< Mai Hadishi 10 >

1 Kamar yadda matattun ƙudaje sukan ɓata ƙanshin turare, haka’yar wauta takan ɓata hikima da daraja.
As dead flies bring a stench to the perfumer’s oil, so a little folly outweighs wisdom and honor.
2 Zuciyar mai hikima takan karkata ga yin abin da yake daidai, amma zuciyar wawa takan karkata ga yin mugun abu.
A wise man’s heart inclines to the right, but the heart of a fool to the left.
3 Ko yayinda yake tafiya a kan hanya wawa yakan nuna cewa ba shi da hankali, yakan nuna wa kowa wawancinsa.
Even as the fool walks along the road, his sense is lacking, and he shows everyone that he is a fool.
4 In hankalin mai mulki ya tashi game da kai, kada ka bar inda kake, gama kwantar da hankali yakan sa a yafe manyan laifofi.
If the ruler’s temper flares against you, do not abandon your post, for calmness lays great offenses to rest.
5 Akwai muguntar da na gani a duniya, irin kuskuren da yake fitowa daga masu mulki.
There is an evil I have seen under the sun— an error that proceeds from the ruler:
6 Akan sa wawaye a manyan matsayi, yayinda masu arziki suna ƙarƙashi.
Folly is appointed to great heights, but the rich sit in lowly positions.
7 Na taɓa ganin bayi a kan dawakai, yayinda’ya’yan sarki suna takawa a ƙasa kamar bayi.
I have seen slaves on horseback, while princes go on foot like slaves.
8 Duk wanda ya haƙa rami shi ne zai fāɗa a ciki; duk wanda ya rushe katanga, shi maciji zai sara.
He who digs a pit may fall into it, and he who breaches a wall may be bitten by a snake.
9 Duk mai farfasa duwatsu shi za su yi wa rauni; duk mai faskaren itace yana cikin hatsarinsu.
The one who quarries stones may be injured by them, and he who splits logs endangers himself.
10 In gatari ya dakushe ba a kuma wasa shi ba, dole a yi amfani da ƙarfi da yawa, amma ƙwarewa yana kawo nasara.
If the axe is dull and the blade unsharpened, more strength must be exerted, but skill produces success.
11 In maciji ya sari mutum kafin a ba shi makarin gardi, ina amfanin maganin?
If the snake bites before it is charmed, there is no profit for the charmer.
12 Kalmomi daga bakin mai hikima alheri ne, amma maganganun wawa za su hallaka shi.
The words of a wise man’s mouth are gracious, but the lips of a fool consume him.
13 Farkon maganarsa wauta ce, ƙarshenta kuma takan zama muguwar hauka,
The beginning of his talk is folly, and the end of his speech is evil madness.
14 wawa kuma yakan yi ta surutu. Ba wanda ya san abin da zai zo wa zai iya faɗa masa abin da zai faru bayan rasuwarsa?
Yet the fool multiplies words. No one knows what is coming, and who can tell him what will come after him?
15 Aikin wawa yakan gajiyar da shi, har bai san hanyar zuwa gari ba.
The toil of a fool wearies him, for he does not know the way to the city.
16 Kaitonki, ya ke ƙasa wadda sarkinki bawa ne wadda kuma hakimanta ke ta shagali tun da safe.
Woe to you, O land whose king is a youth, and whose princes feast in the morning.
17 Mai albarka ce, ya ke ƙasa wadda sarkinki haifaffen gidan sarauta ne, wadda hakimanta suke samun abincinsu a daidai lokacin don samun ƙarfi ba don buguwa ba.
Blessed are you, O land whose king is a son of nobles, and whose princes feast at the proper time— for strength and not for drunkenness.
18 In mutum rago ne, sai tsaiko yă lotsa, in hannuwansa ba masa yin kome, ɗaki yakan yi yoyo.
Through laziness the roof caves in, and in the hands of the idle, the house leaks.
19 Akan shirya abinci don jin daɗi, ruwan inabi kuwa don faranta zuciya, amma kuɗi ne amsar kome.
A feast is prepared for laughter, and wine makes life merry, but money is the answer for everything.
20 Kada ka zagi sarki ko da a cikin tunaninka ne, ko ka zagi mai arziki ko da a ɗakin kwananka ne, gama tsuntsun sararin sama zai iya ɗauki maganarka, tsuntsu mai fikafikai zai sanar da abin da ka ce.
Do not curse the king even in your thoughts, or curse the rich even in your bedroom, for a bird of the air may carry your words, and a winged creature may report your speech.

< Mai Hadishi 10 >