< Esta 2 >
1 Daga baya sa’ad da fushin Sarki Zerzes ya huce, sai ya tuna da Bashti da abin da ta yi, da kuma dokar da ya bayar game da ita.
2 Sai masu hidimar sarki na musamman, suka kawo shawara cewa, “Bari a nemi, kyawawan budurwai saboda sarki.
3 Bari sarki yă naɗa komishinoni a kowane yanki na masarautarsa, domin su kawo dukan waɗannan kyawawan’yan mata cikin harabar mazaunin masarautar a Shusha. Bari a sa su a hannun Hegai, bābān sarki, wanda yake lura da mata, bari kuma a yi musu kulawa ta musamman.
4 Sa’an nan bari yarinyar da ta gamshi sarki, tă zama sarauniya a maimakon Bashti.” Wannan shawara ta gamshi sarki, ya kuwa yi na’am da ita.
5 To, a cikin mazaunin masarauta a Shusha, akwai wani mutumin Yahuda, daga Kabilar Benyamin mai suna Mordekai, ɗan Yayir, ɗan Shimeyi, ɗan Kish,
6 wanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya ɗauka tare’yan zaman bauta cikin waɗanda ya ɗauko daga Urushalima, tare da Yekoniya, sarkin Yahuda.
7 Mordekai yana da wata’yar kawunsa mai suna Hadassa, wanda ya yi reno, ba ta da mahaifi ko mahaifiya. Ita ce yarinyar da aka santa da suna Esta. Kyakkyawa ce ƙwarai. Mordekai dai ya ɗauke ta tamƙar’yarsa sa’ad da mahaifinta da mahaifiyarta suka mutu.
8 Da aka yi shelar umarni da dokar sarki, sai aka kawo’yan mata masu yawa a mazaunin masarauta a Shusha, aka kuma sa su ƙarƙashin kulawar Hegai. Aka kawo Esta ma zuwa fadar sarki, aka danƙa ta wa Hegai, wanda yake lura da mata.
9 Yarinyar ta gamshe shi, ta kuma sami tagomashinsa. Nan da nan ya tanada mata, ya ba ta man shafawa da abinci na musamman. Ya ba ta bayi mata bakwai da aka zaɓa daga fadar sarki. Ya kuma kai ta tare da bayinta zuwa wuri mafi kyau na gidan matan kulle.
10 Esta ba tă bayyana asalin al’ummarta da na iyalinta ba, domin Mordekai ya hana yin haka.
11 Kowace rana Mordekai yana kai da komowa kusa da harabar filin gidan matan kulle, domin ya san yadda Esta take, da kuma abin da yake faruwa da ita.
12 Kafin a kai kowace yarinya wurin Sarki Zerzes, sai ta gama watanni goma sha biyu cif ana yin mata kwalliyar da aka tsara, akan ɗauki watanni shida ana shafa mata man mur, a ɗauki watanni shida kuma ana shafa mata man ƙanshi da kayan shafe-shafe.
13 A kuma koya mata yadda za tă tafi wurin sarki. Aka ba ta duk abin da take so ta riƙe daga gidan matan kulle zuwa fadar sarki.
14 Da yamma za tă tafi can, da safe kuma ta dawo wani ɓangaren gidan matan kullen da yake a ƙarƙashin kulawar Sha’ashgaz, bābā na sarki, wanda yake lura da ƙwarƙwarai. Ba ta dawowa wurin sarki sai in ta gamshe shi, sai ya kuma kira ta da suna.
15 Sa’ad da lokaci ya yi da Esta (yarinyar da Mordekai ya ɗauka tamƙar’yarsa,’yar kawunsa Abihayil) za tă shiga wurin sarki, ba tă nemi a ba ta kome ba in ban da abin da Hegai, bābān sarki mai lura da gidan matan kulle, ya ba da shawara. Esta kuwa ta sami tagomashin kowa da ya ganta.
16 Aka kai Esta wurin Sarki Zerzes a mazaunin sarauta a wata na goma, watan Tebet, a shekara ta bakwai ta mulkinsa.
17 To, sarki ya so Esta fiye da duk sauran matan, ta kuma sami tagomashinsa da kuma yardarsa fiye da duk sauran budurwai. Saboda haka ya sa rawanin sarauta a kanta, ya kuma mai da ita sarauniya a maimakon Bashti.
18 Sarki kuwa ya yi ƙasaitacciyar liyafa, liyafar Esta, wa dukan hakimansa da shugabannin masarautarsa. Ya yi shelar hutu ko’ina a larduna, ya kuma raba kyautai a yalwace irin na sarauta.
19 Sa’ad da aka tara budurwai karo na biyu, Mordekai kuwa yana zama a bakin ƙofar sarki.
20 Amma Esta ta ɓoye asalin iyalinta da na al’ummarta yadda Mordekai ya ce ta yi, gama ta ci gaba da bin umarnan Mordekai yadda take yi sa’ad da yake renonta.
21 Sa’ad da Mordekai yake zaune a bakin ƙofar sarki, sai Bigtana da Teresh, biyu daga cikin hafsoshin sarki masu gadin ƙofar shiga, suka yi fushi, suka kuma ƙulla su kashe sarki Zerzes.
22 Mordekai kuwa ya sami labarin makircin, ya kuma faɗa wa Sarauniya Esta, wadda ta faɗa wa sarki, ta kuma nuna masa cewa Mordekai ne ya ji.
23 Sa’ad da aka bincika labarin aka kuma iske gaskiya ne, sai aka rataye hafsoshin nan biyu a wurin rataye mai laifi. Aka rubuta dukan wannan a cikin littafin tarihi a gaban sarki.