< Esta 5 >
1 A rana ta uku, Esta ta sanya rigunanta na sarauta, ta tafi ta tsaya a harabar fada, a gaban zaure sarki. Sarki yana zaune a kan gadon sarautarsa a zauren, yana fuskantar ƙofar shiga.
第三天,艾斯德爾身穿王后的華服,站在王宮的內院,面向宮殿;那時君王正坐在宮殿的寶座上,面向宮門。
2 Sa’ad da ya ga Sarauniya Esta tsaye a harabar, sai ya ji daɗin ganinta, ya miƙa mata sandan sarauta na zinariya da take hannunsa. Sai Esta ta matsa kusa ta taɓa kan sandan.
君王一見艾斯德爾王后在庭院內,就對她起了寵幸的心,於是向艾斯德爾伸出手中的金杖,艾斯德爾遂上前來,摸了金杖的頂端。
3 Sai sarki ya ce mata, “Me kike so, Sarauniya Esta? Mene ne roƙonki? Kai, ko rabin masarautata ce, za a ba ki.”
君王問她說:「艾斯德爾后,你有什麼事﹖你要求什麼﹖即使要求一半江山,我也必賜給你! 」
4 Esta ta ce, “In ya gamshi sarki, bari sarki, tare da Haman su zo wurin liyafar da na shirya wa sarki yau.”
艾斯德爾答說:「若大王開恩,請大王今日與哈曼同去飲妾為陛下所預備的酒宴。」
5 Sai sarki ya ce, “Maza a kawo Haman don mu yi abin da Esta ta roƙa.” Saboda haka, sarki da Haman suka tafi liyafar da Esta ta shirya.
王遂說:「快叫哈曼來,以滿足艾斯德爾的心願! 」於是王和哈曼一同去赴艾斯德爾預備的酒宴。
6 Yayinda suke shan ruwan inabi, sarki ya sāke ce wa Esta, “Yanzu, mece ce bukatarki? Za a biya miki shi. Kuma mene ne roƙonki? Kai, ko rabin masarautata ce, za a ba ki.”
酒興之餘,王對艾斯德爾說:「你要求什麼,我必給你;不管你求什麼,那怕是半壁江山,也必照辦。」
7 Esta ta amsa ta ce, “Bukatata da kuma roƙona shi ne,
艾斯德爾答說:「這即是我的懇請和要求:
8 in na sami tagomashi a wurin sarki, in kuma sarki ya yarda yă biya mini bukatata, yă kuma ji roƙona, bari sarki da Haman su zo gobe wurin liyafar da zan shirya musu. Sa’an nan zan amsa tambayar sarki.”
如果我見寵於大王,如果大王樂意俯允我的懇請,實踐我的要求,就請大王明天與哈曼,再來飲妾所設的酒宴;明天我必依照君王的命答覆陛下。」
9 Haman ya fita a ranan da murna, ya kuma ji daɗi. Amma sa’ad da ya ga Mordekai a bakin ƙofar sarki, ya kuma lura cewa bai tashi, ko yă nuna bangirma a gabansa ba, sai ya cika da fushi.
那一天,哈曼出去,非常高興,滿心喜樂;但是哈曼一見在御門前的猶太人摩爾德開既不起立,也不退避,就對他滿懷憤恨,
10 Duk da haka, Haman ya cije, ya tafi gida. Sai ya kira abokansa da kuma matarsa, Zeresh,
卻仍忍氣回了家,且打發人叫他的朋友和愛妻則勒士來,
11 ya yi ta taƙama game da ɗumbun wadatarsa, da yawan’ya’yansa maza, da dukan yadda sarki ya girmama shi, ya kuma ɗaga shi bisan sauran hakimai da shugabanni.
向他們誇耀自己如何富貴榮華,子女如何眾多,君王如何尊崇他,如何高舉他在眾公卿和朝臣之上。
12 Haman ya ƙara da cewa, “Ba duka ke nan ba, kai, ni ne kaɗai mutumin da Sarauniya Esta ta gayyata yă tafi tare da sarki zuwa liyafar da ta shirya. Ta sāke gayyace ni tare da sarki gobe.
他又說:「甚至,艾斯德爾王后,除我以外,沒有請任何人與君王一同赴她設的盛宴;明天又請我再同君王到她那裏去。
13 Amma dukan wannan bai biya mini bukata ba, muddin ina ganin wannan mutumin Yahudan nan Mordekai, yana zama a bakin ƙofar sarki.”
但每當我一見坐在御門前的猶太人摩爾德開時,這一切於我都乏味了! 」
14 Matarsa Zeresh, da dukan abokansa suka ce masa, “Ka sa a gina wurin rataye mai laifi, mai tsawo, ƙafa saba’in da biyar, da safe kuwa ka ce wa sarki a rataye Mordekai a kansa. Sa’an nan ka tafi cin abincin dare tare da sarki da murna.” Wannan shawarar ta faranta wa Haman rai, ya kuma sa aka gina wurin rataye mai laifi.
他的愛妻則勒士和他的朋友便對他說:「該做一個高五十尺的刑架,天一亮就對君王說:把摩爾德開懸在上面! 這樣你可欣然與君王共同赴筵了。」哈曼看這主意不錯,就叫人做了一個刑架。