< Maimaitawar Shari’a 30 >
1 Sa’ad da dukan albarku da la’anonin nan da na sa a gabanku suka zo muku, kuka kuma sa su a zuciya, a duk inda Ubangiji Allahnku ya watsar da ku a cikin al’ummai,
Cum ergo venerint super te omnes sermones isti, benedictio, sive maledictio, quam proposui in conspectu tuo: et ductus pœnitudine cordis tui in universis gentibus, in quas disperserit te Dominus Deus tuus,
2 sa’ad da kuma ku da’ya’yanku kuka komo ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma yi biyayya da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, bisa ga kome da na umarce ku a yau,
et reversus fueris ad eum, et obedieris eius imperiis, sicut ego hodie præcipio tibi, cum filiis tuis, in toto corde tuo, et in tota anima tua:
3 a sa’an nan ne Ubangiji Allahnku zai yi muku jinƙai, yă ji tausayinku, yă kuma sāke tattara ku daga dukan al’ummai inda ya warwatsa ku.
reducet Dominus Deus tuus captivitatem tuam, ac miserebitur tui, et rursum congregabit te de cunctis populis, in quos te ante dispersit.
4 Ko da ma an kore ku zuwa ƙasa mafi nisa a ƙarƙashin sammai, daga can Ubangiji Allahnku zai tattara ku, yă dawo da ku.
Si ad cardines cæli fueris dissipatus, inde te retrahet Dominus Deus tuus,
5 Zai dawo da ku zuwa ƙasar da take ta kakanninku, za ku kuwa mallake ta. Zai sa ku yi arziki, ku kuma yi yawa fiye da kakanninku.
et assumet, atque introducet in Terram, quam possederunt patres tui, et obtinebis eam: et benedicens tibi, maioris numeri te esse faciat quam fuerunt patres tui.
6 Ubangiji Allahnku zai yi wa zukatanku kaciya da kuma zukatan zuriyarku, saboda ku ƙaunace shi da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, ku kuma rayu.
Circumcidet Dominus Deus tuus cor tuum, et cor seminis tui: ut diligas Dominum Deum tuum in toto corde tuo, et in tota anima tua, ut possis vivere.
7 Ubangiji Allahnku zai sa dukan waɗannan la’anoni a kan abokan gābanku waɗanda suke ƙinku, suke kuma tsananta muku.
Omnes autem maledictiones has convertet super inimicos tuos, et eos, qui oderunt te et persequuntur.
8 Za ku sāke yi wa Ubangiji biyayya, ku kuma bi dukan umarnan da nake ba ku a yau.
Tu autem reverteris, et audies vocem Domini Dei tui: faciesque universa mandata quæ ego præcipio tibi hodie:
9 Sa’an nan Ubangiji Allahnku zai mayar da ku masu arziki ƙwarai a cikin dukan aiki hannuwanku, da kuma cikin’ya’yanku, da’ya’yan shanunku, da kuma hatsin gonarku. Ubangiji zai sāke jin daɗinku yă sa ku yi arziki, kamar dai yadda ya ji daɗin kakanninku.
et abundare te faciet Dominus Deus tuus in cunctis operibus manuum tuarum, in sobole uteri tui, et in fructu iumentorum tuorum, in ubertate terræ tuæ, et in rerum omnium largitate. Revertetur enim Dominus, ut gaudeat super te in omnibus bonis, sicut gavisus est in patribus tuis:
10 In dai kuka yi biyayya ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma kiyaye umarnansa da ƙa’idodin da aka rubuta a wannan Littafin Doka, kuka juyo ga Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku.
si tamen audieris vocem Domini Dei tui, et custodieris præcepta eius et ceremonias, quæ in hac lege conscripta sunt: et revertaris ad Dominum Deum tuum in toto corde tuo, et in tota anima tua.
11 To, abin da nake umartanku a yau, ba mai wuya ba ne gare ku, ba kuma abin da ya fi ƙarfinku ba ne.
Mandatum hoc, quod ego præcipio tibi hodie, non supra te est, neque procul positum,
12 Ba ya can sama, balle ku ce, “Wa zai hau sama yă kawo mana, yă kuma furta mana, don mu yi biyayya?”
nec in cælo situm, ut possis dicere: Quis nostrum valet ad cælum ascendere, ut deferat illud ad nos, et audiamus atque opere compleamus?
13 Ba kuwa yana gaba da teku ba, da za ku ce, “Wa zai haye tekun don yă kawo mana, yă kuma furta mana, don mu yi biyayya?”
Neque trans mare positum: ut causeris, et dicas: Quis ex nobis poterit transfretare mare, et illud ad nos usque deferre: ut possimus audire, et facere quod præceptum est?
14 A’a, kalmar tana nan dab da ku, tana cikin bakinku da cikin zuciyarku, don ku yi biyayya.
Sed iuxta te est sermo valde, in ore tuo, et in corde tuo, ut facias illum.
15 Ku duba, na sa a gabanku a yau, rai da wadata, mutuwa da kuma hallaka.
Considera quod hodie proposuerim in conspectu tuo vitam et bonum, et econtrario mortem et malum:
16 Gama na umarce ku a yau, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, don ku yi tafiya a hanyoyinsa, ku kuma kiyaye umarnansa, ƙa’idodinsa da kuma dokokinsa, sa’an nan za ku rayu, ku kuma ƙaru, Ubangiji Allahnku kuwa zai albarkace ku a ƙasar da kuke shiga don ci gādonta.
ut diligas Dominum Deum tuum, et ambules in viis eius, et custodias mandata illius ac ceremonias atque iudicia: et vivas, atque multiplicet te, benedicatque tibi in Terra, ad quam ingredieris possidendam.
17 Amma in zukatanku suka kangare, ba su kuwa yi biyayya ba, in kuma aka rinjaye ku don ku rusuna ga waɗansu alloli ku yi musu bauta,
Si autem aversum fuerit cor tuum, et audire nolueris, atque errore deceptus adoraveris deos alienos, et servieris eis:
18 na furta muku yau cewa tabbatacce za a hallaka ku. Ba za ku zauna a ƙasar da kuke hayewa Urdun don ku shiga ku ci gādonta ba.
prædico tibi hodie quod pereas, et parvo tempore moreris in Terra, ad quam, Iordane transmisso, ingredieris possidendam.
19 A wannan rana na kira bisa sama da ƙasa a matsayin shaidu a kanku, cewa na sa a gabanku rai da mutuwa, albarku da la’anoni. Yanzu sai ku zaɓi rai, saboda ku da’ya’yanku ku rayu
Testes invoco hodie cælum et terram, quod proposuerim vobis vitam et mortem, benedictionem et maledictionem. Elige ergo vitam, ut et tu vivas, et semen tuum:
20 don kuma ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku saurari muryarsa, ku kuma manne masa. Gama Ubangiji shi ranku, zai kuwa ba ku shekaru masu yawa a ƙasar da ya rantse zai ba wa kakanninku, Ibrahim, Ishaku da Yaƙub.
et diligas Dominum Deum tuum, atque obedias voci eius, et illi adhæreas (ipse est enim vita tua, et longitudo dierum tuorum) ut habites in Terra, pro qua iuravit Dominus patribus tuis, Abraham, Isaac, et Iacob, ut daret eam illis.