< Mai Hadishi 4 >

1 Na sāke dubawa sai na ga zaluncin da ake yi a duniya. Na ga hawayen waɗanda ake zalunta kuma ba su da mai taimako; masu iko suna goyon bayan masu zalunci, ga shi ba su da mai taimako.
Then I turned and saw all the oppressions which take place under the sun; and, behold, there were the tears of the oppressed, and they had no comforter; and from the hand of their oppressors there was violence, and they had no comforter.
2 Sai na furta cewa matattu, waɗanda suka riga suka mutu, sun fi waɗanda suke a raye farin ciki, waɗanda har yanzu suke da rai.
Therefore I praised the dead, who have been long ago dead, more than the living, who are yet alive.
3 Amma wanda ya fi su duka shi ne wanda bai riga ya kasance ba, wanda bai ga muguntar da ake yi a duniya ba.
Yea, better than both of them is he who hath not yet been, who hath not seen the evil work which is done under the sun.
4 Sai na gane cewa, duk wata fama da duk wata nasara sun samo asali daga kishin da mutum yake yi na maƙwabcinsa ne. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.
And I saw all labor, and all success in work, that for this a man is envied by his neighbor. This also is vanity, and striving after wind.
5 Wawa yakan kame hannuwansa yă kuma lalatar da kansa.
The fool foldeth his hands together and eateth his own flesh.
6 Gara tafin hannu guda cike da kwanciyar rai da tafin hannu biyu cike da tashin hankali da harbin iska kawai.
Better is a hand full of quietness, than both hands full of weariness and striving after wind.
7 Na kuma ga wani abu marar amfani a duniya.
Then I turned and saw other vanity under the sun.
8 Akwai wani mutum shi kaɗai; bai shi da ɗa ko ɗan’uwa. Ba shi da hutu daga wahalarsa, duk da haka bai ƙoshi da dukiyarsa ba. Ya tambayi kansa, “Ma wane ne nake wannan wahala, kuma me ya sa nake hana kaina jin daɗi?” Wannan ma ba shi da amfani, harkar baƙin cikin ne kawai!
There is one who is alone, and no one with him; yea, he hath neither son nor brother; yet is there no end to all his labor, and his eye is not satisfied with riches. “For whom, then [[saith he]], do I labor and deprive myself of good?” This also is vanity; yea, it is an evil thing!
9 Biyu sun fi ɗaya, gama suna samun riba mai kyau na aikinsu.
Two are better than one, because they have a good reward for their labor.
10 In ɗaya ya fāɗi, abokinsa zai taimake shi yă tashi. Amma abin tausayi ne ga mutumin da ya fāɗi ba shi kuma da wanda zai taimake shi yă tashi!
For if they fall, the one will lift his fellow up; but woe to him who is alone when he falleth, and hath not another to help him up!
11 In mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna. Amma yaya mutum ɗaya zai ji ɗumi yana shi kaɗai?
Again, if two lie together, then they have heat; but how can one be warm alone?
12 Ana iya shan ƙarfin mutum ɗaya, mutum biyu za su iya kāre kansu. Igiya riɓi uku tana da wuya tsinkawa.
And if an enemy prevail against one, two shall withstand him; and a threefold cord is not quickly broken.
13 Gara saurayi wanda yake matalauci amma yake da hikima da sarkin da ya tsufa mai wauta, wanda ba ya karɓar shawara.
Better is a child poor but wise, than a king old and foolish, who will no more be admonished.
14 Yana yiwuwa saurayin yă fito daga kurkuku yă hau gadon sarauta, ko kuma dai an haife shi cikin talauci a ƙasarsa.
For out of prison cometh forth such a one to reign; for in his own kingdom he was born a poor man.
15 Na ga cewa dukan waɗanda suka rayu suka kuma yi tafiya a duniya sun bi saurayin, magājin sarkin.
I saw that all the living, who walk under the sun, were with the child who stood up in his stead.
16 Babu ƙarshe ga dukan mutanen da suka riga su. Amma waɗanda suka zo daga baya, ba su gamsu da magājin ba. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.
There was no end to all the people before whom he went forth; yet they that come afterwards shall not rejoice in him. This also is vanity, and striving after wind.

< Mai Hadishi 4 >