< Esta 3 >
1 Bayan waɗannan al’amura, sai Sarki Zerzes ya girmama Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, ya ɗaukaka shi, ya kuma ba shi matsayi mafi girma fiye da na dukan sauran hakiman.
2 Dukan masu hidimar da suke a ƙofar sarki suka riƙa durƙusa suna ba wa Haman girma, gama sarki ya ba da umarni a yi masa haka. Amma Mordekai bai durƙusa ya ba shi girma ba.
3 Sa’an nan masu hidimar da suke a ƙofar sarki suka tambaye Mordekai, “Me ya sa ba ka yin biyayya da umarnin sarki?”
4 Kowace rana suna masa magana, amma ya ƙi yă yi. Saboda haka, suka faɗa wa Haman game da wannan don su ga ko za a jure da halin Mordekai, gama ya faɗa musu cewa shi mutumin Yahuda ne.
5 Sa’ad da Haman ya ga cewa Mordekai ba ya durƙusa ko yă girmama shi, sai ya fusata.
6 Da yake an faɗa masa asalin Mordekai, sai ya ga a kashe Mordekai kaɗai ba zai biya masa bukata ba. A maimakon haka, Haman ya nemi hanya a hallaka dukan mutanen Mordekai, wato, Yahudawa, a ko’ina a dukan masarautar Zerzes.
7 A shekara ta goma sha biyu ta Sarki Zerzes, a wata na farko, watan Nisan, sai suka jefa fur (wato, ƙuri’a) a gaban Haman don a zaɓi rana da watan da zai dace da ƙulle-ƙullen. Sai ƙuri’a ta fāɗa a kan wata na goma sha biyu, wato, watan Adar.
8 Sai Haman ya ce wa Sarki Zerzes, “Akwai waɗansu mutanen da suke a warwatse, sun kuma bazu a cikin mutane cikin dukan lardunan masarautarka, waɗanda al’adunsu sun yi dabam da na dukan sauran mutane. Mutanen nan ba sa biyayya da dokokin sarki; ba zai yi wa sarki kyau a jure su ba.
9 In ya gamshi sarki, bari a yi doka, don a hallaka su, zan kuma sa talenti dubu goma na azurfa a cikin ma’ajin fada saboda mutanen da suka aikata wannan sha’ani.”
10 Saboda haka sarki ya zare zoben hatimi daga yatsarsa, ya ba wa Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, abokin gāban Yahudawa.
11 Sarki ya ce wa Haman, “Ka riƙe kuɗin, ka kuma yi da mutanen yadda ka ga dama.”
12 Sa’an nan aka kira magatakardun sarki a rana ta goma sha uku na wata na fari. Suka rubuta dukan umarnin Haman a irin rubutun kowane lardi, kuma cikin harshen kowane mutane, zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da gwamnonin larduna dabam-dabam, da kuma hakiman mutane dabam-dabam. Aka rubuta waɗannan a sunan Sarki Zerzes da kansa, aka kuma hatimce da zobensa.
13 Aka aika’yan-kada-tă-kwana da saƙoni zuwa dukan lardunan sarki da umarni a hallaka, a karkashe, a kuma kawar da dukan Yahudawa, manya da ƙanana, mata da yara, a kuma washe kayayyakinsu.
14 Za a ba da kofin rubutun a matsayin doka a kowane lardi, a kuma sanar da mutanen kowace al’umma, domin su zauna da shiri don wannan rana.
15 Bisa ga umarnin sarki, sai’yan-kada-tă-kwana, suka tafi da sauri. Aka ba da umarni a mazaunin masarauta da yake a Shusha. Sai Sarki da Haman suka zauna don su sha, amma birnin Shusha ya ruɗe.