< Afisawa 2 >
1 Ku kam, a dā ku matattu ne saboda laifofinku da kuma zunubanku.
2 Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya ga sarki masu ikon sarari sama, wato, ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙin biyayya ga Allah. (aiōn )
3 Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah.
4 Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai,
5 ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku.
6 Allah ya tashe mu tare da Kiristi, ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya.
7 Allah ya yi haka domin a tsararraki masu zuwa yă nuna yalwar alherinsa da ya wuce misali, an bayyana alheransa da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu. (aiōn )
8 Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah.
9 Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai.
10 Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.
11 Saboda haka, ku tuna dā ku Al’ummai ne bisa ga haihuwa, waɗanda kuma ake kira masu “kaciya” sukan kira ku “marasa kaciya” (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu).
12 Ku kuma tuna a lokacin ba ku san Kiristi ba. A ware kuke daga mutanen Isra’ila, ba ku kuma da dangantaka da alkawaran da Allah ya yi da su. Kun yi zama a duniyan nan babu bege kuma babu Allah.
13 Amma yanzu a cikin Kiristi Yesu, ku da dā kuke can da nesa an kawo ku kusa ta wurin jinin Kiristi.
14 Gama shi kansa shi ne salamarmu, shi ne ya kawo ƙungiyoyi biyu suka zama ɗaya, ya kuma rushe katangan nan ta ƙiyayya wadda ta raba mu.
15 Kiristi ya ba da jikinsa don yă kawar da doka da dukan umarnanta da kuma ƙa’idodinta. Ya yi haka domin yă halicci sabuwar zuriya daga zuriyoyin nan biyu. Ta haka kuma ya kawo salama tsakaninsu.
16 A kan gicciye, Kiristi ya kawar da ƙiyayyar da take tsakaninmu da juna. Ya kuma kawo sulhu tsakaninmu da Allah.
17 Ya zo ya yi muku wa’azin salama; ku da kuke nesa da shi, ya kuma yi wa waɗanda suke kusa.
18 Gama ta wurinsa dukanmu za mu iya zuwa gun Uba ta wurin Ruhu guda.
19 Don haka, yanzu ku ba baƙi ba ne, ku kuma ba bare ba ne. Ku’yan ƙasa ne tare da mutanen Allah, iyalin gidan Allah kuma.
20 Ku gini ne wanda manzanni da annabawa suke tushensa, Kiristi kuma shi ne dutse mafi muhimmanci na ginin.
21 Ta wurinsa ne dukan ginin yake a haɗe, shi ne kuma yake sa ginin yă yi girma, yă zama haikali mai tsarki domin Ubangiji.
22 Ku ma sashe ne na wannan ginin da Kiristi ya yi inda Allah yake zaune ta wurin Ruhunsa.