수산에 거하는 유다인으로 내일도 오늘날 조서대로 행하게 하시고 하만의 열 아들의 시체를 나무에 달게 하소서
14 Sai sarki ya ba da umarni a yi haka ɗin. Aka ba da doka a Shusha, aka kuma rataye’ya’ya maza goma na Haman.
왕이 그대로 행하기를 허락하고 조서를 내리니 하만의 열 아들의 시체가 달리니라
15 Yahudawan da suke Shusha suka taru a ran goma sha huɗu na watan Adar suka kuma karkashe mutum ɗari uku a Shusha, amma ba su taɓa dukiyarsu ba.
아달월 십사일에도 수산에 있는 유다인이 모여 또 삼백 인을 수산에서 도륙하되 그 재산에는 손을 대지 아니하였고
16 Ana cikin haka, sai saura Yahudawa waɗanda suke lardunan sarki su ma suka taru domin su kāre kansu su kuma sami hutu daga abokan gābansu. Suka karkashe mutum dubu saba’in da biyar amma ba su taɓa dukiyarsu ba.
왕의 각 도에 있는 다른 유다인들이 모여 스스로 생명을 보호하여 대적들에게서 벗어나며 자기를 미워하는 자 칠만 오천 인을 도륙하되 그 재산에는 손을 대지 아니하였더라
17 Wannan ya faru a ran goma sha uku na watan Adar. A rana ta goma sha huɗu kuwa suka huta, suka kuma mai da ita ranar biki da kuma ta farin ciki.
아달월 십삼일에 그 일을 행하였고 십사일에 쉬며 그 날에 잔치를 베풀어 즐겼고
18 Amma Yahudawan da suke a Shusha suka taru a rana ta goma sha uku da ta sha huɗu, sa’an nan a rana ta goma sha biyar suka huta, suka kuma mai da ita ranar biki da ta farin ciki.
수산에 거한 유다인은 십삼일과 십사일에 모였고 십오일에 쉬며 이 날에 잔치를 베풀어 즐긴지라
19 Shi ya sa Yahudawan ƙauyuka, waɗanda suke zama a karkara, suke kiyaye rana ta goma sha huɗu ta watan Adar a matsayin ranar farin ciki da ta biki, ranar ba da kyautai ga juna.
그러므로 촌촌의 유다인 곧 성이 없는 고을 고을에 거하는 자들이 아달월 십사일로 경절을 삼아 잔치를 베풀고 즐기며 서로 예물을 주더라
20 Sai Mordekai ya rubuta waɗannan abubuwa, ya kuma aika wasiƙu ga dukan Yahudawa ko’ina a lardunan Sarki Zerzes, na kusa da na nesa.
모르드개가 이 일을 기록하고 아하수에로 왕의 각 도에 있는 모든 유다인에게 무론 원근하고 글을 보내어 이르기를
21 Ya sa su yi bikin kowace shekara a ranaku goma sha huɗu da goma sha biyar na watan Adar
한 규례를 세워 해마다 아달월 십사일과 십오일을 지키라
22 a matsayin lokacin da Yahudawa suka sami huta daga abokan gābansu, da kuma a matsayin watan da aka mai da baƙin cikinsu ya zama farin ciki, makokinsu kuma ya zama ranar biki. Ya rubuta musu su kiyaye ranakun a matsayin ranakun biki da na farin ciki. Su kuma ba da kyautai na abinci ga juna, da kuma kyautai ga matalauta.
이 달 이 날에 유다인이 대적에게서 벗어나서 평안함을 얻어 슬픔이 변하여 기쁨이 되고 애통이 변하여 길한 날이 되었으니 이 두 날을 지켜 잔치를 베풀고 즐기며 서로 예물을 주며 가난한 자를 구제하라 하매
23 Ta haka, Yahudawa suka yarda su ci gaba da bikin da suka fara, suna aikata abin da Mordekai ya rubuta musu.
유다인이 자기들의 이미 시작한 대로 또는 모르드개의 보낸 글대로 계속하여 행하였으니
24 Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, abokin gāban dukan Yahudawa, ya ƙulla maƙarƙashiya game da Yahudawa, domin a hallaka su, ya kuma jefa fur (wato, ƙuri’a) don yă hallaka su.
