< Esta 6 >

1 A daren nan, sarki bai iya barci ba, saboda haka ya ba da umarni a kawo, a kuma karanta masa littafin tarihi na shekara-shekara, da rubutaccen labarin mulkinsa.
On that night the king was unable to sleep, so he gave orders to bring the books that recorded memorable deeds, and they were read before the king.
2 Aka tarar, a rubuce a ciki, cewa Mordekai ya tone ƙulle-ƙullen Bigtana da Teresh, biyu daga hafsoshin sarki, waɗanda suke tsaron mashigin ƙofa, waɗanda suka ƙulla su kashe Sarki Zerzes.
It was found recorded how Mordecai had furnished information regarding Bigthan and Teresh, two of the king’s attendants who guarded the entrance of the palace, who had attempted to kill King Ahasuerus.
3 Sarki ya ce, “Wace girma da daraja ce aka ba wa Mordekai saboda wannan?” Masu hidimarsa suka ce, “Ba a yi masa wani abu ba.”
“What honor and dignity have been conferred on Mordecai for this?” the king asked. When the king’s pages who waited on him replied “Nothing has been done for him,”
4 Sarki ya ce, “Wa yake a haraba?” Daidai lokacin kuwa Haman ya shigo harabar waje na fada don yă yi magana da sarki a kan a rataye Mordekai a wurin rataye mai laifin da ya shirya.
the king said, “Who is in the court?” Now Haman had just entered the outer court of the king’s house to speak to the king about hanging Mordecai on the gallows that he had prepared for him.
5 Masu yi wa sarki hidima, suka amsa, “Haman yana tsaye a haraba.” Sarki ya umarta, “A kawo shi ciki.”
So the king’s pages said to him, “Haman is standing there, in the court.” The king said, “Let him enter.”
6 Sa’an nan Haman ya shigo, sai sarki ya ce masa, “Me ya kamata a yi wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama?” Haman dai ya yi tunani a ransa ya ce, “Wane ne sarki zai girmama in ba ni ba?”
So Haman entered, and the king said to him, “What should be done for the man whom the king wishes to honor?” Haman said to himself, “Whom besides me could the king wish to honor?”
7 Sai ya amsa wa sarki cewa, “Saboda mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama,
So he said to the king, “For the man whom the king wishes to honor
8 bari a kawo rigar sarautar da sarki ya taɓa sawa, da kuma dokin da sarki ya taɓa hawa, wanda aka sa kambin sarauta a kai.
let a royal garment be brought, which the king has worn, and the horse on which the king has ridden and on whose head a royal diadem has been placed.
9 Sa’an nan, bari a ba da rigar da kuma dokin wa ɗaya daga cikin manyan sarakuna mafi kirki na sarki. Bari shi kuma yă sa wannan riga wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama, a kuma bi da shi a bisan doki ko’ina a titunan birni, ana shela a gabansa ana cewa, ‘Wannan shi ne abin da ake yin wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!’”
Then let the garment and the horse be placed in charge of one of the king’s noble officials. Let him clothe the man whom the king wishes to honor and let him lead that man on the horse through the city square, proclaiming before him, ‘This is what is done for the man whom the king wishes to honor.’”
10 Sarki ya umarci Haman ya ce, “Tafi yanzu ka karɓi rigar da dokin, ka kuma yi yadda ka shawarta wa Mordekai, mutumin Yahudan nan, wanda yake zama a bakin ƙofar sarki. Kada ka kāsa yin kome daga cikin abin da ka faɗa.”
Then the king said to Haman, “Make haste and take the garment and the horse, as you have said, and do this to Mordecai the Jew, who sits in the king’s gate. Omit nothing of all you have said.”
11 Saboda haka, Haman ya karɓo rigar da dokin. Ya sa wa Mordekai rigar, ya kuma bi da shi a kan doki ko’ina a titunan birnin, yana shela a gabansa yana cewa, “Wannan shi ne abin da ake yi wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!”
So Haman took the garment and the horse and clothed Mordecai, and made him ride through the city square and proclaimed before him, “This is what is done for the man whom the king wishes to honor.”
12 Daga baya, Mordekai ya dawo zuwa ƙofar sarki. Amma Haman ya ruga gida, kansa a rufe, saboda baƙin ciki.
Mordecai returned to the king’s gate, but Haman hurried to his house, mourning, with his head covered.
13 Ya je ya faɗa wa matarsa Zeresh, da dukan abokansa, me ya same shi. Masu ba shi shawara, da matarsa Zeresh, suka ce masa, “Idan Mordekai, wanda ka fara fāɗuwa a gabansa, daga zuriyar Yahudawa yake, to, ba za ka yi nasara a kansa ba, tabbatacce za ka fāɗi a gabansa!”
Haman recounted to Zeresh his wife and to all his friends everything that had happened to him. Then his wise men and Zeresh his wife said to him, “If Mordecai before whom you have already been humiliated is of the Jewish people, you can do nothing against him but will surely fall before him.”
14 Suna cikin magana da shi ke nan, sai ga bābānnin sarki, suka iso suka kuma hanzarta da Haman zuwa liyafar da Esta ta shirya.
While they were still talking with him, the king’s attendants came and quickly took Haman to the banquet that Esther had prepared.

< Esta 6 >