< Mai Hadishi 6 >
1 Na ga wani mugun abu a duniya, ya kuma nawaita wa mutane ƙwarai.
Il est un mal que j'ai vu sous le soleil, et qui pèse sur les hommes:
2 Allah yakan ba mutum dukiya, da wadata da kuma girma, don kada yă rasa abin da ransa yake so, amma Allah bai ba shi zarafin more su ba, a maimakon haka ma sai baƙo ne yă more su. Wannan ba shi da amfani, mugun abu ne ƙwarai.
un homme à qui Dieu donne des richesses, des biens et des honneurs, de sorte qu'il ne manque de rien pour son âme de tout ce qu'il désire, mais Dieu ne lui donne pas le pouvoir d'en manger, et c'est un étranger qui en mange. C'est là une vanité, et c'est une mauvaise maladie.
3 Mutum zai iya kasance da’ya’ya ɗari, yă kuma yi shekaru masu yawa; duk da haka kome daɗewarsa, in bai more wadatarsa ba, bai kuma sami kyakkyawar binnewa ba, na ce, gara wanda aka haife shi gawa.
Si un homme engendre cent enfants, et vit de longues années, de sorte que les jours de ses années sont nombreux, mais que son âme ne soit pas remplie de bien, et que de plus il n'ait pas de sépulture, je dis qu'un enfant mort-né vaut mieux que lui;
4 Haihuwa ba tă amfane wanda aka haifa gawa ba, gama ya zo daga duhu ya koma duhu inda aka manta da shi.
car il vient dans la vanité, et s'en va dans les ténèbres, et son nom est couvert de ténèbres.
5 Ko da yake bai ga hasken rana ba, bai kuma san kome ba, duk da haka ya dai huta, fiye da mutumin da bai more wa ransa ba,
Il n'a pas vu le soleil et ne l'a pas connu. Celui-ci a plus de repos que l'autre.
6 ko da ya yi shekara dubu biyu amma bai more wadatarsa ba. Ba wuri ɗaya dukansu biyu za su tafi ba?
Oui, quand bien même il vivrait mille ans à deux reprises, et qu'il ne jouirait pas du bien, tous ne vont-ils pas au même endroit?
7 Dukan ƙoƙarin da mutum yake yi, yana yi ne domin bakinsa, duk da haka bai taɓa gamsar da abin da yake marmari.
Tout le travail de l'homme est pour sa bouche, et cependant l'appétit n'est pas rassasié.
8 Da me mai hikima ya fi wawa? Wace riba ce matalauci yakan samu don yă iya zama da mutane?
Car quel avantage le sage a-t-il sur l'insensé? Qu'a le pauvre, qui sait marcher devant les vivants?
9 Gara abin da ido ya gani da kwaɗayin da bai sami biyan bukata ba. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.
Mieux vaut la vue des yeux que le vagabondage du désir. Cela aussi est vanité et poursuite du vent.
10 Duk abin da ya kasance, to, yana da suna, kuma duk abin da mutum yake, an riga an sani. Ba mutumin da zai iya ƙarawa da wanda ya fi shi ƙarfi.
Ce qui a été, on le nomme depuis longtemps; et l'on sait ce qu'est l'homme, et il ne peut lutter contre celui qui est plus puissant que lui.
11 Yadda yawan magana take haka ƙarancin amfaninta, yaya wannan zai amfane wani?
Car il y a beaucoup de paroles qui créent la vanité. Quel profit l'homme en tire-t-il?
12 Gama wa ya san abin da ya fi dacewa ga mutum a’yan kwanakinsa marasa amfani da sukan wuce kamar inuwa? Wa kuma zai iya faɗa masa abin da zai faru a duniya bayan ya rasu?
Car qui sait ce qui est bon pour l'homme dans la vie, tous les jours de sa vie vaine qu'il passe comme une ombre? Car qui peut dire à l'homme ce qu'il y aura après lui sous le soleil?