곧 아각 사람 함므다다의 아들 모든 유다인의 대적 하만이 유다인을 진멸하기를 꾀하고 부르 곧 제비를 뽑아 저희를 죽이고 멸하려 하였으나
25 Amma sa’ad da sarki ya sami labarin maƙarƙashiyar, sai ya ba da umarnai a rubuce cewa mugun shirin da Haman ya ƙulla a kan Yahudawa yă komo kansa, kuma cewa a rataye shi da’ya’yansa maza a kan gumagumai.
에스더가 왕의 앞에 나아감을 인하여 왕이 조서를 내려 하만이 유다인을 해하려던 악한 꾀를 그 머리에 돌려 보내어 하만과 그 여러 아들을 나무에 달게 하였으므로
26 (Saboda haka, aka kira ranakun nan Furim, daga kalma fur). Saboda dukan abin da aka rubuta cikin wannan wasiƙa da kuma abin da suka gani, da abin da ya same su.
무리가 부르의 이름을 좇아 이 두 날을 부림이라 하고 유다인이 이 글의 모든 말과 이 일에 보고 당한 것을 인하여
27 Yahudawa suka ɗauki nawayar kafa al’adar cewa su, da zuriyarsu, da dukan waɗanda suka haɗa hannun da su, za su kiyaye waɗannan kwanaki biyu, kowace shekara yadda aka tsara, a kuma lokacin da aka keɓe dominsu.
뜻을 정하고 자기와 자손과 자기와 화합한 자들이 해마다 그 기록한 정기에 이 두 날을 연하여 지켜 폐하지 아니하기로 작정하고
28 Za a tuna, a kuma kiyaye waɗannan kwanaki a kowane zamani, cikin kowane iyali, da kuma cikin kowane lardi, da kowace birni. Kuma kada Yahudawa su fasa yin bikin waɗannan kwanakin Furim, ko su bar jikokinsu su manta da kiyaye waɗannan ranaku biyu.
각 도, 각 읍, 각 집에서 대대로 이 두 날을 기념하여 지키되 이 부림일을 유다인 중에서 폐하지 않게 하고 그 자손 중에서도 기념함이 폐하지 않게 하였더라
29 Saboda haka Sarauniya Esta,’yar Abihayil, tare da Mordekai mutumin Yahuda, suka rubuta da cikakken iko, suka tabbatar da wannan wasiƙa ta biyu game da Furim.
아비하일의 딸 왕후 에스더와 유다인 모르드개가 전권으로 글을 쓰고 부림에 대한 이 둘째 편지를 굳이 지키게 하되
30 Mordekai kuwa ya aika da wasiƙu zuwa ga dukan Yahudawa cikin larduna 127 na masarautar Zerzes. Saƙon fatan alheri da na tabbaci,
화평하고 진실한 말로 편지를 써서 아하수에로의 나라 일백이십칠 도에 있는 유다 모든 사람에게 보내어
31 don a kafa waɗannan ranakun Furim a keɓaɓɓen lokacinsu, kamar yadda Mordekai mutumin Yahuda da Sarauniya Esta suka dokace su. Yadda kuma suka kafa wa kansu da zuriyarsu, game da lokutansu na azumi da makoki.
정한 기한에 이 부림일을 지키게 하였으니 이는 유다인 모르드개와 왕후 에스더의 명한 바와 유다인이 금식하며 부르짖은 것을 인하여 자기와 자기 자손을 위하여 정한 바가 있음이더라
32 Dokar Esta ta tabbatar da waɗannan umarnai game da Furim, aka kuma rubuta ta cikin tarihi.
에스더의 명령이 이 부림에 대한 일을 견고히 하였고 그 일이 책에 기록되었더라

< Esta 9 >