< Maimaitawar Shari’a 32 >

1 Ku saurara, ya ku sammai, zan yi magana; bari duniya ta ji maganar bakina.
האזינו השמים ואדברה ותשמע הארץ אמרי פי
2 Bari koyarwata tă zubo kamar ruwan sama kalmomina kuma su sauko kamar raɓa, kamar yayyafi a kan sabuwar ciyawa, kamar ruwan sama mai yawa a kan tsirai marasa ƙarfi.
יערף כמטר לקחי תזל כטל אמרתי כשעירם עלי דשא וכרביבים עלי עשב
3 Zan yi shelar sunan Ubangiji. Ku yabi girman Allahnmu!
כי שם יהוה אקרא הבו גדל לאלהינו
4 Shi Dutse ne, ayyukansa cikakku ne, dukan hanyoyinsa kuwa masu adalci ne. Allah mai aminci, wanda ba ya yin rashi gaskiya, shi mai adalci ne, nagari ne kuma.
הצור תמים פעלו כי כל דרכיו משפט אל אמונה ואין עול צדיק וישר הוא
5 Sun aikata mugunta a gabansa; saboda abin kunyarsu, su ba’ya’yansa ba ne, amma wata muguwar tsara ce, karkatacciya.
שחת לו לא בניו מומם דור עקש ופתלתל
6 Haka za ku biya Ubangiji, Ya ku wawaye da kuma mutane marasa hikima? Shi ba Ubanku ba ne, Mahaliccinku, wanda ya yi ku, ya kuma siffanta ku?
ה ליהוה תגמלו זאת-- עם נבל ולא חכם הלוא הוא אביך קנך הוא עשך ויכננך
7 Ku tuna da kwanakin dā, ku tuna da tsararrakin da suka wuce tun tuni, Ku tambayi iyayenku, za su faɗa muku, dattawanku, za su kuma bayyana muku.
זכר ימות עולם בינו שנות דר ודר שאל אביך ויגדך זקניך ויאמרו לך
8 Sa’ad da Mafi Ɗaukaka ya ba da al’ummai gādonsu, sa’ad da ya raba dukan’yan adam, ya kafa iyakoki wa mutane bisa ga yawan’ya’yan Isra’ila maza.
בהנחל עליון גוים בהפרידו בני אדם יצב גבלת עמים למספר בני ישראל
9 Gama rabon Ubangiji shi ne mutanensa, Yaƙub shi ne rabon gādonsa.
כי חלק יהוה עמו יעקב חבל נחלתו
10 A cikin hamada ya same shi, a jeji marar amfani, inda namomi suke kuka. Ya tsare shi, ya kuma lura da shi; ya bi da shi kamar ƙwayar idonsa,
ימצאהו בארץ מדבר ובתהו ילל ישמן יסבבנהו יבוננהו-- יצרנהו כאישון עינו
11 kamar gaggafar da take yawo a kan sheƙarta tana rufe’ya’yanta, ta buɗe fikafikanta don tă kwashe su tă ɗauke su a kafaɗunta.
כנשר יעיר קנו על גוזליו ירחף יפרש כנפיו יקחהו ישאהו על אברתו
12 Ubangiji kaɗai ya jagorance shi; babu wani baƙon gunkin da yake tare da shi.
יהוה בדד ינחנו ואין עמו אל נכר
13 Ya sa shi ya hau ƙwanƙolin dutse ya ciyar da shi da amfanin gona. Ya shayar da shi da zuma daga dutse, da kuma mai daga dutsen ƙanƙara,
ירכבהו על במותי (במתי) ארץ ויאכל תנובת שדי וינקהו דבש מסלע ושמן מחלמיש צור
14 da kindirmo da madara daga shanu da tumaki da ƙibabbun tumaki da awaki, da zaɓaɓɓun ragunan Bashan da kuma ƙwayoyin alkama mafi kyau. Ka sha ruwan inabi ja wur mai kumfa.
חמאת בקר וחלב צאן עם חלב כרים ואילים בני בשן ועתודים עם חלב כליות חטה ודם ענב תשתה חמר
15 Yeshurun ya yi ƙiba, ya yi kauri; cike da abinci, ya zama da nauyi, ya kuma zama sumul. Ya yashe Allahn da ya yi shi, ya ƙi Dutse Cetonsa.
וישמן ישרון ויבעט שמנת עבית כשית ויטש אלוה עשהו וינבל צור ישעתו
16 Suka sa shi kishi saboda baƙin allolinsu, suka husata shi da gumakan banƙyamarsu.
יקנאהו בזרים בתועבת יכעיסהו
17 Suka yi hadaya ga aljanu, waɗanda ba Allah ba, ga allolin da ba su sani ba, ga allolin da aka shigo da su daga baya, allolin da kakanninku ba su ji tsoronsu ba.
