< Afisawa 3 >

1 Saboda haka, ni Bulus, na zama ɗan kurkuku na Kiristi Yesu saboda ku Al’ummai.
ܡܛܠ ܗܢܐ ܐܢܐ ܦܘܠܘܤ ܐܤܝܪܐ ܐܢܐ ܕܝܫܘܥ ܡܫܝܚܐ ܥܠ ܐܦܝܟܘܢ ܥܡܡܐ
2 Na tabbata kun ji labarin hidimar alheri na musamman da Allah ya ba ni dominku.
ܐܢ ܫܡܥܬܘܢ ܡܕܒܪܢܘܬܐ ܕܛܝܒܘܬܗ ܕܐܠܗܐ ܕܐܬܝܗܒܬ ܠܝ ܒܟܘܢ
3 Wannan wasiƙa za tă faɗa muku kaɗan game da yadda Allah ya bayyana mini shirinsa na asiri.
ܕܒܓܠܝܢܐ ܐܬܝܕܥ ܠܝ ܐܪܙܐ ܐܝܟܢܐ ܕܟܬܒܬ ܠܟܘܢ ܒܙܥܘܪܝܬܐ
4 A yayinda kuke karanta wannan, za ku gane abin da na sani game da wannan shirin Kiristi.
ܐܝܟ ܡܐ ܕܡܫܟܚܝܬܘܢ ܟܕ ܩܪܝܢ ܐܢܬܘܢ ܠܡܤܬܟܠܘ ܝܕܥܬܝ ܕܒܐܪܙܗ ܕܡܫܝܚܐ
5 Ba a sanar da wannan asiri wa wani a sauran zamanai ba, amma a yanzu an bayyana shi ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzanninsa da annabawansa.
ܗܘ ܕܒܕܪܐ ܐܚܪܢܐ ܠܐ ܐܬܝܕܥ ܠܒܢܝܢܫܐ ܐܝܟ ܕܗܫܐ ܐܬܓܠܝ ܠܫܠܝܚܘܗܝ ܩܕܝܫܐ ܘܠܢܒܝܘܗܝ ܒܪܘܚ
6 Asirin nan kuwa shi ne cewa ta wurin bishara, Al’ummai sun zama waɗanda za su yi gādo tare da Isra’ila, sun zama gaɓoɓin jiki ɗaya, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Kiristi Yesu.
ܕܢܗܘܘܢ ܥܡܡܐ ܒܢܝ ܝܪܬܘܬܗ ܘܫܘܬܦܐ ܕܦܓܪܗ ܘܕܡܘܠܟܢܐ ܕܐܬܝܗܒ ܒܗ ܒܝܕ ܐܘܢܓܠܝܘܢ
7 Na zama bawan wannan bishara ta wurin baiwar alherin Allah da aka yi mini ta wurin ikonsa da yake aiki a cikina.
ܗܘ ܕܐܢܐ ܗܘܝܬ ܡܫܡܫܢܗ ܐܝܟ ܡܘܗܒܬܐ ܕܛܝܒܘܬܗ ܕܐܠܗܐ ܕܐܬܝܗܒܬ ܠܝ ܡܢ ܡܥܒܕܢܘܬܐ ܕܚܝܠܗ
8 Ko da yake ni ba kome ba ne a cikin dukan mutanen Ubangiji, aka ba ni wannan baiwa mai daraja don in faɗa wa Al’ummai cewa saboda Kiristi akwai albarkun da suka wuce gaban misali.
ܠܝ ܕܙܥܘܪܐ ܐܢܐ ܕܟܠܗܘܢ ܩܕܝܫܐ ܐܬܝܗܒܬ ܛܝܒܘܬܐ ܗܕܐ ܕܐܤܒܪ ܒܥܡܡܐ ܥܘܬܪܗ ܕܡܫܝܚܐ ܗܘ ܕܠܐ ܡܬܥܩܒ
9 An zaɓe ni in bayyana wa dukan mutane shirin asirin nan wanda Allah, mahaliccin kome, ya ɓoye shekara da shekaru. (aiōn g165)
ܘܐܢܗܪ ܠܟܠܢܫ ܐܝܕܐ ܗܝ ܡܕܒܪܢܘܬܐ ܕܐܪܙܐ ܗܘ ܕܟܤܐ ܗܘܐ ܡܢ ܥܠܡܐ ܒܐܠܗܐ ܕܟܠ ܒܪܐ (aiōn g165)
10 Nufinsa shi ne, yanzu, ta wurin ikkilisiya, a sanar da hikima iri dabam-dabam na Allah ga masu mulki, da masu iko a samaniya.
