< Mai Hadishi 3 >
1 Akwai lokaci domin kowane abu, da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya.
2 Lokacin haihuwa da lokacin mutuwa, lokacin shuki da lokacin tumɓukewa.
3 Lokacin kisa da lokacin warkarwa, lokacin rushewa da lokacin ginawa.
4 Lokacin kuka da lokacin dariya, lokacin makoki da lokacin rawa.
5 Lokacin warwatsa duwatsu da lokacin tara su, lokacin runguma da lokacin dainawa.
6 Lokacin nema, da lokacin fid da zuciya, lokacin ajiyewa da lokacin zubarwa.
7 Lokacin yagewa da lokacin ɗinkewa, lokacin yin shiru da lokacin magana.
8 Lokacin ƙauna da lokacin ƙiyayya, lokacin yaƙi da lokacin salama.
9 Wace riba ce ma’aikaci yake da ita saboda wahalarsa?
10 Na ga nawayar da Allah ya ɗora a kan mutane.
11 Ya yi kowane abu da kyau a lokacinsa. Ya kuma sa matuƙa a zukatan mutane, duk da haka sun kāsa gane abin da Allah ya yi daga farko zuwa ƙarshe.
12 Na san ba abin da ya fi wa mutane kyau fiye da su ji daɗi su kuma yi alheri yayinda suke da rai.
13 Cewa kowa yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗi cikin dukan aikinsa, wannan kyautar Allah ce.
14 Na san cewa duk abin da Allah ya yi zai dawwama har abada; ba abin da za a ƙara ko a rage. Allah ya yi haka domin mutane su girmama shi.
15 Duk abin da yana nan ya taɓa kasancewa, kuma abin da zai kasance, ya taɓa kasancewa; Allah kuma zai nemi bayanin abubuwan da suka wuce.
16 Sai na ga wani abu kuma a duniya, a wurin shari’a, akwai mugunta a can, a wurin adalci, akwai mugunta a can.
17 Sai na yi tunani a zuciyata, “Allah zai shari’anta masu adalci da masu mugunta, gama za a kasance da lokaci domin kowane aiki, lokaci domin kowane abu.”
18 Na sāke yin tunani, “Game da mutane kam, Allah kan gwada su don su san cewa ba su fi dabba ba.
19 Ƙaddarar mutum ɗaya take da ta dabba; ƙaddara ɗaya ce take jiransu biyu. Yadda ɗayan yake mutuwa, haka ma ɗayan. Dukansu numfashinsu iri ɗaya ne; mutum bai fi dabba ba. Kowane abu ba shi da amfani.
20 Duka wuri ɗaya za su tafi; gama duka daga turɓaya suka fito, kuma ga turɓaya duka za su koma.
21 Wa ya tabbatar cewa ruhun mutum yakan tashi sama sa’an nan na dabba yă sauka ƙasa?”
22 Saboda haka na ga babu abin da ya fi kyau wa mutum fiye da yă more wahalar aikinsa, domin wannan ne rabonsa. Gama wa zai kawo shi yă ga abin da zai faru a bayansa?