< Mai Hadishi 11 >
1 Ka jefa burodinka a bisa ruwaye, gama bayan kwanaki masu yawa, za ka sāke samunsa.
Send forth your bread on the face of the waters, For in the multitude of the days you find it.
2 Ka raba abin hannunka ga mutum bakwai, I, har ma takwas, gama ba ka san bala’in da zai auko wa ƙasar ba.
Give a portion to seven, and even to eight, For you do not know what evil is on the earth.
3 In gizagizai sun cika da ruwa, sukan zub da ruwan sama bisa duniya. Itace ya fāɗi, ko wajen kudu ne, ko wajen arewa, inda ya fāɗi a nan zai kwanta.
If the thick clouds are full of rain, On the earth they empty [themselves]; And if a tree falls in the south or to the north, The place where the tree falls, there it is.
4 Duk mai la’akari da iska, ba zai yi shuka ba, mai la’akari da gizagizai kuma, ba zai yi girbi ba.
Whoever is observing the wind does not sow, And whoever is looking on the thick clouds does not reap.
5 Kamar yadda ba ka san hanyar iska ba, ko yadda aka siffanta jiki a cikin mahaifiya, haka ba za ka fahimci aikin Allah Mahaliccin dukan abubuwa ba.
As you do not know what [is] the way of the spirit, How—bones in the womb of the full one, So you do not know the work of God who makes the whole.
6 Ka shuka irinka da safe, da yamma kuma kada ka janye hannunka, gama ba ka san wanda zai yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuma duka biyunsu su yi albarka.
In the morning sow your seed, And at evening do not withdraw your hand, For you do not know which is right, this or that, Or whether both of them alike [are] good.
7 Haske da yana da kyau, abu mai kyau ne kuma idanu su dubi rana.
Sweet also [is] the light, And good for the eyes to see the sun.
8 Kome tsawon rayuwar mutum, bari yă more su duka. Amma bari kuma yă tuna da kwanakin duhu, gama su ma za su yi yawa. Duk abin da zai faru ba shi da amfani.
But if man lives many years, In all of them let him rejoice, And remember the days of darkness, For they are many! All that is coming [is] vanity.
9 Ka yi murna, kai matashi, a ƙuruciyarka, bari zuciyarka kuma tă yi farin ciki a kwanakin ƙuruciyarka. Ka bi shawarar zuciyarka da kuma duk abin da idanunka suka gani, amma ka sani fa, cikin dukan al’amuran nan Allah zai shari’anta ka.
Rejoice, O young man, in your childhood, And let your heart gladden you in days of your youth, And walk in the ways of your heart, And in the sight of your eyes, And know that for all these, God brings you into judgment.
10 Saboda haka, ka fid da tsoro daga zuciyarka ka kakkaɓe duk wani abin da ya dami rayuwarka, gama ƙuruciya da ƙarfi ba su da amfani.
And turn aside anger from your heart, And cause evil to pass from your flesh, For the childhood and the age [are] vanity!