ܕܒܝܕ ܥܕܬܐ ܬܬܝܕܥ ܚܟܡܬܗ ܕܐܠܗܐ ܡܠܝܬ ܦܘܪܫܢܐ ܠܐܪܟܘܤ ܘܠܫܘܠܛܢܐ ܕܒܫܡܝܐ
11 Wannan shi ne madawwamin shirinsa, kuma an aikata shi ta wurin Kiristi Yesu Ubangijinmu. (aiōn g165)
ܗܝ ܕܥܬܕ ܗܘܐ ܡܢ ܥܠܡܐ ܘܥܒܕܗ ܒܝܫܘܥ ܡܫܝܚܐ ܡܪܢ (aiōn g165)
12 A cikinsa, kuma ta wurin bangaskiya a cikinsa ne muke da ƙarfin halin zuwa kusa da Allah gabagadi.
ܗܘ ܕܒܗ ܐܝܬ ܠܢ ܦܪܗܤܝܐ ܘܩܪܝܒܘܬܐ ܒܬܘܟܠܢܐ ܕܗܝܡܢܘܬܗ
13 Don haka, ina roƙonku kada ku fid da zuciya saboda abin da ake yi mini a nan. Ai, saboda ku ne nake shan wahalolin nan, wannan kuwa ɗaukakarku ce.
ܡܛܠ ܗܢܐ ܫܐܠܢܐ ܕܠܐ ܬܡܐܢ ܠܝ ܒܐܘܠܨܢܝ ܕܥܠ ܐܦܝܟܘܢ ܕܗܕܐ ܗܝ ܬܫܒܘܚܬܟܘܢ
14 Saboda wannan ne nake a durƙushe a gaban Uba,
ܘܟܐܦܢܐ ܒܘܪܟܝ ܠܘܬ ܐܒܘܗܝ ܕܡܪܢ ܝܫܘܥ ܡܫܝܚܐ
15 wanda ya ba wa kowane iyali a sama da ƙasa suna.
ܗܘ ܕܡܢܗ ܡܫܬܡܗܐ ܟܠ ܐܒܗܘܬܐ ܕܒܫܡܝܐ ܘܒܐܪܥܐ
16 Ina addu’a cewa daga yalwar ɗaukakarsa zai ƙarfafa ku da iko daga ciki ta wurin Ruhunsa.
ܕܢܬܠ ܠܟܘܢ ܐܝܟ ܥܘܬܪܐ ܕܬܫܒܘܚܬܗ ܕܒܚܝܠܐ ܬܫܬܪܪܘܢ ܒܪܘܚܗ ܕܒܒܪܢܫܟܘܢ ܕܠܓܘ
17 Ina addu’a domin Kiristi yă zauna a cikin zukatanku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu’a saboda ku da kuka kahu sosai cikin ƙauna,
ܢܥܡܪ ܡܫܝܚܐ ܒܗܝܡܢܘܬܐ ܘܒܠܒܘܬܟܘܢ ܒܚܘܒܐ ܟܕ ܢܗܘܐ ܫܪܝܪ ܥܩܪܟܘܢ ܘܫܬܐܤܬܟܘܢ
18 don ku sami iko, tare da dukan tsarkaka, ku fahimci fāɗi, tsawo, da kuma zurfin ƙaunar Kiristi take.
ܕܬܫܟܚܘܢ ܠܡܕܪܟܘ ܥܡ ܟܠܗܘܢ ܩܕܝܫܐ ܡܢܘ ܪܘܡܐ ܘܥܘܡܩܐ ܘܐܘܪܟܐ ܘܦܬܝܐ
19 Ku kuma san wannan ƙauna wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan cikar Allah.
ܘܬܕܥܘܢ ܪܒܘܬܐ ܕܝܕܥܬܐ ܕܚܘܒܗ ܕܡܫܝܚܐ ܘܬܬܡܠܘܢ ܒܟܠܗ ܡܘܠܝܐ ܕܐܠܗܐ
20 Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi shi wanda yake da ikon yin aiki a cikinmu, yana kuma aikata abubuwa fiye da dukan abin da muke roƙo, ko muke tunani.
ܠܗܘ ܕܝܢ ܕܡܨܐ ܒܚܝܠܐ ܝܬܝܪ ܡܢ ܟܠ ܠܡܥܒܕ ܠܢ ܘܝܬܝܪ ܡܢ ܡܐ ܕܫܐܠܝܢܢ ܘܪܢܝܢܢ ܐܝܟ ܚܝܠܗ ܕܡܤܬܥܪ ܒܢ
21 Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi a cikin ikkilisiya da kuma a cikin Kiristi Yesu, har yă zuwa dukan zamanai, har abada abadin! Amin. (aiōn g165)
ܠܗ ܬܫܒܘܚܬܐ ܒܥܕܬܗ ܒܝܫܘܥ ܡܫܝܚܐ ܒܟܠܗܘܢ ܕܪܐ ܕܥܠܡܝ ܥܠܡܝܢ ܐܡܝܢ (aiōn g165)

< Afisawa 3 >