< Afisawa 4 >
1 A matsayina na ɗan kurkuku saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi rayuwar da ta dace da kiran da aka yi muku.
2 Kullum ku kasance masu sauƙinkai da kuma hankali; ku zama masu haƙuri, kuna jimrewa da juna cikin ƙauna.
3 Ku yi ƙoƙari sosai ku kiyaye zaman ɗayan nan da Ruhu ya ba ku, ku yi haka ta wurin zaman lafiya da juna.
4 Dukanku jiki ɗaya ne, kuna kuma da Ruhu guda. An ba ku bege guda sa’ad da aka kira ku.
5 Ubangiji ɗaya, bangaskiya ɗaya, baftisma kuma ɗaya,
6 Allah ɗaya Uban duka, wanda yake a bisa duka, ta wurin duka, a cikin duka kuma.
7 Amma ga kowannenmu an ba da alheri bisa ga yadda Kiristi ya rarraba.
8 Shi ya sa aka ce, “Sa’ad da ya hau sama, ya bi da kamammu kamar tawagarsa ya kuma ba da baye-baye ga mutane.”
9 (Me ake nufin da “ya hau,” in ba cewa dā ya sauka can ƙarƙashin ƙasa ba?
10 Shi wannan da ya sauka ɗin, shi ne kuma ya hau zuwa can sama, kai, gaba da sammai, don mulkinsa yă cika duniya gaba ɗaya.)
11 Saboda haka Kiristi kansa ya ba wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu su zama annabawa, waɗansu su zama masu wa’azi, waɗansu kuma su zama fastoci, da kuma malamai.
12 Ya yi haka don yă shirya mutanensa saboda ayyukan hidima, don a gina jikin Kiristi.
13 Wannan zai ci gaba har sai mun zama ɗaya a cikin bangaskiya da kuma ta wurin fahimtarmu na Ɗan Allah. Sa’an nan za mu zama balagaggu, kamar yadda Kiristi yake, mu kuma zama gaba ɗaya cikakku kamar sa.
14 An yi wannan kuwa don kada mu koma zama kamar yara, muna ta canja zukatanmu game da abin da muka gaskata don kawai wani ya faɗa mana wani abu dabam, ko domin wani ya yi wayo ya ruɗe mu, ya sa ƙarya ta zama kamar gaskiya.
15 Ya kamata kullum ƙauna tă sa mu faɗa gaskiya. Ta haka za mu yi girma a kowace hanya, mu kuma zama kamar Kiristi, wanda yake kan
16 dukan jiki. Shi ne ya haɗe jiki duka, ya kuma sa dukan gaɓoɓin jiki suna aiki daidai, yayinda kowace gaɓa take aikinta cikin ƙauna.
17 To, ina dai faɗa muku, ina kuma nace faɗa muku a cikin Ubangiji, cewa kada ku ci gaba da yin rayuwa kamar yadda Al’ummai suke yi, masu banzan tunani.
18 Suna a cikin duhu a fahimtarsu, kuma a rabe suke daga ran Allah saboda jahilcin da yake cikinsu ta dalilin taurarewar zukatansu.
19 Ba sa damu da wani abu ko mai kyau ko marar kyau. Rayukansu sun cika da kowace irin ƙazanta da haɗama.
20 Amma ba abin da aka koya muku ke nan ba sa’ad da kuka zo ga sanin Kiristi.
21 Da yake kun ji duka game da shi, kuka kuma koyi gaskiyar da take cikin Yesu,
22 sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta dā, wadda take lalacewa saboda sha’awace-sha’awacen da suke ruɗe ku.
23 A maimakon haka, bari Ruhu yă sabunta tunaninku da kuma halayenku.
24 Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, yă bayyana cikin adalci, da zaman tsarki.
25 Saboda haka dole kowannenku yă bar yin ƙarya, yă kuma riƙa faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya, gama dukanmu gaɓoɓi jiki ɗaya ne.
26 “Cikin fushinku kada ku yi zunubi.” Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi,
27 kada kuma ku ba wa Iblis dama.
28 Duk wanda yake sata, sai yă daina sata, dole kuma yă yi aiki, yă yi wani abu mai amfani da hannuwansa, don yă sami abin da zai iya raba da masu bukata.
29 Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta.
30 Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa.
31 Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta.
32 Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.