< Afisawa 5 >
1 Ku zama masu koyi da Allah, kamar ƙaunatattun’ya’ya,
2 ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu, har ya ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah.
3 Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata, ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da mutane masu tsarki na Allah ba.
4 Haka ma bai kamata a sami datti, ƙazamar magana, ko zancen banza a cikinku ba, domin ba su dace ba, a maimakon haka sai ku yi ta yin godiya.
5 Ku dai tabbata, ba wani mai fasikanci, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayin (wanda shi da mai bautar gumaka ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Kiristi da na Allah.
6 Kada wani yă ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya.
7 Saboda haka kada ku haɗa kai da su.
8 Gama a dā zukatanku sun cika da duhu, amma yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi rayuwa kamar’ya’yan haske
9 (domin amfanin haske ya ƙunshi nagarta, adalci, da kuma gaskiya)
10 ku nemi abin da zai gamshi Ubangiji.
11 Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su.
12 Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da marasa biyayya suke yi a ɓoye.
13 Duk abin da aka kawo a gaban haske ana iya ganinsa, kuma duk abin da aka haskaka yakan zama haske.
14 Shi ya sa aka ce, “Ka farka, ya kai mai barci, ka tashi daga matattu, Kiristi kuwa zai haskaka ka.”
15 Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima.
16 Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne.
17 Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji.
18 Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu.
19 Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji.
20 Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.
21 Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke nuna wa Kiristi.
22 Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, kamar ga Ubangiji ne kuke yi.
23 Gama miji shi ne kan mace, yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa.
24 To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome.
25 Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta.
26 Ya mai da ikkilisiya ta zama mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa.
27 Kiristi ya yi haka don yă miƙa wa kansa ikkilisiya mai ɗaukaka da kuma mai tsarki, marar aibi, marar tabo, da kuma marar lahani.
28 Don haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa, yana ƙaunar kansa ne.
29 Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai yă ciyar da shi, yă kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya,
30 gama mu gaɓoɓin jikinsa ne.
31 “Saboda haka mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su biyun su zama jiki ɗaya.”
32 Wannan babban asiri ne, amma na ɗauke shi a matsayin kwatanci ne na Kiristi da ikkilisiya.
33 Duk da haka, dole kowannenku yă ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa, kuma dole matar tă yi biyayya ga mijinta.