< Mai Hadishi 9 >
1 Sai na yi tunani a kan wannan na kuma gane cewa masu adalci da masu hikima da kuma abubuwan da suke yi suna a hannun Allah ne, amma ba wanda ya san ko ƙauna ko ƙiyayya ce take jiransa.
2 Dukansu makomarsu ɗaya ce, masu adalci da masu mugunta, masu kirki da marasa kirki, masu tsabta da marasa tsabta, masu miƙa hadaya da waɗanda ba sa yi. Kamar yadda yake ga mutumin kirki, haka yake ga mai zunubi. Kamar yadda yake ga masu yin rantsuwa, haka ma da masu tsoron yi.
3 Wannan ita ce muguntar da take faruwa a cikin dukan abubuwa a duniya. Ƙaddara ɗaya ce take a kan kowa. Amma zukatan mutane cike suke da mugunta, akwai kuma hauka a zukatansu yayinda suke a raye, bayan haka kuma sai su mutu.
4 Duk wanda yake da rai a wannan duniya ta rayayyu, yana sa zuciya, gara rayayyen kare da mataccen zaki!
5 Gama rayayyu sun san za su mutu, amma matattu ba su san kome ba; ba su da wata lada nan gaba an manta da su ke nan gaba ɗaya.
6 Ƙaunarsu, ƙiyayyarsu, da kuma kishinsu tuni sun ɓace; ba za su taɓa zama sashen wani abin da yake faruwa a duniya ba.
7 Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da farin zuciya, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah.
8 Kullum ka kasance cikin farin riguna, ka kuma shafe kanka da mai kullum,
9 Ka more rayuwa da matarka, wadda kake ƙauna, dukan kwanakin nan marasa amfani da Allah ya ba ka a duniya. Gama wannan ne rabonka a rayuwa da kuma na faman aikinka a duniya.
10 Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima. (Sheol )
11 Na kuma ga wani abu a duniya. Ba kullum maguji ne yake nasara a tsere ba, ba kullum jarumi ne yake yin nasara ba, ba kullum mai hikima ne da abinci ba ba kullum mai basira ne yake da wadata ba ba kullum gwani ne yake samun tagomashi ba; amma sa’a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu.
12 Ban da haka ma, ba wanda ya san sa’ad da lokacin mutuwarsa zai yi. Kamar yadda akan kama kifi a muguwar raga, ko a kama tsuntsu a tarko, haka mugun lokaci yakan auko wa mutane, ba tsammani.
13 Na kuma ga wani misali game da hikima a duniya wanda ya burge ni sosai.
14 An yi wani ɗan ƙaramin birni mai mutane kaɗan a ciki. Sai wani babban sarki ya kawo masa yaƙi, ya kafa masa babban sansani.
15 A cikin birnin nan kuwa akwai wani mutum matalauci amma mai hikima, ya kuma ceci birnin ta wurin hikimarsa. Amma ba wanda ya tuna da matalaucin nan.
16 Sai na ce, “Hikima ta fi ƙarfe ƙarfi.” Amma aka rena hikimar matalaucin, ba a ma jin maganarsa.
17 Raɗar mai hikima da aka saurara cikin natsuwa ta fi ihun mai mulkin wawaye.
18 Hikima ta fi kayan yaƙi, amma mai zunubi ɗaya yakan rushe alheri mai yawa.