< Afisawa 3 >
1 Saboda haka, ni Bulus, na zama ɗan kurkuku na Kiristi Yesu saboda ku Al’ummai.
2 Na tabbata kun ji labarin hidimar alheri na musamman da Allah ya ba ni dominku.
3 Wannan wasiƙa za tă faɗa muku kaɗan game da yadda Allah ya bayyana mini shirinsa na asiri.
4 A yayinda kuke karanta wannan, za ku gane abin da na sani game da wannan shirin Kiristi.
5 Ba a sanar da wannan asiri wa wani a sauran zamanai ba, amma a yanzu an bayyana shi ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzanninsa da annabawansa.
6 Asirin nan kuwa shi ne cewa ta wurin bishara, Al’ummai sun zama waɗanda za su yi gādo tare da Isra’ila, sun zama gaɓoɓin jiki ɗaya, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Kiristi Yesu.
7 Na zama bawan wannan bishara ta wurin baiwar alherin Allah da aka yi mini ta wurin ikonsa da yake aiki a cikina.
8 Ko da yake ni ba kome ba ne a cikin dukan mutanen Ubangiji, aka ba ni wannan baiwa mai daraja don in faɗa wa Al’ummai cewa saboda Kiristi akwai albarkun da suka wuce gaban misali.
9 An zaɓe ni in bayyana wa dukan mutane shirin asirin nan wanda Allah, mahaliccin kome, ya ɓoye shekara da shekaru. (aiōn )
10 Nufinsa shi ne, yanzu, ta wurin ikkilisiya, a sanar da hikima iri dabam-dabam na Allah ga masu mulki, da masu iko a samaniya.
11 Wannan shi ne madawwamin shirinsa, kuma an aikata shi ta wurin Kiristi Yesu Ubangijinmu. (aiōn )
12 A cikinsa, kuma ta wurin bangaskiya a cikinsa ne muke da ƙarfin halin zuwa kusa da Allah gabagadi.
13 Don haka, ina roƙonku kada ku fid da zuciya saboda abin da ake yi mini a nan. Ai, saboda ku ne nake shan wahalolin nan, wannan kuwa ɗaukakarku ce.
14 Saboda wannan ne nake a durƙushe a gaban Uba,
15 wanda ya ba wa kowane iyali a sama da ƙasa suna.
16 Ina addu’a cewa daga yalwar ɗaukakarsa zai ƙarfafa ku da iko daga ciki ta wurin Ruhunsa.
17 Ina addu’a domin Kiristi yă zauna a cikin zukatanku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu’a saboda ku da kuka kahu sosai cikin ƙauna,
18 don ku sami iko, tare da dukan tsarkaka, ku fahimci fāɗi, tsawo, da kuma zurfin ƙaunar Kiristi take.
19 Ku kuma san wannan ƙauna wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan cikar Allah.
20 Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi shi wanda yake da ikon yin aiki a cikinmu, yana kuma aikata abubuwa fiye da dukan abin da muke roƙo, ko muke tunani.
21 Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi a cikin ikkilisiya da kuma a cikin Kiristi Yesu, har yă zuwa dukan zamanai, har abada abadin! Amin. (aiōn )