< Mai Hadishi 5 >

1 Ka lura da matakanka sa’ad da ka tafi gidan Allah. Ka je kusa don ka saurara a maimakon miƙa hadaya kamar wawaye, waɗanda ba su san sun yi laifi ba.
שמר רגליך (רגלך) כאשר תלך אל בית האלהים וקרוב לשמע מתת הכסילים זבח כי אינם יודעים לעשות רע
2 Kada ka yi subul da bakinka, kada zuciyarka tă yi garajen furta wani abu a gaban Allah. Allah yana sama kai kuma kana duniya, saboda haka, kada kalmominka su zama da yawa.
אל תבהל על פיך ולבך אל ימהר להוציא דבר--לפני האלהים כי האלהים בשמים ואתה על הארץ על כן יהיו דבריך מעטים
3 Kamar yadda son cika buri yakan zo sa’ad da kana da yawan damuwa, haka jawabin wawa yake sa’ad da yake yawan magana.
כי בא החלום ברב ענין וקול כסיל ברב דברים
4 Sa’ad da ka yi alkawari ga Allah, kada ka ɓata lokaci wajen cika shi. Ba ya jin daɗin wawaye; ka cika alkawarinka.
כאשר תדר נדר לאלהים אל תאחר לשלמו--כי אין חפץ בכסילים את אשר תדר שלם
5 Gara kada ka yi alkawari, da ka yi amma ba ka cika ba.
טוב אשר לא תדר--משתדור ולא תשלם
6 Kada ka bar bakinka ya kai ga yin zunubi. Kada kuma ka kai ƙara wurin ɗan saƙon haikali cewa, “Alkawarin da na yi kuskure ne.” Me ya sa Allah yake fushi a kan abin da ka faɗa har yă lalatar da aikin hannuwanka?
אל תתן את פיך לחטיא את בשרך ואל תאמר לפני המלאך כי שגגה היא למה יקצף האלהים על קולך וחבל את מעשה ידיך
7 Yawan buri da yawan magana ba su da amfani. Saboda haka, ka ji tsoron Allah.
כי ברב חלמות והבלים ודברים הרבה כי את האלהים ירא
8 In ka ga ana zaluntar matalauta a wani yanki, ba a yin adalci, ana kuma tauye hakki, kada ka yi mamakin waɗannan abubuwa; domin akwai wani jami’in da yake bisa da wani, a bisansu biyu kuwa akwai wani.
אם עשק רש וגזל משפט וצדק תראה במדינה--אל תתמה על החפץ כי גבה מעל גבה שמר וגבהים עליהם
9 Kowa yakan amfana da bunkasar amfanin ƙasa, sarki kansa yana samun riba daga gonaki.
ויתרון ארץ בכל היא (הוא)--מלך לשדה נעבד
10 Duk mai ƙaunar kuɗi ba ya samun isashe; duk ma ƙaunar dukiya ba ya ƙoshi da abin da yake samu. Wannan ma ba shi da amfani.
אהב כסף לא ישבע כסף ומי אהב בהמון לא תבואה גם זה הבל
11 Kamar yadda kaya suke haɓaka, haka ma masu amfani da su. Kuma wane amfani ne suke ga mai shi in ba ciyar da idanunsa a kansu ba?
ברבות הטובה רבו אוכליה ומה כשרון לבעליה כי אם ראית (ראות) עיניו
12 Barcin ma’aikaci daɗi gare shi, ko yă ci kaɗan ko da yawa, amma yalwar mai arziki ba ta barinsa yă iya yin barci.
מתוקה שנת העבד אם מעט ואם הרבה יאכל והשבע לעשיר--איננו מניח לו לישון
13 Na ga wani mugun abu a duniya, arzikin da aka ajiye don yă cuce mai shi,
יש רעה חולה ראיתי תחת השמש עשר שמור לבעליו לרעתו
14 ko kuwa dukiyar da ta ɓace ta wata hasara, har ya zama sa’ad da ya haifi ɗa, babu abin da ya bar masa.
ואבד העשר ההוא בענין רע והוליד בן ואין בידו מאומה
15 Tsirara mutum yakan fito daga cikin mahaifiyarsa, kuma kamar yadda ya fito, haka zai koma. Ba ya ɗaukan kome daga wahalarsa da zai riƙe a hannunsa.
כאשר יצא מבטן אמו ערום ישוב ללכת כשבא ומאומה לא ישא בעמלו שילך בידו
16 Wannan ma mugun abu ne, Yadda mutum ya zo, haka zai koma, to, wace riba ce ya ci, da yake ya yi wahalar iska ce kawai?
וגם זה רעה חולה כל עמת שבא כן ילך ומה יתרון לו שיעמל לרוח
17 Duk rayuwarsa ya ci abinci a cikin duhu, da ɓacin rai mai tsanani, da azaba, da fushi.
גם כל ימיו בחשך יאכל וכעס הרבה וחליו וקצף
18 Sa’an nan na gane cewa abu mai kyau ne, daidai ne kuma mutum yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗin aikin da ya yi a’yan kwanakin da Allah ya ba shi, gama wannan shi aka ƙaddara wa mutum daga faman wahalarsa a duniya a cikin’yan kwanakin da Allah ya ba shi a duniya, gama wannan shi ne rabonsa.
הנה אשר ראיתי אני טוב אשר יפה לאכול ולשתות ולראות טובה בכל עמלו שיעמל תחת השמש מספר ימי חיו אשר נתן לו האלהים--כי הוא חלקו
19 Ban da haka ma, sa’ad da Allah ya ba wa mutum dukiya da wadata, ya kuma ba shi zarafi yă ji daɗinsu, ya kuma amince da rabonsa, sai yă ji daɗin aikinsa, wannan kyauta ce ta Allah.
גם כל האדם אשר נתן לו האלהים עשר ונכסים והשליטו לאכל ממנו ולשאת את חלקו ולשמח בעמלו--זה מתת אלהים היא
20 Da ƙyar yake tunani a kan kwanakin rayuwarsa, domin Allah ya yarje masa, yă zauna da farin ciki.
כי לא הרבה יזכר את ימי חייו כי האלהים מענה בשמחת לבו

< Mai Hadishi 5 >