יזבחו לשדים לא אלה-- אלהים לא ידעום חדשים מקרב באו לא שערום אבתיכם
18 Kuka rabu da Dutsen da ya zama mahaifi gare ku; kuka manta da Allahn da ya haife ku.
צור ילדך תשי ותשכח אל מחללך
19 Ubangiji ya ga wannan ya kuma ƙi su, domin’ya’yansa maza da mata sun husata shi.
וירא יהוה וינאץ מכעס בניו ובנתיו
20 Ya ce, “Zan ɓoye fuskata daga gare su, in ga ƙarshensu; gama su muguwar tsara ce,’ya’ya ne marasa aminci.
ויאמר אסתירה פני מהם-- אראה מה אחריתם כי דור תהפכת המה בנים לא אמן בם
21 Sun sa ni kishi ta wurin abin da ba allah ba, suka kuma husata ni da gumakansu na wofi. Zan sa su yi kishi ta wurin waɗanda ba mutane ba; zan sa su yi fushi ta wurin al’ummar da ba ta da sani.
הם קנאוני בלא אל כעסוני בהבליהם ואני אקניאם בלא עם בגוי נבל אכעיסם
22 Gama fushina ya kama wuta, tana ci har ƙurewar zurfin lahira. Za tă cinye duniya da girbinta, tă kuma sa wuta a tussan duwatsu. (Sheol h7585)
כי אש קדחה באפי ותיקד עד שאול תחתית ותאכל ארץ ויבלה ותלהט מוסדי הרים (Sheol h7585)
23 “Zan tula masifu a kansu in kuma gama kibiyoyina a kansu.
אספה עלימו רעות חצי אכלה בם
24 Zan aika da yunwa mai tsanani a kansu, zazzaɓi mai zafi da muguwar annoba; zan aika da haƙoran namun jeji a kansu, da dafin mesa masu ja da ciki.
מזי רעב ולחמי רשף וקטב מרירי ושן בהמת אשלח בם עם חמת זחלי עפר
25 Waɗanda suke a waje, takobi zai kashe su, a cikin gidajensu kuma tsoro zai mamaye su.’Yan maza da’yan mata za su hallaka, haka ma jarirai da maza masu furfura.
מחוץ תשכל חרב ומחדרים אימה גם בחור גם בתולה--יונק עם איש שיבה
26 Na ce zan watsar da su in sa a manta da su a tunanin’yan adam.
אמרתי אפאיהם אשביתה מאנוש זכרם
27 Amma ina tsoron tsokanar abokin gāba, don kada abokan gāba su kāsa ganewa har su ce, ‘Hannunmu ne ya yi nasara; ba Ubangiji ne ya aikata dukan wannan ba.’”
לולי כעס אויב אגור-- פן ינכרו צרימו פן יאמרו ידנו רמה ולא יהוה פעל כל זאת
28 Al’ummai ne marasa azanci, babu ganewa a cikinsu.
כי גוי אבד עצות המה ואין בהם תבונה
29 A ce su masu hikima ne har su gane wannan su gane abin da ƙarshensu zai zama!
לו חכמו ישכילו זאת יבינו לאחריתם
30 Yaya mutum guda zai kore dubu, mutum biyu su sa dubu goma su gudu, sai ko Dutsensu ya sayar da su, sai ko Ubangiji ya bashe su.
איכה ירדף אחד אלף ושנים יניסו רבבה אם לא כי צורם מכרם ויהוה הסגירם
31 Gama dutsensu ba kamar Dutsenmu ba ne, abokan gābanmu sun san da haka.
כי לא כצורנו צורם ואיבינו פלילים
32 Kuringarsu ta fito daga kuringar Sodom ne, daga gonakin Gomorra kuma.’Ya’yan inabinsu dafi ne, nonnansu masu ɗaci ne.
כי מגפן סדם גפנם ומשדמת עמרה ענבמו ענבי רוש-- אשכלת מררת למו
33 Ruwan inabinsu dafin macizai ne, mugun dafin gamshaƙa ne.
חמת תנינם יינם וראש פתנים אכזר
34 “Ban jibge wannan a ma’ajiya na kuma yimƙe shi a taskokina ba?
הלא הוא כמס עמדי חתום באוצרתי
35 Sakayya nawa ne, zan kuwa ɗau fansa. A cikin lokaci, ƙafarsu za tă yi santsi; ranar masifarsu ta yi kusa hallakarsu kuma tana gaggautawa a kansu.”
לי נקם ושלם לעת תמוט רגלם כי קרוב יום אידם וחש עתדת למו
36 Ubangiji zai shari’anta mutanensa yă kuma ji tausayin bayinsa sa’ad da ya ga ƙarfinsu ya ƙare babu kowa kuma da ya rage, bawa ko’yantacce.
