< Maimaitawar Shari’a 6 >
1 Waɗannan su ne umarnai, ƙa’idodi da kuma dokokin da Ubangiji Allahnku ya umarce ni in koya muku don ku kiyaye a ƙasar da kuke haye Urdun don mallaka,
2 saboda ku,’ya’yanku, da kuma’ya’yansu bayansu za su ji tsoron Ubangiji Allahnku muddin kuna rayuwa ta wurin kiyaye dukan ƙa’idodinsa da umarnan da na ba ku, da kuma don ku yi tsawon rai.
3 Ku ji, ya Isra’ila, ku kuma kula, ku kiyaye su don yă zama muku da lafiya, ku kuma ƙaru sosai a ƙasa mai zub da madara da zuma, kamar dai yadda Ubangiji, Allahn kakanninku ya yi muku alkawari.
4 Ku ji, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.
5 Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku.
6 Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku.
7 Ku koya wa’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.
8 Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku.
9 Ku rubuta su a dogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.
10 Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku cikin ƙasar da ya rantse ga kakanninku, ga Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, yă ba ku, ƙasa mai girma, mai manyan biranen da ba ku kuka gina ba,
11 gidaje cike da kowane irin abubuwa masu kyau, da ba ku kuka tanadar ba, rijiyoyin da ba ku kuka haƙa ba, da gonakin inabi da itatuwan zaitun da ba ku kuka shuka ba, sa’ad da kuwa kuka ci, kuka kuma ƙoshi,
12 ku yi hankali cewa ba ku manta da Ubangiji wanda ya fitar da ku daga Masar, da gidan bauta ba.
13 Ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa shi kaɗai, ku kuma yi alkawaranku da sunansa.
14 Kada ku bi waɗansu alloli, allolin mutanen da suke kewaye da ku;
15 gama Ubangiji Allahnku, wanda yake cikinku, Allah ne mai kishi, fushinsa kuma zai yi ƙuna gāba da ku, zai kuma hallaka ku daga fuskar ƙasar.
16 Kada ku gwada Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi a Massa.
17 Ku tabbata kun kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, da farillansa da kuma ƙa’idodinsa da ya ba ku.
18 Ku aikata abin da yake daidai da kuma mai kyau a idon Ubangiji, don yă zama muka da lafiya, ku kuwa shiga ku mallaki ƙasa mai kyau da Ubangiji ya yi alkawari da rantsuwa ga kakanninku.
19 Zai kuwa korin dukan abokan gābanku da suke gabanku, yadda Ubangiji ya faɗa.
20 Nan gaba, sa’ad da’ya’yanku suka tambaye ku, “Mene ne ma’anar farillai, ƙa’idodi da kuma dokokin da Ubangiji Allahnmu ya umarce ku?”
21 Sai ku gaya musu, “Dā mu bayin Fir’auna ne a Masar, amma Ubangiji ya fitar da mu daga Masar da hannu masu ƙarfi.
22 A idanunmu Ubangiji ya aikata manyan alamu masu banmamaki, da al’ajabai gāba da Masarawa, da Fir’auna, da kuma dukan gidansa.
23 Amma ya fitar da mu daga can domin yă kawo mu cikin ƙasar da ya yi wa kakanninmu alkawari tare da rantsuwa zai ba mu.
24 Ubangiji ya umarce mu mu yi biyayya da dukan waɗannan ƙa’idodi, mu kuma ji tsoron Ubangiji Allahnmu, saboda kullum mu ci gaba, a kuma bar mu da rai, kamar yadda yake a yau.
25 In kuma muka kula, muka kiyaye dukan dokokin nan a gaban Ubangiji Allahnmu, kamar yadda ya umarce mu, wannan zai zama adalci a gare mu.”