< Afisawa 6 >
1 Ku’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan.
Imrli, wotre batiembi wa batie ni mi Rjia, ahi kpe u bi.
2 Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,
To tie mbi ni yi mbi ni nfutu ahi njitre u mumlan ni alkawali.
3 don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”
ndu yi kpa lulu, ndi tie se gbugbuu ni mgbu mgblu yi
4 Ku kuma iyaye, kada ku tsokane’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.
Nakima me, Batie, na tie kpe wa ani kpa sron mrlimbi tir memea na, tsro ba kon ndi ndi ni mitre Baci.
5 Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya. Ku nuna musu halin bangirma, kuna kuma yin musu biyayya cikin dukan abu, da zuciya ɗaya kamar ga Kiristi kuke yi.
Igran, wo tre batie ko mbi u mgbumgbluyi ndi klu sissri mba ni mi dri mbi, wo tre mba nawa bi wo u' kristia.
6 Ku yi aiki sosai, ba don kawai ku gamshe su sa’ad da suke kallonku ba. Da yake ku bayin Kiristi ne, ku aikata nufin Allah da dukan zuciyarku.
Na tir kpe ndi ndi ni shishi ba tre ko mbi ni ndu ba gbre yi san na tie na bi gran kristi tie kpe wa Rji ni son'a rji nimi dri mbi.
7 Ku yi aikinku da kyakkyawar niyya, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba mutane ba.
Tiendu ni sron me wawuu, na wu tie ni Baci, ana ni ndji na.
8 Gama kun san cewa Ubangiji zai ba da lada ga kowa gwargwadon kowane aiki nagarin da ya yi, ko shi bawa ne, ko’yantacce.
Ki to ndi kpe ndindi wa ndji ba tiea ba kpalulu ni Baci, I gran ko ndji wa ba cuwu cuwoa.
9 Ku kuma masu bayi, dole ku bi da bayinku da kyau. Ku daina ba su tsoro. Ku tuna, ku da su, Maigida ɗaya kuke da shi a sama, kuma ba ya nuna bambanci.
Na kima, i ttieko, tie ni gran na kima me na nuba sissri na. Irji mba ni u mbia he ni shu. ana tie sontuwa
10 A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji yă ba ku ƙarfi.
I clema, tie mgbe mgble ni mi Baci.
11 Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan.
Sru kpe ku u Rji, ndi ndu zayi krli ni kagji u shetan.
12 Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. (aiōn )
Iku mbua na he u nama ni yi na, ama ahi mgbemgble, ni mahukunta u mgbumgblu yi ubwu ni rudunai bi bwu u memme ni mi shu gbugbuu. (aiōn )
13 Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge.
Naki ban kpe ku u Rji, don ni krli mgbanmgban ni memme vi. Bita tie koge bi krli ni mgbemgble.
14 Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya tă zama ɗamararku, adalci yă zama sulkenku,
Krli mgban mgban, ndi lo rji rji ni tri mbi, ndi sru damgban u tsratsra.
15 shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku.
Tie nayi ndi lo za mbi mgbamgban ndi ji tre rji u si sron hi.
16 Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita.
Ni me kpe wawuu, ban dagban u yosron, wawumbi wu i whien bi memme.
17 Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.
Ndi ban tagya u gbujbu ni njigban u brji tsratsra, wa a hi tre Rjia.
18 A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a.
Ni bre mbi wawuu, ta tre ni baci cacuu nimi tsratsra. Ni cleama, taya ni yosron nita tre ni baci nitu ndi bi hu wawuu.
19 Ku kuma yi addu’a domina, don duk sa’ad da na buɗe bakina, in sami kalmomi babu tsoro, don in sanar da asirin bishara,
Bre nimu ndu me kpa tori ni ton wa mi bwu yyua. Bre nimu ndume fe sron wa mi hla tre jaji wa baria.
20 wadda nake jakadanta cikin sarƙoƙi. Ku yi addu’a don in iya yin shelarta babu tsoro, yadda ya kamata in yi.
Nitu bishara mi kati ndi u tondu wa baya, zie ni mi zrea, ndi dume tre hamma ni glu sissiri.
21 Tikikus, ƙaunataccen ɗan’uwa da kuma amintaccen bawa cikin Ubangiji, zai faɗa muku kome, domin ku ma ku san yadda nake, da kuma abin da nake yi.
Tikikus, vayimu wa misonwu kpu kpome, ndi kpau y'me a hi gran nimi Baci, ani hla ni yuwuu wawuu.
22 Na aike shi gare ku musamman don wannan, domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa ku.
Nitu kimayi miton wu ye niyi ni ndu yito kpe wa ki he nimiandi ndu yi fe si ni sron bi.
23 ’Yan’uwa, salama tare da ƙauna da kuma bangaskiya daga Allah Uba da Ubangiji Yesu Kiristi su kasance tare da ku.
Ndu si he ni mrli, ison ni yosron ni Rji tie ni Baci Yesu Almasihu.
24 Alheri yă tabbata ga dukan masu ƙaunar Ubangiji Yesu Kiristi da ƙauna marar ƙarewa.
Ndu si he ni biwa ba son Baci mbu Yesu Almasihu ni son u kakle.