< Mai Hadishi 12 >
1 Ka tuna da Mahaliccinka a kwanakin ƙuruciyarka, kafin lokacin wahala ta zo shekaru kuma su ƙarato sa’ad da za ka ce, “Ba na jin daɗinsu,”
2 kafin rana da haske wata da taurari su daina haske, gizagizai kuma su tattaru bayan da suka sheƙa ruwa;
3 sa’ad da masu tsaron gida suke rawar jiki, majiya ƙarfi kuma suka rasa ƙarfi, sa’ad da masu niƙa suka daina don ba su da yawa, idanun da suke duba ta taga suka duhunta;
4 sa’ad da aka rufe ƙofofin shiga tituna ƙarar niƙa kuma ya tsagaita; sa’ad da kukan tsuntsaye ta farkar da mutane, ba a kuwa jin waƙoƙinsu,
5 sa’ad da mutane suke jin tsoron tudu da kuma hatsarori a tituna; sa’ad da itacen almon ya toho, fāra kuma ya yi ta jan jikinsa da ƙyar, sha’awace-sha’awace sun kafe. Daga nan mutum ya tafi madawwamiyar gidansa ya bar masu makoki suna ta yi.
6 Ka tuna da shi, kafin igiyar azurfa ta katse, ko tasar zinariya ta fashe; kafin tulu yă ragargaje a maɓulɓula, ko guga ta tsinke a rijiya,
7 turɓaya ta koma ƙasar da ta fito, rai kuma yă koma ga Allah wanda ya ba da shi.
8 “Ba amfani! Ba amfani!” In ji Malami, “Gaba ɗaya ba amfani!”
9 Ba kawai Malami ya kasance mai hikima ba, amma kuma ya koyar da mutane. Ya yi tunani ya kuma yi binciken da ya tsara karin magana masu yawa.
10 Malami ya yi bincike don yă sami kalmomin da suka dace, kuma abin da ya rubuta daidai ne da kuma gaskiya.
11 Kalmomin masu hikima kamar tsinken tsokanar dabba ne, tarin maganganunsu kuma kamar ƙusoshi ne da aka kafa daram, da aka ba wa Makiyayi guda.
12 Ka yi hankali ɗana, game da duk wani ƙari a kan waɗannan. Wallafa littattafai ba shi da iyaka, kuma yawan karatu yakan gajiyar da jiki.
13 Yanzu an ji kome; ga ƙarshen magana. Ka ji tsoron Allah ka kuma kiyaye umarnansa, gama wannan shi ne dukan hakkin mutum.
14 Gama Allah zai shari’anta kowane irin aiki, har da waɗanda aka yi a ɓoye, ko nagari ne, ko mugu.