כי ידין יהוה עמו ועל עבדיו יתנחם כי יראה כי אזלת יד ואפס עצור ועזוב
37 Zai ce, “To, ina allolinsu, dutsen da suka yi mafaka a ciki,
ואמר אי אלהימו-- צור חסיו בו
38 allolin da suka ci kitsen hadayunsu suka kuma sha ruwan inabin hadayunsu? Ku sa su tashi su taimake ku mana! Bari su ba ku mafaka!
אשר חלב זבחימו יאכלו ישתו יין נסיכם יקומו ויעזרכם-- יהי עליכם סתרה
39 “Ku duba yanzu cewa ni ne Shi! Ba wani allah in ban da ni. Nakan kashe in kuma rayar, nakan sa rauni in kuma warkar, ba wanda yake da iko yă cece wani daga hannuna.
ראו עתה כי אני אני הוא ואין אלהים עמדי אני אמית ואחיה מחצתי ואני ארפא ואין מידי מציל
40 Na ɗaga hannu sama na kuma furta. Muddin ina raye har abada,
כי אשא אל שמים ידי ואמרתי חי אנכי לעלם
41 sa’ad da na wasa takobi mai walƙiya hannuna kuwa ya cafke shi don yin hukunci, zan ɗau fansa a kan abokan gābana in sāka wa waɗanda suke ƙina.
אם שנותי ברק חרבי ותאחז במשפט ידי אשיב נקם לצרי ולמשנאי אשלם
42 Zan sa kibiyoyina su bugu da jini, yayinda takobina yana cin nama, jinin kisassu da na kamammu, kawunan shugabannin abokan gāba.”
אשכיר חצי מדם וחרבי תאכל בשר מדם חלל ושביה מראש פרעות אויב
43 Ku yi farin ciki, ya ku al’ummai, tare da mutanensa, gama zai rama ɗau fansar jinin bayinsa; zai ɗau fansa a kan abokan gābansa yă kuma yi kafara domin ƙasarsa da mutanensa.
הרנינו גוים עמו כי דם עבדיו יקום ונקם ישיב לצריו וכפר אדמתו עמו
44 Sai Musa ya zo da Yoshuwa ɗan Nun suka faɗa dukan waɗannan kalmomi wannan waƙa a kunnen mutane.
ויבא משה וידבר את כל דברי השירה הזאת--באזני העם הוא והושע בן נון
45 Sa’ad da Musa ya gama karanta waɗannan kalmomi ga dukan Isra’ila,
ויכל משה לדבר את כל הדברים האלה--אל כל ישראל
46 ya ce musu, “Ku riƙe dukan kalmomin da na furta muku a yau, don ku umarce’ya’yanku su lura, su yi biyayya da dukan kalmomin wannan doka.
ויאמר אלהם שימו לבבכם לכל הדברים אשר אנכי מעיד בכם היום אשר תצום את בניכם לשמר לעשות את כל דברי התורה הזאת
47 Ba kalmomi kurum ba ne dominku, amma har ranku ma. Ta wurinsu za ku yi tsawon rai a ƙasar da kuke haye Urdun ku ci gādonta.”
כי לא דבר רק הוא מכם--כי הוא חייכם ובדבר הזה תאריכו ימים על האדמה אשר אתם עברים את הירדן שמה לרשתה
48 A wannan rana Ubangiji ya ce wa Musa,
וידבר יהוה אל משה בעצם היום הזה לאמר
49 “Ka hau Duwatsun Abarim zuwa Dutsen Nebo a Mowab, tsallake daga Yeriko, ka hangi Kan’ana, ƙasar da nake ba wa Isra’ilawa gādo.
עלה אל הר העברים הזה הר נבו אשר בארץ מואב אשר על פני ירחו וראה את ארץ כנען אשר אני נתן לבני ישראל לאחזה
50 A can kan dutsen da ka hau za ka mutu a kuma tara ka ga mutanenka, kamar yadda ɗan’uwanka Haruna ya mutu a Dutsen Hor aka kuma tara shi ga mutanensa.
ומת בהר אשר אתה עלה שמה והאסף אל עמיך כאשר מת אהרן אחיך בהר ההר ויאסף אל עמיו
51 Wannan kuwa domin ku biyu kun fid da aminci gare ni a gaban Isra’ilawa a ruwan Meriba ta Kadesh, a Hamadar Zin kuma saboda ba ku riƙe tsarkina a cikin Isra’ilawa ba.
על אשר מעלתם בי בתוך בני ישראל במי מריבת קדש מדבר צן--על אשר לא קדשתם אותי בתוך בני ישראל
52 Saboda haka, za ka ga ƙasar daga nesa kawai; ba za ka shiga ƙasar da nake ba wa mutanen Isra’ila ba.”
כי מנגד תראה את הארץ ושמה לא תבוא--אל הארץ אשר אני נתן לבני ישראל

< Maimaitawar Shari’a 32 >